← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 61

Sashe 14

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

After kaman 1 hour na dawo palourn
Zaune suke sun gama cin abincin hira suke cikin nishaɗi da farin ciki!! Ameera ce tace "habeebyn Ummeyh wai yaushe zaka Bauchi ne? Kakus fa tana neman ka" caɓ gashi Ni kuwa ban shirya zuwa Bauchi ba. Umma ce tace "Aikuwa sai kaje dan nice nan zan kora ka" tura baki yayi Umma bakison ganina ko? Carab Ameera ta amsa "ai kuwa Umma ke son ganinka kai dai asirin ka a rufe ka kama hanyan Bauchi state gobe. Harara ya doka wa Ameera ko ba gobe ba kam sai ta ganni. "Haba bros angon Kakus so kake Amarya ta buga mu a court in bata ganka ba" Daddyn Little ya faɗa yana dariya. Tura baki soja yayi ya kalli Umma!! Murmusawa tayi tace "ku fita idon Auta na ko na saɓa maku son kai da Ameeran, sunkuyar da kai Daddyn Little yayi yana "Allah huci zuciyan Umman mu mun daina.
Dariya Soja ya saka!!! Yace "sistor kinsan mai na tuna kuwa?" Girgiza kai Ameera tayi a'a ban sani ba sai ka faɗa. Dariyan ya kuma sanya wa amma dai gaskiya storon ki yayi yawa sistor wai ɗaxu kin ganki kuwa, Kinga azara'ilu kawai abinki. Harara ta masa ta haɗa fuska!! Daddyn Little ne yace "karfa kaga kai soja kasan dai mun girme ka kuma zamu iya maka bulala kabar taɓa Adda Babba. Umma ce ta murmusa in ga mai taɓa mun Auta inaji dai ba sharri ya mata ba. Haka suka ci gaba da hiransu tsakanin su suna darawa!! Kowa farin cikin ganin soja ne tattare da shi.
Abba kuwa kaman yafi kowa jin daɗin ganin ɗan nasa barin ma da ya gajesa a dai-dai lokacin da yake kusa da yin retire a aikin nasa. kasancewan shekaru sun ja kuma gashi babba sosai a cikin sojojin. Farin ciki yake sosai na ganin iyalan nasa kuma cikin farin ciki, yana kuma gode wa Allah da addu'an wanzuwar farinciki na har abada a gare su. Sai dai gefe guda na zuciyar sa, yaron sa yake tunani yana jin inama ace dashi duka a zaune anan wata qila da shima har da iyalan sa.

Umma ke stokanan Autan nata. "Wai yaushe zaka je ɗauko mun yarana en tunda ka dawo gida" ɓata fuska yayi! Umma nifa in yarinyar nan Maha tazo gidan nan Tom barinsa zanyi ah to don tamun fitsaran ta bubbuge ta zan yi.
Dariya suka saka duka! har da Daddyn Little dan Abba ya tashi ya shige ciki shikam
"Shikkenan kuwa na huta sai ka tattara ka koma Bauchi ko Barack" inji Umma. Wato haka za kice Umma, tom ba inda zan je itace dai ba zata zo ba tayi zaman ta inma zuwan dole ne tom Mahreen tazo dan ta fita hankali. Daddyn Little yace "a'a bros karfa kazo gaba kana cewa na taya ka bata haquri ta yarda ta aure ka". Haɗa fuska yayi!! Umma dai dariya take yi ɗan dama tasan kwanan zance in dai zance ne akan Mahar.
Little dake maqale jikin uncle en nasa yace "gilani cibal mawa unkul daliya a'aco..

🌼 DAJII🌼
Yana hayewa saman dokin suka juya da niyan tafiya. Ido biyu yayi da wannan stohon da suka haɗu ranan (wanda ya basa maganin da yake nema) ba tare da yaji alaman tafiyan zuwan sa ba ko wani alama kawai juyowan da yayi ya gansa. Yaji mamakin ganinsa amma yaboye mamakin!!
Murmushi stohon yayi! yace "yarona sai gida ne?" Gaida shi Amjad yayi tukun na bayan ya amsa, sai yace "eh baba gida zan koma naa samu abun da na fito neman.
Stohon Yace "tom yarona hakan yayi kyau ko Ina fatan dai baka storita da gani na ba? Duk da nasan dama kai ɗin jarumin duniya ne ba mai tsoro ba." Murmusawa Amjad yayi ba komi baba namaji daɗin ganin ka
Stohon ne yayi murmushi! Bakin sa wanda kaman ba haqora ya washe yace "yauwa yarona. In kaje gida yau iyayen ka zasu maka wani magana inaso in iyayenka sun umurceka da yin abunda zasu faɗan maka yau ka amsa kaji.
Yace "tom baba duk da dama ban kasance mae masu musu ba, komi Ummata tace ina yi in bai saɓa Addini ba! stohon Yace "haka ake son yaron kirki dama ina mai maka fatan alkhaeri Muhammadu, sannan ka rage yawan karatun Qur'ani da qarfi acikin dokan jejin nan Allah tsare ka ya kare ka akoma gida lafiya."
Godiya ya masa, ,zai wuce yace sannan ko daa me wannan abun dake tunkarar ka yazo maka karka damu Yarona. Allah na tare da kai kuma ina tare dakai sannan kai ɗin mai Sa'a ne mai kawo dai-dai to ga al'umma. Ka amshi koma menene, domin hanya ce ta buɗin haske da farin ciki a rayuwarka ina mai maka fatan nasara. suka yi sallama ya juya ya kama hanyan gida dan tabbas yayi kewan Umman sa!!
Ya kama hanyan gida yana tafiya bisa dokin sa a wannan dokan daji da baka jin komi sai kukan stunstaye. Mamaki ne cike da ransa na abubuwan da ke faruwa tsakanin shi da wannan dattijon. yanzu ma shi ai a iya sanin sa cikin farinciki yake zaune tare da iyayensa. Amma dai koma me zai yi yacce stohon ya umurce sa da kuma yacce iyayensa zasu umurcesa. Sunyi nisa sosai da tafiya ba abinda yake sai karatun Qur'ani a zuciyar sa tunda stohon can ya masa faɗa ya daina ɗaga murya Insha Allahu...
Chapter 14 · 0% Book details