Sashe 21
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba Sarki kaɗai ba kowa dake wajan cike da mamaki suke kallon sa, suna qara buɗe kunnen su dan su tabbatar da gaske ne abinda suke ji, Abba dai bai yi mamaki ba dan sarai yasan halin ɗan nasa, haka Umman sa murmushi kawai tayi wanda ke ɗauke da ma'anoni da yawa, albarka kawai take sawa ɗan nata. dama tun can damuwanta ɗan ta yayi aure bawai kuɗi ba, kuma tasan ko anbasa bazai amsa ba.
Wannan abu da Amjad ya faɗa ya qara sanya Sarki cikin kogin farin ciki dan tabbas ko ba'a faɗa masa ba yanzu yasan ƴar sa tasamu miji Insha Allahu kuma ko bayan ransa yasan wannan bawan Allah zai riqe wannan gari cikin Amana, ba qaramin qara burge Mai martaba Amjad yayi ba.
Mai martaba yace "maganan dukiya alqawari ne acikin sharruɗan gasa amma duk da haka ba komi Allah ya maku albarka duka Allah nuna mana lokacin bikin da rai da lafiya, sannan zaka iya fara zuwa wajan gimbiya dan qara dedeta kanku kamun ranan biki. Baqin mu na nesa da kusa muna matuqar Godiya da halartar wannan taro da kuka yi ina mai roqon Allah subhanahu wata'ala da ya maidaku qasashen ku, garuruwanku, da gidajen ku lafiya."
Sarkin shela ne yaci gaba da jawabi da kuma godiya ga jama'a. Da kuma qara gayyatan su zuwa ɗaurin auren Gimbiya da yariman gobe inshà Allahu nan da wata huɗu.
Manyan baqi da sauran jama'a sai taya sa murna suke suna tayasa godiya.
Cike da farin ciki sarki ya haye dokin sa suka yi hanyan fada shi da fadawan sa, da sauran manyan baqi waɗan da ba ƴan garin ba.
Ƴammatan wajan kuwa waɗan da suke crushing akan Amjad sai suka fara jin kishin Gimbiya, dan tunda suka qyallare ido suka gansa duk yawanci su suka qyasa, sauran kuma dama suna kallon sa wani bin a kasuwa.
"Alhamdulillahi ni bintalo addu'a ta ta karɓu, Allah ka gani ina taya wannan bayi naka farinciki dan tabbas sun dace da juna Allah ka kare su daga sharrin masu sharri" bintalo ta faɗa hannun ta a sama!
Rahama tace "kai amma dai bintalo aiki ya ganki sai kace qannin ubanki ne shi lallai sannunki"
eh anji imma ba qanin ubana ba ai ɗan uwa nane musulmi, kuma dai dan kiji shi Hassada ba hali mai kyau bane ko kafuran zamanin Annabi SAW haddasa suka masa dan tabbas sun san shi Annabi ne, dan haka ina rabaki da abinda Annabi ya hanemu da yi, Ni dai alhamdulillahi har raina ina taya su duka farinciki both Gimbiya da Yarima Amjad insha Allahu, nan da wata huɗu kuwa har da ankon biki zamuyi, ko ba haka ba lubcy? Ah sosaima bintalo insha Allahu zamuyi anko Allah nuna mana da rai da lafiya. Rahama ko qala bata qara cewa ba tayi gaba, bintalo bin ta suka yi dan su wuce gida duka.
A hankali a hankali ake ta wastewa a filin kowa na kama gaban sa
Umma da Abba sun lelleqa basuga ɗan nasu ba, báko shakka sun san gida ya tafi dan haka suma suka kama hanyan komawa gida.
Fili ya waste shall kaman ba'a yi taro a wajan ba kowa ya koma gidan sa.
𝙆𝘼𝘿𝙐𝙉𝘼
Zaune suke a palourn har da Umma suna fira, Little dai na maqale da Maha. Ameera ce ta sauqo sanye take da mayafi, da alama zasu koma Abujan du yau ne.
Waje Ameera ta samu ta zauna jin hiran nasu sai ta kama dariya, duk sai suka zuba mata ido har dai Daddyn Little, mamaki suke dan su dai sun rasa me yasa ta dariyan.
Ummace tace " ke lafiyanki kuwa? Dariyan me kike?" dariya ta qara fashewa dashi "
Wallahi Lafiya ta lau Umma, kawai ina tunanin wannan irin zazzafar soyayyan dake tsakanin Habeeby da Maha ne, yafa kamata ayi gaggawan haɗasu a Aurar dasu in ba haka ba soyayyan zai fi haka, dubi fa yacce basa kunyan kowa ko a ina soyewa suke" ta faɗa tana dariya.
Haɗe rai Autan Umma yayi! Ita kuwa Maha turo baki tayi, tace "Ummata ki faɗawa aunty banaso, Ni mema zan yi dashi caɓɓ"
Ummace tayi murmushi tace "yi shiru abinki ki qyale ta ai kinfi qarfin sa, daughter na sai mai gida da motor da jirgin sama". Mai zasu yi a palourn in ba kwashewa da dariya ba, Mahreen har da kama ciki.
Daddyn little ne yasa baki, haba dai Umma ke da zaki ce tayi sa'a ma zata Auri soja ɗan fari kyakkyawa kuma Autan Abba, ai Umma kin sai dai Auta duk yana da abubuwan da kika lissafa. Mahreen ce tace "yauwá dai uncle faɗawa Umma ya habeeby kam in baice yafi qarfin wannan mara jin ba ita bata isa tace tafi qarfin shi ba ato"
Harara soja ya gallawa Ameera, in an rainani ma kece kika jamun, kuma ki kaita ki barota nikam bulale ta xanyi sai tayi jinya ta san halina.
Ameera qunshe dariyan bakinta tayi, Allah huci zuciyan angon Maryam sai ta kuma sa dariya!
Allah shiryaki Ameera yanzu zaki haɗa mun yara faɗa aka taɓamun yarinya akanki zan rama mata, maza tashi ki barman gida.
Tashuwa habeeb yayi ya nufi hanyan fita a palourn yana cewa "in kin gama haɗamun renin sai kuzo na kaiku airport en akwai inda zanje" ya faɗa ya fice a palourn.
Miqewa Daddyn Little yayi, Umma kina koranmu ba mu tafi muma, waje ya nufa yana murmushi! Ameera kam dariya take yi, tana cewa "Umma Autan kin nan ya renani ya rena inda na zauna ki koramu shima ya wani ce wai yana da inda zai je, inda zai je ya wuce hira cikin palourn Ummata wajan qanwaty Maha, Allah Umma yaronki yana ga kaman yanzu shine babba, baisan dai duk girman sa Ni auntyn sa bace" ta faɗa tana miqewa. Rataye jakanta tayi ta gyara mayafinta har yanzu murmushi ne a fuskan ta!
Murmushi kawai Umma tayi tace "duk kunfi kusa nice bare tsakanin ku ya rage maku Ni dai adaina takuranmun daughter".
dukansu miqewa suka yi suka nufi waje, sun samu habeeb da Daddyn Little already suna cikin motorn fitowan Ameera kawai suke jira. Har bakin motorn suka rako Ameera ta buɗe gidan baya ta shiga gefen mijin ta, ta zauna. Miqawa Little Hanu tayi my boy zo mu tafi, maqale kafaɗa Little yayi, ya qara qanqame Maha.
Kamun kowa ya ankare ko ya kula sai aka ga Maha da Little maqale a gaban Motor, Juyowa habeeb da ke zaune mazaunin driver yayi, ya kalleta yace "ki fitamun a motor ni ba sa'an yawo dake bane, hararan gefe Maha tayi, shide little bai san menene ba yace "unkui damu fika nida anci na" ya faɗa yana washe bakin sa
Habeeb ya buɗe baki zai yi magana Umma ta kallesu duka tace "kul ya isa kuje kawai Allah tsare hanya ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, su kuma Allah stare masu hanya" Suka ce Ameen Umma.
Jan Motorn yayi da gudun gaske suka fice a gidan, Umma da Mahreen na ɗaga masu hannu, bayan fitan su suma suka juya suka koma cikin gidan.
Komawa palourn Umma da Mahreen suka yi, Umma tace "daughter yaushe zakuje wajan Amarya? Umma zamuje wataqila nan da sati kamun nan mun huta, Muje muji rigiman kakus.
Dan qwalo Umma ta mata, kun raina mana uwa ko..
---
Har airport suka kai su Ameera, ganin jirgin nasu ba yanzu take zai tashi ba, sallama suka masu da addu'an Allah stare hanya ya kai su lafiya, Little har dashi a masu bye bye ba ruwan sa yana jikin Maha.
Bayan sun baro airport, juyowa habeeb yayi ya kalle ta yace "saura kuma naje dake wajan abokai na kimun fitsara agabansu mu koma gida jikinki ya faɗa maki." Turo baki tayi tace "haba dai yah habeebu Nifa ina da hankali, ba kaman sojoji ba. Su sojojin mene rashin hankalin nasu? Tun anan zaki fara kasa hali ko hmmn. Ina soja yaga hankali yah habeebu in zaka faɗi gaskiya, Haka dae suke ta rigiman su a motorn Little kam baccin sa yake sha ajikin mummyn sa Maha.
Direct eatery suka yi, saya masu icecream, shawarma da chocolate yayi, Maha dai ta kwashi tarkace don Little yana bacci.
Bayan sun fito wajan sayayyan nasu wuce wa wajan abokin nasa suka yi. Da suka isa fita yayi a motorn suna gaisawa da abokin. Man wannan ce amaryar tamu kenan, irin dacewa haka kallifa yaron sai yayi kaman naku. Hararansa yayi in kasan renani da yarinyar nan tayi bazaka ma haɗani da ita ba Man, kasan rashin jinta kuwa, ba inda zankai wannan yarinya qaramar.
Shikkenan aboki in baka ciki ni amun hanya kawai na shiga layin masu nema, dan tabbas tamun.
Hararansa yayi, ya ɓatar da maganan
Suka yi sallama ya shige motorn yaja, bai bari ko sunyi magana ba.
Gida suka koma ita kamma bacci tayi a motorn, ga little ma na baccin sa.
Kallonta yayi ga yarinya dai kyakkyawa da fuskan innocent girls amma rashin kunyanta ya fita shekaru.
-------------
Mai martaba sun koma fada ankai manyan baqi masauqi.
Ya umurce waziri da a aika aqira masa wannan yaro da yaci gasan, acikin baqin kamun su wuce gobe akwai masu buqatan haɗuwa dashi. Waziri yace "Tom shikkenan ranka shidaɗe, Allah ja kwanan mai martaba Allah gwada mana goben da rai da lafiya" da Ameen Sarkin ya amsa.