Sashe 59
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Maha kiji storon Allah me kike yi a dinning cikin daren nan?" Mahreen ta faɗa da mamaki.
Ga kuwa Abinda nake kin gani, abinci na gama ci yanzu zan dawo ɗakin.
Yanxu duk jimawan da kika yi abinci kike ci? Cup na ruwa ta ɗauka ta sha ta miqe tsaye, tom na gama muje mu kwanta Addah am an gama waya da ya Abdoul ɗin ne?
Gamawa tun yaushe Maha, kece ma da naga baki dawo ba na zaci ko ba lafiya ba ai.
"To Kin ganni rass nake na ma fiki lafiya" ta faɗa yayin da suke shigewa ɗakin su.
Tun da ta fita idon sa na kan qofan bai kau da ba. Me yarinyar nan ke nufi? Ina mata magana tayi banza ta wuce.
"Mtswww" tsaki yaja.
Dama ban qira ki ba ke kika kawo kanki shashasha kawai. System ɗin nasa ya buɗe yaci gaba da aikin sa in peace, amma dai qasan ran sa reaction na yarinyar na basa mamaki ko renin da ta masa har ya kai hana oho.
Suna shiga ɗakin gado suka faɗa duka ko wacce addu'an bacci tayi suka ja blanket suka lulluɓu.
Can ta leqa Mahreen gani tayi ita kam ta jima dayin bacci ma.
Qaramin tsaki ta ja tace "Ɗan renin hankali kawai wai dan an damu baka da lafiya shine har da wulaqanci wani ai mai aiki ce ta kawo masa coffee, hmnn zan rama ne ba dai ka warke ba ina dede da mutum." Juyawa tayi ta rufe idon ta dan bacci ya ɗauke ta itama.
Umma na shiga ɗakin murmushi Abban yayi mata! Ƴammata na sai yanzu aka biyo ni?
"Yallaɓoi aimun aikin gafara" ta faɗa da murmushi itama. Matata bata laifi ko tayi ma an yafe mata.
Gidiya nake yallaɓoi baban yara.
Isowa wajan da yake tsaye yana rage kayan jikinsa tayi tana taya sa rage kayan, murmusawa yayi yace "Allah maki albarka" da Ameen ta amsa ta wuce bathroom ta wasta ruwa.
Bayan ta fito shiryawa tayi cikin dogon rigan ta na bacci, zaunawa tayi bakin gadon gefen sa kallon ta yayi yace "Hajiya ta da alama dai bakinki da magana menene ya faru?"
Yallaɓoi maganan yaron da su Ameerah suka yi jinyan sa ne, an turo mun layin nasa sai dai na qira ba'a ɗauka ba da alama ko wayan nasa baya tare da shi.
Karki damu maman yara tunda gobe Litinin zamu Bauchin inyaso sai mu tafi tare daga nan sai kiga yaron naki. Maganan da yayi na "daga nan sai kiga yaron ki" ba qaramin tsaya mata a rai yayi ba hakan ya sanya tana qara jin wani iri game da yaron, wanda bata san ko menene ba?
Cewa tayi "wai dama nufin ka yallaɓoi ku kaɗai zabkuje ni ba za'a je dani na gaida Mama ba?" A'a na isa Hajiya ta qafata qafar matata.
Murmusawa tayi, Allah kaimu goben da rai da lafiya. "Ameen ya Rabbi Hajiya ta" Abba ya amsa mata.
Bayan sun kammala abubuwan da ya kamata kwantawa suka yi sai muce safiyar alkhaery.
🅆🄰🅂🄷🄴 🄶🄰🅁🄸
Gari na gama haske Amjad ya gama kimstawa ya shirya, tuwon karin da aka kawo masa ma stakura yayi kaɗan.
Gaba ɗaya yau jin sa yake cikin farin cikin nasaran samun maganin da yayi yake, gashi kuma yau zai kama hanya wanda da yardan Allah zuwa gobe zai ga Ummansa ta gansa ya faɗa mata irin kewanta da yayi, to sai dai agefe ɗaya kuma cike yake da fargaba da kuma tunani akan faɗuwan gaban dake damun sa wanda ya tabbata akwai abinda zai faru.
Lumshe ido yayi yana faɗin "Ya Rabb ka sanya komi dake shirin faruwa dani yazo da sauqi Alfarman fiyayyen halitta SAW, tabbas stinkewan zuciya na ba alkhaeri kuma ko da akwai alkhaeryh to wani babban abu dai zai faru". Yau saura sati 1 da ƴan kai wa'adin da aka ɗibar mun su cika ya kamata ace ina gida iwar haka, Allah ka iya mun.
Liman ya iso inda yake a tsaye a qofan ɗakin baqin, sallama liman yayi shiru Amjad bai amsa ba, qara Sallaman yayi shiru kuma du.
Matsowa limamin yayi ya ɗan taɓa Amjad yace "bawan Allah mai kake tunani haka? Nayi sallama bakina uku shiru baka ko ji na ina fatan lafiya kam?".
Qasa Amjad yayi da kai yana ajiyan zuciya sai yace "lafiya lau Alhamdulillahi Allah gafarta malam"
A'a kaga yaro faɗa mun gaskiya wani abu ne ya faru kuma sai kace a'a lafiya.
Can sai ya nisa yace "Allah gafarta malam gabana ke faɗuwa sosai-sosai kuma ni tun ina yaro haka nake indai wani mummunan abu zai faru to ko nayi mafarki ko kuma na tashi da faɗuwan gaba tom ina tunanin wani abun na shirin faruwa"
Lima yace "subhanallahi! To yaro ko zaka iya haqura da tafiyan nan yau ne mu koma ciki
Qasa Amjad yayi da kai cike da ladabi yace "Allah gafarta malam amun addu'a kawai amma zan tafi yau Inshà Allah yanzu ma haka munyi magana da wanda zai zo ɗauka na ya kusa isowa".
Dogon numfashi malam liman yaja kamun ya jinjina kai yace "bawan Allah ba ina nufin hanaka tafiyan ka dan abinda kake tunanin faruwansa ba a'a ko ɗaya ina hanaka tafiyan ne dan samun nistuwan zuciyanka, ka riga da ka sanyawa ranka indai faɗuwan gaba ya sameka to mummunan abu ne zai faru to shiyasa nake son ka dakatar da tafiyan naka dan kasani cewa shi mumini a rayuwan sa akwai qaddara haɗe da jarabawar Ubangiji sannan duka abu biyu wanda kusan ma'anan su ɗaya ana son duk wani mumini wanda ya yarda da Allah da Manzon sa to yayi imani da su, wani lokacin alkairi zai kawo bugawan zuciyan ka wani lokacin kuma akasin alkairi sai dai duk acikin sun akwai abinda Allah ke nufi da hakan wa lau ya ɗaga matsayinka wa lau ya jarraba imaninka sannan..." sosai yai masa nasiha mai haɗe da tunatar wa.
Ajiyan zuciya Amjad ya sauqe bayan malam liman ya ida nasihan sa, Allah ya saka da alkairi Malam in Allah ya yarda zan gyara amma ina mai bada haquri da maganan tafiyana yau, tabbas nasan komai sai Allah yaso kuma sai ya qaddara amma ina mai addu'an Allah yasa tafiyana yau ɗin ya zame mun alkairi,
Bazan taɓa mance alkairinka gareni ba malam Allah ya saka da Aljanna Allah kuma ya qaddara saduwanmu.
Amarya da hayra ne zaune a dinning area suna karyawa, shiru babu mai magana (table manners).
Da sallama Abdoul ya shigo sashen kakar tasu, ganin suna dinning tsayawa yayi daga tsakiyan palourn yace "Amarya ta gud morning"
Amarya tace "ubanka ke gudu da moni, ɗan jakar uba banson ɗiban albarka da tangaɗewa da sanyi safiya ka isheni da yaren ƴan wuta, yanzu inbanda sinqin sikitin layii da tangaɗi wai ƴan adam baza suyi yaren ƴan aljanna ba sai na ƴan wuta to haram ba dani ba ni Mairo".
Tunda Abdoul yayi magana hayra ke dariya har amarya ta qare sababin ta dariya take har da kama ciki "ko shima ya Abdoul me ya kaisa oho" ta faɗa tana dariya qasa-qasa.
Amarya Juyowa kanta tayi tace "matar ubanki hansatu ce ta kaisa, ba dai matar nan ta koya maki sinqin fistara ba to zan kwashe maki ƴar buhun uba kawai".
Abdoul da ya gaji da tsayuwan jin surutun kakar tasu sai ta juya zai fice, amarya tace "yanzu Abdu renine har haka dan ni ba uwarka saratu ba ina faɗama gaskiya shine ka iza farantin goshinka a gaba zaka fice? To da mai ma ya kawo ka sashe na gulman me kazo yi? To in ban haifeka ba ai na haifi ubanka Muhammadu don haka ina zaka da sassafen nan ka faɗamun ko na kwashe maka sauran albarka".
Qaramin tsaki Abdoul yaja jin fitinan stohuwar nan, ni na kawo kaina ai dole ki isheni da surutu.
Kwantar da murya yayi yace "Amarya ta aike Umma ta sani bawan Allahn da mijin Ameera ya buge ne zanje mu haɗu dashi zai koma garinsu.
Salati Amarya tayi tace "Abdu ɗan albarka zaka aikin lada shine dan tsabar sinqin baqin hali ba za ka ce na raka ka ba, to Allah shiryeka kuma ka tabbatar ka kawomun shi na sa masa albarka, kai ina tsaya dai na ɗauko mayafi mu tafi tare tunda motar da kuɗin yarona ka saya to sai na hau" ta qarisa faɗa tana miqewa ta nufi ɗaki.
Abdoul na ganin ta shige ya fice a sashen da sauri, motorn sa ya shige yai mata key da gudu ya fice a gidan sanin halin kakar tasa.
Hayra haɗa kwanuka tayi ta gyara dinning ɗin, duk abinda suke tana ganinsu dariya ne kawai take dannewa dan tasan tabbas yau akwai qaramin bori a gidan nan. Tana cikin tunanin haka Amarya ta fito a ɗaki sanye da hijab nata har da sanja kaya tayi tana faɗin "Angon kayi haquri na jima mu tafi yanzu.." bata qarisa ba ganin palour wayam ba Abdoul ba labarin sa da sauri tayi hanyan waje tana faɗin "ɗan albarka ai nace kayi haquri shine dan ka gaji da jira na sai kayi waje salon kaban wahala".
Gama duba haraban gidan tayi amma ba Abdu ba motorn Abdu, Amarya ta cika tayi fam sai ta rasa me ma za tayi ɗaya? Sashen iyayen sa ta nufa gadan gadan ko sallama ba tayi ba ta tura qofa ta shiga tana bambami..
Amjad suna staye da malam liman sai qira ya shigo wayansa, ganin layin Abdoul ne sai ya ɗauka. Magana suka yi yayi masa kwatancen gidan malam liman kaman yanda limamin ya faɗa masa, da suka gama magana sai ya kashe wayan.
Malam liman yace "yaro yanzu dai tafiyan zaka yi, to Allah ya tabbatar da alkhaeryh ya kuma kai ka gida lafiya ba na shiga gida ina fitowa kamun dai shi mai ɗaukan naka ya iso". Amjad yace "to Allah gafarta malam a fito lafiya".