← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 61

Sashe 8

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko wanne ɗan sarki, ya sauqa a masauqin da aka ta nadar don shi da jama'ar sa. Sannan an wadata ko wannen su da duk abubuwan da zasu buqata, a matsayinsu na yaran sarakuna sannan kuma manya-manyan baqi " A MASARAUTAN QUBAISH.

🅁🄰🄽🄰🅁 🄶🅄🄳🄰🄽🄰🅁 🄳🄰 🄶🄰🅂🄰
"𝙧𝙖𝙣𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙦𝙖𝙧𝙮𝙖" faɗin malam ba'haushe wai "sai dai uwar ɗiya taji kunya".
FILIN TARO
Mutane ne a cike a wannan qatoton fili, ba ko masaka stinke. Sosai filin aka qawata shi dan wannan taron(gasa) ya cika fam da jama'a, mutane da dama sun hallari wannan taro.
A gefe guda kuwa na wannan fili, ko wanne ɗan sarki, da wajan zamansa shi da tawagar sa(hadimominsa).
Taro yayi taro. Ko wa ka gani fuskan sa ɗauke da fara'a!! ko wa ya qagu yaga abun da ze wakana a wannan fili. Sannan kuma wa zata zaɓa a cikin yaran sarakunan? wane ne jarumin da zai lashe gasan? Kowa kawai zuba na mujiyarsa yake, ya ga ta inda Gimbiyar tasu zata ɓullo.
Gefe guda kuwa a munbari mai girma Sarki Qaseem ne da fadawan sa,waziri, galadima,da dai sauran dogarae da kuma ƴan fada.
Manyan ƴan kasuwan cikin Masarautan dama wasu a wajen Masarauta, manyan masu kuɗi na Masarautan da wajen Masarauta, suma wajan zaman su a qa wace. Guri yayi guri, taro yayi taro(abun se wanda ya gani kawai).
hayaniyan da ke tashi a wajen ne ya ɗauke cak!! Abun da ya ɗau hankalina na juya dan ganin ko menene?? Wajen yayi tsit, ba kajin qaran komi sai sawun takalma gami da qirarin da dogarae da kuyangu ke yi!! Wanda hakan ze tabbatar maka Gimbiyar ce ke shigowa filin taron.

***
𝙏𝙖𝙠𝙖𝙬𝙖𝙧 𝙠𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖
𝙔𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞, 𝙟𝙞𝙠𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞!!
𝙎𝙖𝙡𝙚𝙡𝙚𝙣 𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖!
𝙈𝙖𝙘𝙚 𝙙𝙖𝙮𝙖 𝙩𝙖𝙢 𝙠𝙖𝙧 𝙢𝙖𝙯𝙖 𝙙𝙪𝙗𝙪,
𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙖, 𝙮𝙖𝙧 𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞, 𝙟𝙞𝙠𝙖𝙧 𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞.
𝙆𝙤 𝙣𝙖𝙢𝙞𝙟𝙞 𝙗𝙖𝙮𝙖 𝙩𝙪𝙣𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣 𝙠𝙞 𝙨𝙚 𝙮𝙖 𝙨𝙝𝙞𝙧𝙮𝙖.
𝙂𝙖𝙗𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣! 𝙗𝙖𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣! 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙖𝙣𝙞𝙮𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧𝙚𝙣 𝙝𝙖𝙦𝙤𝙧𝙖,,
𝙁𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙨𝙝𝙖 𝙠𝙖𝙡𝙡𝙤
𝙆𝙞𝙣 𝙯𝙖𝙧𝙘𝙚 𝙕𝙞𝙣𝙖𝙧𝙚 𝙠𝙤 𝙈𝙪𝙧𝙟𝙖𝙣𝙞 𝙠𝙖𝙞 𝙝𝙖𝙧𝙙𝙖 𝙢𝙖 𝙡𝙪'𝙪 𝙡𝙪'𝙪 𝙙𝙖𝙣 𝙠𝙪𝙬𝙖 𝙨𝙖𝙞 𝙢𝙖𝙞 𝙩𝙨𝙖𝙣-𝙩𝙨𝙖𝙣 𝙧𝙖𝙗𝙤 𝙙𝙖 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙩𝙖 𝙣𝙚 𝙯𝙚 𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙠𝙞, 𝙩𝙖𝙠𝙖𝙬𝙖𝙣𝙠𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙔𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞 𝙠𝙪𝙢𝙖, 𝙎𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙢𝙪 𝙩𝙖 𝙜𝙤𝙗𝙚 𝙄𝙣𝙨𝙝𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝𝙪, 𝙢𝙖𝙩𝙖𝙧 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞, 𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞, 𝙟𝙞𝙠𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙢𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞.
𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼 𝙈𝙀𝙃𝙒𝙄𝙎𝙃 𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙣 𝙢𝙪 𝙩𝙖 𝙜𝙤𝙗𝙚 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙞𝙣𝙘𝙚𝙬𝙖𝙣 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝.
𝙃𝙖𝙮𝙮𝙖 𝙠𝙖𝙞 𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙨𝙖𝙣 𝙠𝙖𝙞 𝙗𝙖 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞𝙣 𝙣𝙖𝙢𝙞𝙟𝙞 𝙗𝙖 𝙣𝙚 𝙟𝙖𝙖 𝙠𝙖𝙪𝙘𝙚 𝙠𝙖 𝙗𝙖𝙬𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖 𝙛𝙞𝙡𝙞 𝙙𝙖𝙣 𝙢𝙖𝙜𝙖𝙣𝙖𝙣 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙩𝙖 𝙖𝙟𝙚.
𝙅𝙖𝙧𝙪𝙢𝙖, 𝙗𝙖𝙨𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙞𝙮𝙖, 𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙠𝙮𝙖𝙬𝙖𝙬𝙖𝙣 𝙙𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙖. 𝘼𝙣𝙮𝙞 𝙖𝙣𝙮𝙞 𝙖𝙣 𝙠𝙖𝙨𝙖 𝙠𝙞𝙣 𝙜𝙖𝙜𝙖𝙧𝙞 𝙪𝙗𝙖𝙣 𝙢𝙪𝙩𝙪𝙢 𝙗𝙖𝙡𝙡𝙚 𝙢𝙪𝙩𝙪𝙢 𝙙𝙖 𝙠𝙖𝙣𝙨𝙖, 𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙟𝙖 𝙠𝙬𝙖𝙣𝙖 𝙮𝙖 𝙗𝙖𝙠𝙞 𝙩𝙨𝙖𝙬𝙤𝙣 𝙧𝙖𝙞 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖, 𝙠𝙞 𝙩𝙖𝙠𝙖 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙮𝙖𝙧 𝙜𝙖𝙩𝙖 𝙮𝙖 𝙙𝙖𝙮𝙖 𝙩𝙞𝙡𝙤, 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 𝙝𝙖𝙬𝙖𝙮𝙚𝙣 𝙈𝘼𝙎𝘼𝙍𝘼𝙐𝙏𝘼𝙉 𝙌𝙐𝘽𝘼𝙄𝙎𝙃!!!
***

𝙌𝙞𝙧𝙖𝙧𝙞 𝙠𝙖𝙬𝙖𝙞 𝙩𝙖𝙠𝙚 𝙨𝙝𝙖 𝙩𝙪𝙣 𝙠𝙖𝙣 𝙩𝙖 ɓ𝙪𝙡𝙡𝙤 tsakiyan taron 𝙝𝙖𝙧 t𝙖 𝙞𝙨𝙤 𝙩𝙨𝙖𝙠𝙞𝙮𝙖𝙝𝙣 𝙩𝙖𝙧𝙤𝙣 jama'an.
Idanuwa ne duk suka koma kanta, kowa ka gani yana magana tom yabon kyau irin na halitta da Ubangiji SWT yayi mata ake.
Sanye take da kaya irin na jarumai mata masu zuwa yaqi, ko ina na a rufe yake baka ganin komi se qwayan idanuwan ta. Duk da kasancewan kayan yaqi ne ajikin ta kuma jikin a rufe hakan be hana bayyana kyau, jarumta, baiwa, sadaukan taka, da komi da Allah ya azurta ta dashi ba, ma bayyani.
Fara ce sol! Duk da baka ganin fatan jikin ta, Amma qwayan idanuwan ta kaɗai ka gani ze tabbatar maka da hakan, qwayan idanun da ke zautar da mai kallon su. Blue-Blue haka qwayan idon su ke, ga farin idon kuma fari tass!! ka ranste ba idon mutum ba, dan kallon su ma na ɗauke wa mutum ido.
Wu cewa tayi ta zauna wajan da aka qanwata, aka kuma masa kwalliya, dan zaman ta.
Tun shigowan ta filin taron ba iya jama'a ba har yaran sarakunan duk suka ruɗe, kowa ji yake kaman ya ɗauke ta ya gudu da ita.

Mai magana ne ya tashi, ya na jawabi da farko maraba yaiwa duk baqin da suka hallara da ma ɗauka cin jama'ar gari. Ya gaida kowa yacce ya kamata. Yama yaran Sarakunan barka da kuma addu'an nasara ga mai rabo. Sannan ya fara koro jawabi :-
"Kaman yacce aka sani ba wanda ya taɓa ganin fuskan GIMBIYA MEHWISH. To musabbabin taron nan gasa ne tsakanin yaran sarakuna masu nema da biɗar auren Gimbiya. Abu ɗaya ne duk wanda yake ganin ya shirya a yaran sarakunan tom ze iya fitowa su gwabxa. Duk wanda yayi nasaran cire abunda ke fuskanta tom shine de yaci gasa kuma Insha Allahu Shine wanda zai Aureta".
Yaran sarakunan ne suka fara mamaki!! Just simple abun fuskan ta, ta ɗauki kowa rago kenan? Kowannen su faɗi yake a ransa "zata sha mamaki".
Ku san dukkansu a tare suka tashi.
Magana mutumin ya qara yi. "Da alama de gwarazan mazaje ne suka zo neman auren Gimbiyar tamu kuma Sarauniyar gobe Insha Allahu.
" Yanxu dai za'a fara ne da na farko a jadawali, ɗan sarkin garin A𝙠𝙠𝙖𝙡. Daga jin sunan sa ya tashi ya fito, bayan ya kimtsa zan zaronsa sannan ya damqi takobin sa, cike da faɗi da tafiya cikin jarumta ya shige cikin fili da yake na buga gasan.
"Gimbiya ana buqatan ki a fili" faɗin mutumin da ke magana da abun sauti. tashuwa tayi cike da jarumta da haiba ta nufi cikin filin
"Ana mata kirari da kuma tafi".
Husur aka hura musu nan take suka fara gobzawan.
Gobzawa suke yi abun gwanin burgewa!
Tun yariman garin A𝙠𝙠𝙖𝙡 na ganin abun wasa har abu yafi qarfin sa, tun yakan iya kai hari har ya dawo kare kansa kawai yake yi. Ana hakan har Gimbiya ta kaisa qasa ko jikinta takobin sa bai taɓa ba.
Haka aka ta gobzawa tsakanin Gimbiya Mehwish da ƴaƴan Sarakunan har sai da ta gobza da yaran sarkuna huɗu (4) a ranan.
Sannan duk cikin waɗanda duka gwabza da su ba wanda ya ko taɓa jikin ta bare buɗe abun da ta rufe fuskan ta.
A haka gasan ranan ya tsaya sai zuwa gobe kuma. Mutanen masarautan se jin daɗi suke! da nishadi! da kuma qara jin jinawa jarumta irin na Gimbiyar tasu.
Sarki Qaseem kuwa ya kasa cewa komi, kuma ya rasa dalilin ƴar tasa na cewa buɗe fuskanta ne ya zamana ta zaɓe ka. Duk da ya saba da jin tace a buɗe fuskanta ta bada kaza-kaza.
Amma yau ya basa mamaki sai dai bakomi, ya nawa ƴaƴan Sarakunan fatan Sa'a ga mai rabo.
A haka taron yau ya watse sai kuma Allah ya kaimu zuwa gobe su cigaba. A ɓangaren Gimbiya kuwa ba don ta gaji ba, sai dai ganin lokaci na qurewa kuma ga salloli akawunansu( ibada).

Haka taro yawaste kowa ya kama hanyan komawa masauqin sa ƴaƴan Sarakunan, ƴan gari kowa ya koma gidan sa wasu kasuwan su. Gimbiya kuwa ta koma gida da kuyangu ta,ranta wasai!!
Ta sani in dai tayi haka ba mae samun daman kada ita.
( uwar ɗakina mehwish a rage fariya ba musan ikon allah ba).

^^^^ yarinyar da aka kawo wa maganin ta sha ta warke. Sai sam barka, da izinin Allahn da ya sauqe mana magani kamun ya sauqe cutan, duk zafin ciwo da jimawan sa gashi yarinyar ta warke! Masha Allah...

^^( Abun da wasu suka kasa fahimta, shi Allah be sauqe kowanne cuta a duniya ba sanda ya sauqe maganinta, ita ciwo kaffarane
Allah bawa marassa lafiyan mu gida da asibiti lafiya!
Masu lafiya Allah qara masu lafiya!
Wa ɗanda suka rigamu gidan gaskiya Allah masu rahama!
Allah ravamu da iyayenmu lafiya
Alfarman rasulullahi sallallahu alaihi wasallam.)^^

Abba ne zaune da Umma suna hira kasancewan A𝙢𝙟𝙖𝙙 baya nan. Yaje kawo masu magun gunan da Abbansa ke saida wa yake kuma amfani dashi
Abbane yace M𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢𝙖𝙩𝙤𝙪 𝙣𝙖 kin kuwa ga Abinda aka yi yau? Murmushi tayi ni kuwa nagani Abban jarumin Umma. Nifa ko a tarihi in ba de na manta bakam to ban taɓa gani ko jin labarin mace haka ba, in bade a mutanen da ba.
Anya ma macece? dariya Abba yasa wato de anya macece kike cewa. Ta ya za'a nemi mata aure tana ba mace ba tom? Maryama.
A haka dai suke ta hiran su, kasancewan duk suna wajen akayi gasan.
Chapter 8 · 0% Book details