← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 61

Sashe 48

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murmushin da ya yalwata a kyakkyawan fuskansa shi ya tabbatar mun da wacce yake jiran isowanta ya hango
Juyawa nai dan ganin ko wacece haka yake wa wannan murmushin, Abun da ya ban mamaki wata ƴar dattijuwa na gani wacce a shekaru za tayi sa'an Umman sa, murmushin ne itama a shinfiɗe a fuskanta wanda yawan shekaru basu ɓoye kyawunta ba.
Tafiya take a hankali kana ganinta kaga babbar mace wacce kudi da hutu suka zauna mata, sanye take da dakakkiyar shadda ruwan bula ( blue) wanda akai wa ɗinkin dogon riga wuyanta sanye da sarqan gold da kunnensa da zobunansa duka ta yafa farin mayafi qafanta kuma sanye da takalmi kwantacce(flat shoe, Gucci) me ado da stone's blue.
fara ce sol kyakkyawar gaske wanda in ba idonta ka gani ba ba zaka ɗauka tana da shekaru sosai ba(mace sai da gyara). Wayanta ta ciro a bag en dake hanunta (Black Gucci back) tana qoqarin qira taji anyi hugging nata, murmushin dake fuskanta ne ya qaru dan tasan bame mata haka se shi ɗin.
"Habeeby karka ya damu a bainin nasi fa ace ga qatuwa ta faɗi" ta faɗa tana jan kunnen sa.
Dariya yayi yace "Ummeyh bafa iya ya dake zan ba kema kin sani Hajiya Ummeyh Autan Kakus" karɓan trolly enta yayi, Joseph drivern sa yazo da sauri ya amsa yakai motor.
Yace "Ummeyhna welcome to Nigeria, Ummeyh even Nigeria miss you taklless of we and ur old mother"
Murmushi tayi bata ce komai ba, suna isa wajan motorn joseph ya buɗe mata back seat ta shiga tana me ambaton sunan Allah da godiya garesa.
Shima Soja shigewa mazauninsa yayi
Joseph bayan ya kulle masu qofa ya zagaya ya shige mazaunin driver, ya tada motor suka ɗau hanyan gida .
Habeeby ina dai fatahn ba wanda yasan kazo ɗaukoni ko?
Soja yace "Babu Ummeyh sai little kuma shima kinga bacci yake"
Au wai wannan yaron wajan uwata ce eh lallai ikon Allah haka ya girma kace Ummanku na amsan kuɗin cafane ita kaɗai shiyasa take freshh abunta.
Ummeyh wani kuɗin cafane Umma ke karɓa kuɗin rigima dai, dan ma yanzu kam ya samu uwar ɗaki shugaban marassa ji irin sa.
Ummeyh Murmusawa tayi dan ta fahimci wa yake nufi sai tace "koma dai me ku kuka sani kuma kunfi kusa, nidai yanzu gani kuɗin cafene har da ni, Yayana na gida Ko?"
Eh Ummeyh Dukansu ma suna gida na barosu.
Ajiyar zuciya Ummeyh ta sauqe tana maijin wani sanyi yau za taga ƴan uwanta bayan shekaru da dama da suka ja bata ko leqo Nigeria ba kuma dukansu sungullolinsu basu barsu sunje wajanta ba.
GRA Kaduna, sun shigo anguwan nasu shiru kaman ba mutane, gaban tangamemen gate ɗin gidan general Haruna wanda tun daga waje sojoji ne ke tsaye riqe da bingida, horn Joseph yayi, a take aka buɗe gate ɗin sanin horn ɗin motorn waye, Shiga suka yi har wajan qofan shiga palourn ya tsayar da Motorn.
Ummeyh ta sauqa bayan ta ɗauko little wanda ke sharan baccin sa a kafaɗanta, Soja ma sauqa yayi yace "Ummeyh na wannan lukutin yaron zai gajiyar dake kawo sa" ya faɗa yana miqa hannu ta bashi Little.
Murmushi Ummeyh tayi "mijin nawa ne lukutin? tom ku ya ɗauko ai kuma lutayen ne" ta faɗa tana miqa masa Little ɗin, amsan sa yayi yasa shi a kafaɗa, kusta kai cikin palourn Ummeyh tayi bakin ta ɗauke da sallama..

Joseph yaja motorn parking lot yai parking ya fito yazo gaban soja yana sara masa yace "Sir make i help you with the boy"
Soja yace "No leave am just take the luggage and come with it inside"
"Okay sir" Joseph ya faɗa yana juyawa ya kwaso kayan kaman yacce ogan nasa ya umurcesa yabi bayan Soja da tuni ya kama hanyan shiga cikin gidan.
"Assalamualaikum" Ummeyh tayi sallama a qofan palourn tana neman izinin shiga, Abba dake zaune a ɗaya daga royal chairs en dake palourn yana aiki a system ne ya amsa sallaman ba tare da ya ɗago ba.
Umma na dinning area tana haɗowa Abba Black tea tajiyo sallaman ta amsa itama
Qarasa shigowa Ummeyh tayi tana faɗin "ayoyooo yayana" sai sannan Abba ya ɗago kai dan tabbatar da muryan da kunnen sa ke jiyo masa, da mamaki ya zare glass ɗin dake maqale a idonsa yana cewa "boɗɗi ke nake gani ko kuwa waye?"
Aikuwa ba tare da duba girmanta ba ganin yayanta da ɗan saurinta ta qaraso ta rungumesa yaya nice boɗɗin ka yaya nayi kewanku, Shima rungumetan yayi yana marhababukee boɗɗin yaya mutanen jiddah, Sannuki da hanya qanwata.
Umma dake qarasowa palourn jin hayaniyan su ja tayi ta staya da mamaki, yallaɓoi wa nake gani dai kaman Gwaggon yara? murmushi yayi yace "itace dai aminatu"
Ai da sauri ta ajiye cup en Black tea en a center table ɗin dake gaban mijin nata, rungume juna suka yi itaida Ummeyh.
Umman yara ashe rai kanga rai? Ummeyhn su wannan zuwa haka ba alert ba flashing please call me yo ai ko ɗan beef ɗin nan da ake na corona kya mun nasan kina hanya, dariya duka sa suka qara rungume juna suna dariya.
Amun afuwa Umman yara so nake nai maku surprise ke da yaranki da yayana shiyasa banyo maki beef ɗin ba
Murmushi Umma tayi ai kuwa kinyi sai dai ni banji daɗi ba gaskiya yo ai da kin sanar dani da ko raquma ce na kadar na ferfesa maki
Tom Uwar gida ran gida kuma amaryata ai mun afuwa, kuma yanzuma bai ɓaci ba Kinga dai na tayaki ko gyara kayan yaji ne, murmushi Umma tayi haka zaki ce ai, yanzu dai ga waje zauna bana kawo maki ruwa
Dede soja sun shigo da little ya ajiye sa a kan kujera yace "Ummeyh nah sannu da gajiya fa" Tray ɗin da Umma ke isowa da shi ya amsa ya qariso dashi gaban Ummeyh ya ajiye yasa mata ruwan ya miqa mata.
Amsa tayi ɗan albarka habeebyn Ummeyh sannunka da ɗawainiya, Ummace tace "ai kuwa dai habeebyn Ummeyh dan shi kaɗai aka faɗawa ana zuwa da ike shi ana sonsa mukam sai akaimu bolar jiddah
Ummeyh ajiye ruwan dake hannun ta tayi tana dariya, wato dai Umman yara kin ranste sai kinsa na qware, baki haqura ba ko to shikkenan aqara mun afuwa dan ko shima habeeby sanda na iso ya san da zuwa na.
Abba Murmusawa yayi yana sauraran su can sai yasa baki a hiran nasu yace "boɗɗi fita harkan ta so take ta wahalar dake da surutu ko hutawa ba kiyi ba"
Soja tashuwa yayi yana dariya yana jin qaunan iyayen nasa ba ruwan su in sun haɗu kaman yara qanana, hanyan da zai sadashi da ɗakin sa yayi yabar su a palourn suna hiran yaushe gamo, a ransa kuwa yana mamaki ko ina yaran suka shiga basu ji shigowan Ummeyh ba duk da uwar marassa jin.

Umma tace "za kici abinci ne ko za muje ki watsa ruwa tukun Gwaggon yara? Ta faɗa tana idonta akan Ummeyh.
Ah ah matar watsa ruwa dak tukunna duk da de nayi missing na girkin ki uwar gida ran gida, Umma tace "Ai inde girki nane kam zakici har sai ya gimsheki yanzu kamma nida yara na dan made kin shigo Babu flashing kin samu sunje saloon bamu san da zuwan ki ba da mun sani na tabbata ba inda za suje.
Ahh no wonder shiyasa naji gidan shiru oganniyan marassa ji bata nan inji faɗin Habeeby Soja.
Au kema biye masa kike ko Ummeyhn su, tom dan kuji shi ɗan naki da oganniyan marassa jin zamu haɗa sa sai suje yaga rashin jin da kyau kuma maga qarshen sharrin sa. Ummeyh dariya ta sa "in dai yarona baya so baku isa ba atou" ta faɗa tana miqewa tayi hanyan ɗakin da yake dama masauqin ta ne ko yaushe in tazo.
Shiga tayi tana mai qarewa ɗakin kallo, gaskiya a duniya ba abinda zancewa yaya da matar sa sai Allah qara masu zaman lafiya ya raya zuria'a gaskiya yaya yai sa'an mata wallahi, Allah dai ya saka maku da surakunai nagari.
Sosai taji daɗin ganin ɗakin da yake mallakinta a gyare staff kaman wanda suka san da zata zo, rage kayan jikinta tayi ta shige wanka.
Kayayyakin ta da Joseph ya shigo dasu Umma ta jida tana kai mata ɗaki, bayan ta gama ta jawo mata qofan ɗakin ta rufe ta wuce kitchen Dan haɗa mata abinci me sauqi da kanta (me aikinsu tayi tafiya).
Chapter 48 · 0% Book details