← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 61

Sashe 54

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tashuwa yayi ko takan wayansa bebi ba ya shige bayi(toilet) yana fitowa ya ɗaura alwala, cikin ɗakin ya koma yaja qofan ya rufe ya nufi masallaci.
ko da yayi Sallahn magrib bai koma ba har sanda yayi Sallan isha'ee bayan sun idar da sallan ne liman ya ɗan yi tunatar wa ga al'umma(wa'azi) yana idarwa jama'an masallacin suna raguwa har aka waste ya rage mutane qalilan.
Amjad matsawa yayi wajan liman yayi masa sallama suka yi musabaha sannan suka gaisa fuskan liman a sake ba yabo ba fallasa.
Liman yace "saurayi daga ina haka dan ban cika ganinka anan ba?"
Murmushi Amjad yayi yace "malam ni ba ɗan qasan nan bane"
Ikon Allah ikon gaske yanzu tom kazo wajan wani naka ne kenan? A'a Allah gafarta malam banma san kowa ba hasali ma ban taɓa zuwa ba yanzu ma dalili ne nazo neman wani magani ne kuma na shiga jeji sosai iya shiga na ban samu ba ko alaman bishiyar ban gani ba, kuma ance mun dama anan zan samu.
wani magani ne haka? Bawan Allah
Amjad yace "𝗭𝘂𝗹𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘆𝗮"
jinjina kai limamin yayi yace "kai aikam dole ka gama duba wa baka samu ba dan ba'a ta yankin nan ake samu ba sai ta jejin yankari ko can yankin Borno sambisa, amma yanzu dai a ina kake zaune(masauqinka)?
Yace "Allah gafarta malam nan bayan nan ne ba nisa"
Liman yace "to to shikkenan in ba matsala muje gida na in yaso daga nan sai ka wuce ko dan abubuwan na da qa'idodi nasan kasani ba ako ina ake shiga dashi ba.
Nagode Allah gafarta malam yanzu zanje gidan na haɗa abubuwa na na sallami mai ɗakin sai na zo.
to yaro shikkenan sai kazo, sallama suka yi da limamin ya fice a masallacin ya wuce inda yake kwana, buɗe ɗakin yayi ya haɗa komi nasa ya bawa mai ɗakin gefen sa makullin ɗakin shi kuma ya fito yayi gidan limamin.
Da ya isa gidan limamin tsayawa yayi a bakin qofan yayi sallama.
amsawa akayi wata budurwa ce ta amsa tace "ana zuwa".
yana tsaye yaji an buɗe qofan, ɗagowa yayi suka haɗa ido ita, kyakkyawar budurwa ce wacce a shekaru bata haura 20 years ba, ta buɗe qofan tana tambaya waye ne?
Nazo wajan liman ne, sai tace "tom ace masa waye?
Kice masa ɗan Qatar ne, qara kallonsa tayi kamun tace to ba na faɗa masa, cikin gidan ta koma can ta qara fitowa tace wai ka iso.
shigewa cikin gidan tayi yabi bayan ta tai masa jagora har ɗakin baqi bayan sun isa tayi masa iso ya shiga ya samu waje ya zauna ficewa tayi a ɗakin.
can sai gata ta shigo da ruwa a hanunta ajiye masa tayi ta tsugunna ta gaidasa fuskanta da murmushi shi kuwa ba yabo ba fassala fuskan nasa haka ya amsa.
wai kasha ruwa baban yana zuwa, okay nagode.
Murmusawama tayi ba komi sannu da zuwa ta tashi ta fice a ɗakin tana murmushi, bayan fitanta qofan yabi da kallo nustuwan yarinyar ya burgesa sosai.
Bayan mintuna da fitanta sai yaji sallaman liman, amsawa yayi yana sannu da fitowa malam yauwa yaro sannunka ko, waje liman ya samu ya zauna.
Durqusawa yayi ya gaida sa amsawa yayi yana yaro tashi abunka ka zauna, koma wa yayi ya zauna ya sunkuyar da kai, liman yace "yauwa baka faɗamun sunanka ba saurayi" kansa aqasa yace "sunana Muhammad Amjad Allah gafarta malam"
Masha Allah to naji maganin da kake nema ai abinda yasa ba zaka samesa ba a jejinmu na nan saboda wasu bishiyoyin an sassare wasu kuma ba zasu yi amfani ba mugaye sun riga da sun ɓata su wannan ɗinma abinda yasa na qiraka kar acan wani mugun ya gani ya ɓata kasan hausawa sunce shi mugu baida kama.
Hakane Allah gafarta malam Nagode sosai, a'a bakomi saurayi yanzun tunda kace kana samu zaka wuce ko? Eh malam tom mu kwana nan yau gobe Inshà Allah da rai da lafiya sai ka wuce yanzun bana shiga na kawo maka maganin, to Malam Allah saka da alheri Nagode sosai.
tashuwa limamin yayi ya fice a ɗakin yana faɗin "kaqi shan ruwan ko? sosa qeya yayi.
bayan fitan limamin komawa yayi ya jingina da kujeran yana lumshe ido dai-dai lokacin kuma wayan sa ya faɗo masa rai dafe kai yayi ya ciro wayan a aljihun sa da gaggawa.
Cikin gidan liman kuwa Bayan fitan wannan budurwan a ɗakin baqin bakin ta yaqi rufuwa murmushin dake fuskan ta yaqi gushe wa, zuwa tayi ta tsugunna qofan ɗakin mahaifin nata baba nakai masa ruwan nace kana zuwa,Tom ecleemat Yar baba Allah maki albarka da Ameen ta amsa tana murmushi ta tashi tayi ɗakin maman ta shigewa tayi da sallama qanwarta tasamu tana naɗin kaya,amsawa tayi ta juya ta kalleta yaya ecleemah lafiya da murmushi haka tun shigowanki? Kedai bari kawai deejah baqon baba ne tunda na kallesa nake ta murmushin da bansan dalilin yinsa ba.
kai de yaya ecleemah kode-kode? murmushin ta kuma yi bakomi fa. Can suna zaune suka jiyo muryan baba liman yana faɗin ta fito ta kaiwa baqon abinci.
Da murmushi ta tashi da sauri dan har ranta tana son qara kallon sa ficewa tayi tana faɗin "to baba" madafi taje ta haɗa masa abincin akan tray tayi hanyan ɗakin baqin, sallama tayi a qofan ɗakin ta tsaya jiran izinin shiga
Wayan ya ciro ya duba ga message na layin Ameerah ta tura masa sannan ga wani baqon number Wanda yake kyautata zaton na Umma ce dialing yayi bai shiga ba network babu "ya Rabbi" ya furta yana furzar da iska a abakin sa.
sallama yaji a bakin qofan sai ya amsa yace "shigo mana qanwata" shigowa tayi fuskanta ɗauke da fara'a kaman ɗazun kanta aqasa har ta isa gaban sa ta ajiye tray en abincin tana tsugunne kallonta yayi ki zauna mana qanwata kar ki gaji da stugunnon kinji.
Murmushi tayi ta zauna akan ledan ɗakin kanta a qasa layin da Ameera ta tura masa ya qira har kaman baza'a ɗauka ba ya kusa ending can aka yi picking, sallama yayi aka amsa a ɗayan ɓangaren suka gaisa.
Wanda ya qiran ne yace "afuwan ban gane da wa nake magana ba? Numfasawa Amjad yayi yace "Ameerah ce ta turamun layin ka"
Okay am so sorry AMJAD right? Eh shine.
Qara gaisawa suka yi ya faɗa masa nasa sunan shima.
Abdoul yace "yanzu kana inane nazo dan nasan da daren nan ba samun abun hawan da zai kawo ka gida zaka yi ba, no karka damu da safe dai in Allah ya kaimu sai na maka kwatancen inda nake in yaso mu haɗu kamun na wuce.
Har zaka koma kenan? Eh zan koma gobe in Allah yaso ya yarda.
To shikkenan Allah kaimu goben, Ameen ya Rabbi ya faɗa suka yi sallama ya kashe wayan.
Kallon ta yayi har yanzu kansa a qasa murmushi yayi yace "qanwata sorry ina wayane" kanta aqasan ba tare da ta ɗago ba tace "ba komi yaya baqo" murmushi yayi jin sunan da ta raɗa nasa "Au yaya baqo ne sunana kenan?" To yaya ko ruwan ma baka sha ba ga abinci ma na kawo maka in baba ya gani ba zaku shirya ba baison rashin cin abinci.
Karki damu zanci ko, me sunan ki qanwata? kanta aqasa har zuwa yanzun tace tace "𝗲𝗰𝗹𝗲𝗲𝘆𝗺𝗲𝗿𝗵"
Murmushi yayi wow! suna me daɗi amma kinsan me? Girgiza kai tayi a'a yaya na, sai yace "ban taɓa jin me irin sunanki ba amma sunanki yamun daɗi sannan da alama masu sunan suna da hankali" murmushi ne kwance a fuskanta har yanzun, to kaima yayana me sunan ka? Sunana "A𝗺𝗷𝗮𝗱" kaima sunanka da daɗi yayana.
Nagode qanwa ta murmusa wa tayi bata ce komi ba kanta a qasa.
Amjad yace "jeki abinki dare nayi ki kwanta ko Nagode sosai Allah maki albarka" da Ameen ta amsa ta tashi tana masa seda safe ta fice a ɗakin.
sauqa yayi yaci tuwon yasha ruwa yai hamdala, ko da ya gama cin tuwon bai kwanta ba dan tsabar farin ciki, butan da ke ajiye bakin qofan ɗakin baqin (wanda ecleemat ta kawo masa) ya ɗauka ya ɗaura alwala ya koma ɗakin sallayan dake ajiye gefe da carbi da Qur'ani megirma ya ɗauko ya shumfiɗa sannan ya tada sallah farinciki fal ran sa(zekoma yaga Umman sa).
Chapter 54 · 0% Book details