Sashe 22
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Gimbiya gaba ɗaya tun barowan ta wajan gasan jikin ta yake mace sai dai ta rasa dalili kwata kwata batajin haushi ko wani abun gatanan dai kawai, wanka tashiga a wajan wanka ta dirje bakinta har kaman zai ɗaye abinka da farin fata ga laɓɓan nata pink, ta dirje har kaman zata yi kuka dan ko ya ta rufe ido ganin kaman a lokacin ya sumbace take.
Gaba ɗaya ta rasa nustuwanta, qarshe haka ta fito toilet en ta kwanta ta zubawa saman ɗakin ido.
Tana cikin wannan halin jakadiya tayi sallama a qofan ɗakin nata, bargo taja ta rufe jikinta kamun ta amsa Sallaman, shigowa jakadiyan tayi kanta a qasa tace "ranki shidaɗe mai martaba ne yayi qiranki" tafaɗa tana qara qasa da kanta. Da Tom kawai Gimbiya ta amsa, jakadiyan ta tashi ta fice a ɗakin.
Tashuwa Gimbiya tayi ba dan taso ba ta shirya cikin dogon riga ta yafa veil nata har ta rufe fuskanta yacce ta saba kamun ya fito a ɗakin, a palourn ta ta samu jakadiyan da sauran hadiman ta, tana fitowa suna mata Barka da fitowa Gimbiya. Ko kallon su batayi ba bare su samu arziqin a amsa masu, tawuce tayi gaba hanyan da zai sada ta da sashen mai martaba ta nufa dan tasan yana can in dai ya qira ta haka baya wajan Ammaahn ta.
Da sallama ta shiga shashen mai martaba, kuyangu sai durqusawa suke suna gaida ta, ɗaga hannu kawai take musu ta wuce, ko da ta iso qofan palourn mai martaba kuyangun ta stayawa suka yi dan ba'a yarje masu shiga wannan palourn ba. Duk juyawa suka yi ta shige palourn, "Assalamualaikum" tayi sallama jin shiru ba'a amsa mata bane yasa ta tura qofan ta shiga ta samu waje ta zauna jiran fitowan mahaifin nata.
Tana zaune taji anyi sallama a qofan, amsawa tayi aka buɗe qofan aka shigo da mamaki ta ɗaga kanta dan taga waye ne???
Muje zuwa................
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 33&34
💋💋 امى بتولة💋
Waziri ne ya shigo palourn, ganin waziri ne tayi mamaki amma sai bata ce komi ba. Gaida waziri tayi ya amsa mata da fara'a, yana mata sannu da gajiya, Murmushi tayi.
Waziri ya buɗe baki dan tambayan ta mai martaba sai suka jiyo sallaman sa, qarasa shigowa palourn nasa yayi ya samu waje ya zauna. Gimbiya dake durqushe a qasa ne tace "Barka da fitowa Papa" yauwá Gimbiya sannu da gajiya, amsawa tayi.
Waziri sauqa qasa yayi ya durqusa yana "Barka da fitowa
Mai martaba." amsawa Sarki yayi yace "Waziri lafiya kuwa?" Lafiya lau ranka shidaɗe ansanar da yaron saqon qiran da ka masa sannan kuma baqin nan wai in ba damuwa suna son magana da kai. Mai martaba yace "shikkenan a masu iso zuwa ɗayan palourn baqi, ina zuwa". Tashuwa waziri yayi yace "Tom a fito Lafiya Mai martaba" ya juya ya fice a palourn.
Duk zancen da Sarki da waziri keyi tana jin su sai dai kanta na qasa. San da waziri ya fita kamun ta ɗago ta gai da mahaifin nata, amsawa yayi cikin fara'a dan kana ganin fuskan mai martaba kasan yau cikin farin ciki yake.
"Gimbiya Mehwish ina mai tayaki murna a mastayina na mahaifin ki, nasan ko ban faɗa maki ba kema kinsan kinyi Sa'an abokin zama Insha Allahu, ko yau na faɗi na mutu Alhamdulillahi nasan wannan yaro zai riqeki ya riqe wannan Masarauta ba tare da son zuciya ko zalunci ba, acikin sharruɗan gasa na abinda za'a baiwa wanda yaci gasa kinsan har da maganan kasa dukiyata gida huɗu na bawa wanda yaci gasan kaso ɗaya cikin kaso huɗun, amma abun burgewa anan da mamaki shine yacce zamanin nan da muke ciki ya ɓaci jama'a da son kuɗi har kashe rai ake akan dukiya, wannan yaro ya nuna bazai amshi dukiya ba ya yafe, inaji a jikina wannan yaro alkhairin ki ne kuma muma alkhaerin mu ne duka, bana buqatan ki da jayayya ko nuna wani hali daban, ke ƳAR SARKI CE amma inaso ki sani a wajan Allah ke ba kowa bace in dai bakya bin dokokin Allah da kuma son Manzon Allah SAW, shi wannan matsayi da kike da Allah ya baki ne dan kisamu lahiran ki dashi, kyautatawa talakawanki, mu'amala da jama'ar ki ba nuna haqidanci ko zalunci, acikin dokokin Allah har da Aure don sunna ne na mafi soyuwa acikin halittun sa Annabi Muhammadu SAW, hadisin Manzon Allah SAW yace, in zamu nemi Aure mu nemawa yaranmu Uba nagari/Uwa tagari, mai Addini, mai adalci, ba mai dukiya mara hali ba ko mai kyau mara kamala ba, Ako da yaushe ina yawan faɗa maki kibar ɗaukan wannan mastayi naki na Gimbiya ƴar Sarki abakin komi, ki duba Annabi Dawud (AS) irin dukiya nasa da matsayi nasa amma duk da haka yana mu'amalantar jama'a staftacciyan mu'amala, sannan ɗan sa Annabi Sulaiman (AS) wanda in dai mulki ne da ɗaukaka Allah ya bashi amma shima bai zamana mai amfani da wannan dama wajan cutar da jama'ar sa ba, duk wannan abubuwa da nake faɗa maki da misalai da nake kawo maki inaso ne kada ki taɓa cewa ke kaza ce shi kuma kaza ne kinfi qarfin Auran sa, ke kika saka wannan sharaɗin kuma an cika maki, karki ja da lamarin Ubangiji ko gorantawa ga wani dan bai da mulki Allah inyaso zai amshe mulkin a hannunki ya bawa wanda yaso (innallaha yuhlikil mulka liman yasha) dan haka ki amshi wannan zaɓin Ubangiji gare hannu bibbiyu kigode masa sai kiga ya qara maki, Allah Ubangiji ya maki albarka, Allah albarkaci rayuwanki da ta zuri'an ki" tari ne ya sarqe sa ya sa yayi shiru ya fara tarin.
Ruwa ta tashi ta ɗibo a cup ta miqa masa, amsa mai martaba yayi ya sha sanda tarin ya lafa kamun yace "inafatan kinji abun da nace da kyau?" Kanta a qasa tace "naji Papa Nagode kuma Insha Allahu akoda yaushe zan kasance mai aiki da maganan ka, Allah ja kwana ya baka tsawon rai, Allah qara lafiya" da Ameen mai martaba ya amsa yana murmushi! Daga kai yayi yaga agogon dake maqale a bangon palourn nasa yace "Allah maki albarka in yayi daga baya zamu sake magana ko yanzu baqin nan najira na ina tunanin sauran zasu tafi ta wuri gobe in Allah ya kaimu, kije ki kwanta ki huta gajiya ko sannan gobe ki shirya tarban baqonki" mai martaba ya faɗa yana miqewa. Inshà Allahu Papa Nagode Allah qara girma, ficewa mai martaba yayi a palourn ya nufi palourn da baqin nasa suke. Bayan fitan sa Gimbiya ajiyan zuciya ta sauqe ta dafe kai "Ni Maryam dama mai zance inba Alhamdulillahi ba" ta faɗa tana miqewa itama ta fice a palourn ta ja masa qofa ta fita a shashen mai martaba gaba ɗaya.
Sashen mahaifiyar ta ta nufa, da sallama ta shiga ɗakin, direct gadon da Ammaan ta take kwance ta nufa ta kwanta gefen ta tana ajiyan zuciya a haka har bacci ya ɗauke ta.