← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 61

Sashe 33

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

𝙒𝘼𝙎𝙃𝙀 𝙂𝘼𝙍𝙄
Qiran sallah na farko a kunnen Umma dake kwance kan sallaya, miqewa tayi ta fita dan hura wuta tunda yau sammako tilon ɗan nata zai yi. Ana kiran sallah ta tada mijin nata shikuma ɗan nata da kansa ya fito suka yi alwala suka nufi masallaci dan samun jam'i, itama alwala tayi ta wuce dan gabatar da nata Sallahn.
Kamun gari ace ya waye ta kammala komai ta shirya komai wa yaron nata, har kayan d ya haɗa na tafiyan ta qara gyara masa, dawowan Amjad da Abban sa suka samu har ta ta fitowa da Amjad jakan tafiyan nasa.
Bayan sun karya a gurguje yaje yai wanka ya shirya ya fito dan tafiya, Umma ce ta kalle sa murmushi ta sanya sai kuma ga hawaye ya biyo idanuwan ta da sauri ta goge su dan kar ɗan nata ya kalla.
Har qofan gida Umma da Abba suka rako sa, ba zato ba tsammani motor suka tarar a qofan gidan, dogari ne ya fito ya durqusa yana kwasan gaiusuwa, amsawa Amjad yayi yana masa kallon neman bayani.
Dogarin yace "ranka ya daɗe Gimbiya ce ta aiko mu a kaika airport" lumshe ido Amjad yayi yace okay ina zuwa ga kayan kasa a motor. Umma ta murmusa a ranta albarka kawai take sawa surkar tata da ɗan nata, bankwana yayi da iyayennasa suna masa addu'an adawo lafiya da kuma fatan nasara, durqusawa ya ɗan yi Umma ta shafa kansa "Allah maka albarka ka kula sosai" tana gama faɗin haka ta juya tayi cikin gida tana share hawaye. Kallon Abba yayi zai yi magana, saurin taran numfashinsa Abba yayi yace "jeka kawai karka damu ka kula sosai".
Juyawa yayi ya shiga Motorn yanawa Abban nasa murmushi har motor nasu ya ɓace suka ɗau hanyan 𝙌𝘼𝙏𝘼𝙍 𝘼𝙄𝙍𝙋𝙊𝙍𝙏 dake babban birnin 𝘿𝙊𝙃𝘼.
Sun ɗau awanni shida suna tafiya kasancewan Masarautar Qubaish babban gari ne sosai sannan kuma Doha akwai nisa tsakani. Sun isa ya samu tuntuni Mai martaba ya sa an kammala masa komai na issuen tafiya sai dai kawai ya jira washe gari jirginsu ya ɗaga, har ɗakin da zai kwana dogarin ya masa jagora ya kaisa a wani babban hotel na masu hannu da shuni kusa da airport ɗin, sallama suka yi da dogarin ya masa fatan dawowa lafiya ya juya dan komawa Masarauta.

Tafiyansu sai washe gari 7am dan haka ganin kwai sauran lokaci wayan sa ya jawo dan dudduba abubuwan da Ya kamata ya sani game da qasan da zashi, bayan wasu lokuta tashuwa yayi yai sallah sannan yaci abincin da aka shigo masa dashi ba jimawa y wasta ruwa ya bi lafiyan gado ya kwanta sai dai ya kasa bacci sai juyi kawai yake, kewan ummansa ya fara tun yanxu ( niko nace faɗa gaskiya Umma ko Gimbiya? ) Lol.

bayan tafiyan sa Abba da kansa ya haɗa maganin da kuma rubutun da yace zai yi ya tura gidan sarki kaman yacce ya faɗawa yaron nasa zae tura musu, ko da ɗan saqon yaje hannu bibbiyu sarki ya amshe sa sannn ya haɗa masa da tukuici.

WASHE GARI wanda yayi dai-dai da ranan juma'a qarfe 7am jirgin su ya ɗaga sai qasar NIGERIA (qasarmu ta gado).🛫
Lokacin sa na farko kenan da yahau jirgi amma ba mai kallonsa yace hakan, idanuwan sa a lumshe suke yanajin wani nistuwa na ziyartan sa wanda baisan dalilin sa ba. Bayan wasu awanni Jirgin su ya sauqa Lafiya a airport ɗin dake babban birnin ABUJA NIGERIA.

Hamdala yayi ganin kansa a qasan da bai taɓa mafarkin zuwa ba, da bismillah ɗauke a bakin sa gami da addu'oee yayi stepping qafan sa dan fita a jirgin yana kallon ko ina da kyau, yanayin yacce mutane kowa ke harkan gaban sa a wajen sai yaji qasan ya burge sa. Wayan sa ya jawo ya duba ganin da sauran tafiya gaban sa na zuwa garin da yake da tabbacin a can zai samo abun da ya kawo sa, cikin hanzari yaja jakan nasa ya na mai neman taxi.
Taxi ya samu ya tare suka shirya zai kai sa tashan da zai hau motor zuwa Bauchi. Har sun fara tafiya da mai taxi sai motorn ya tsaya cak alaman ya samu matsala, Gashi kuma sun yi nisa da airport.
Mai taxi yace sai dai ya sauqa ya nemi wani abun hawan dan gaskiya in da zai je ya taho da makanike ba kusa ba kuma ba hanyan da zai kaisa tashan motoci bane, Haka badon yaso ba ya sauqa.
Tsayawa a bakin hanya yayi ko zai samu motor sai dai ganin ta gefen da yake ba alaman motor shiru kawai sai ya shirya tsallakawa ɗayan gefen ko zai samu ko lift ne.

Daddyn little ke driving da gudun gaske yanayi yana duba agogon dake maqale a hannun sa kasancewan yau juma'a sauri yake dan ya samu ya koma gida kan lokaci ya shirya ya tafi masallaci, yau ba'a tashesu aiki da wuri ba ya kusa makara.
yasa kai zai tsallaka titi riqe da jakan sa, Motorn Daddyn little ne ya danno kai a guje ba tare da ya kula da wanda ke qoqarin tsallaka hanya ba.
Kamun mai tsallake hanya yayi qoqarin yin gaba ko baya dan kaucewa Motorn ba zato ba tsammani ji kake qiiiiiiiiiiiiiii tibbbbb
Motorn ya ɗaga mutum sama ya fado qasa Daddyn little dake tuqin sai da kan da ya garu da stairyn.
LA ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM shine abunda Daddyn little ya furta bai ko damu da buguwan da kansa yayi ba ganin abunda yake kaucewa ya faru dafe kai yayi yace "Sauri ba wajan zuwa, ya ilahi".
Fita yayi a Motorn nasa ya tsayar da wani motor dake wucewa, mai Motorn da ya tsayar ya taimaka masa suka sanya mutumin daya buge a motorn sa.
Godiya ya masa ya ja Motorn ya juya kan Motorn nasa ya nufi asibiti.

Babban asibiti ne na masu kuɗi ya kaisa, kasancewan yana da aboki a asibitin ba tare da an buqaci zuwan police ba aka amshi patient nasa.
Abokin nasa ne ya kalle sa yacce ya damu yace "freind relax bákomi insha Allahu" ajiyan zuciya Daddyn little ya sauqe plss kuyi duk abun da ya kamata zan dawo yanzu frnd ba naje mosque na dawo, likitan yace "okay freind Allah qara starewa kayi tuqi a hankali, Da damuwa ya ja Motorn nasa ya kama hanyan gida yana mai addu'an Allah yasa bai kashe ɗan mutane ba.

Yana shigowa palourn nasu da sallama Ameera ce ga miqe da mamaki tace "Husby lafiya na ganka haka jikinka da jini mai ya faru?"
Dafe kai yayi wiffey tsautayine ya sameni yau, nan ya kwashe labarin abinda ya faru ya faɗa mata.
Rikicewa tayi harda hawayen ta! Allah sarki bawan Allah, Lallashinta yayi yace in ya dawo masallaci xasu asibitin tare.
Shiryawa yayi ya tafi Masallaci, Allah ya taimake sa ya samu jam'i bayan an idar anshafa addu'a liman ya fita kamo hanyan gida yayi gaba ɗaya a rikice yake bai taɓa hatsari ba a rayuwansa yana storon ya zama sanadin da wani zai rasa rayuwan sa.

Bayan fitan Daddyn little Ameera na zaune sai ga qiran Ummanta ya shigo wayan nata,. Ɗauka tayi suka gaisa Umma tace "Ameera ya naji muryanki haka ko ba lafiya ne? ko dai jikin naki ne?"
Kaman tana gaban Umman haka take girgiza kai
Umma tace "ya naji kinyi shiru? share hawaye tayi! Umma baniba ce Daddyn little ne yayi hatsari
"Hasbunallahu wa ni'eemal wakeel" shine abunda Umma ta furta, da ban qira ba ba zaki faɗa mana ba kenan? Garin yaya yayi hastari? Ya jikin nasa?" Umma ke jero mata tambayoyi.
Umma bafa shi da kansa ba ina nufin ya buge wani ne. Ajiyan zuciya Umma ta sauqe! Amma duk da haka jikinta yayi sanyi taji kaman wani nata aka buge addu'an Allah sauwaqa ya kare na gaba tayi masu tace "Insha Allah Abbanku zai shigo Abuja dama this week in yaso sai ya iso wajan ku ya duba mai jikin nikam bazan samu zuwa ba gobe su Auta zasu Bauchi Kar abar gida ba kowa" shikkenan Umma Allah ya kaimu Allah kai su lafiya suma Mun gode Allah qara girma. Sallama suka yi tana mata faɗa ta rage yawan sa damuwa da kuma tashin hankali a zuciyarta cikine qarami da ita karya zamo mata matsala yanzu ko nan gaba "tace Insha Allah Umma zan kiyaye a gaida su M𝙖𝙝𝙧𝙚𝙚𝙣. Bayan sun gama wayan aje sa tayi dan ta gabatar da sallah kuma ta shirya ganin lokaci yayi an sauqo juma'a.
dawowan sa masallaci yayi dai dai da ta futo wanka, taya ta qarisa shiryawa yayi dan su samu suje asibitin.

---
bayan Umma ta ajiye waya Auta ne ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama.
Umma zamu masallaci ina big broh na?
au wai bai je wajanka ba? To jeka dubosa a waje yashirya tun ɗazu yace zashi ɗakinka ku tafi, Kallonta yayi har xeyi magana sai bece komai ba ya fita.
A jikin Motorn da zasu fita ya samu little na jiran sa yasha jamfa murmushi yayi yace "looking gorgeous my son"
Tacuu Unkui.
motor suka shige sai masallacin juma'a

__
Abba ke shiryawa dan zuwa masallaci ransa a ɓace ganin ko yaushe in zai fita tana taya sa shiri amma tun jiya tafiyan yaron ta daga ta zauna sai tagumi.
Kallonta yayi yace "maryama wai yau kam baza'a taya ni shiryawa ba kuma ansani a gaba da tagumi da hawaye mai yake damunki ne?
Ko duk kewan ɗan nakine tun ba'ayi nisa ba?
Ajiyan zuciya ta sauqe, ba kewansa ba Abban jarumin Umma Kawai Inaji a jikinane kaman wani abu ya samesa, numfasawa Abba yayi yace "A matsayinki na uwa kike masa fatan alkhairy kinji koh karki biye zuciya ko sheɗan addu'a kawai ya isar maki kinji maman amadu.
Lumshe ido Umma tayi tana ajiyan zuciya Insha Allah
Kallonta yayi ya girgiza kai dan tabbas yasan **labarin gizo bai wuce na qoqi**

Allah bai manta damu ba marayamatou nah tabbas haihuwa rahamane Amma rashin haihuwa babban rahama ne ( Allah najin kunyan wanda be bawa haihuwa ba kwata-kwata ranan gobe qiyama)
Share hawayen tayi, ta tashi muje na raka ka ta amsa hulansa tana sa masa.
Chapter 33 · 0% Book details