← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 61

Sashe 28

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

--------
Washe gari da sassafe bayan idar da Sallahn asuba sama-sama ya karya ya kama hanyan shiga jeji.
Shine bai isa inda zashi ba san da gari yagama haske, har fa inda baya isa duk yau ya isa a jejin yasha yawo yasha yawo, amma kwata-kwata bai ga halaman wannan bishiya da yake nema a jejin ba, tun safe har yamma. Ganin lokaci na qure wa ba lallai ya samu ba sai kawai ya karya kan dokin sa dan ya juya ya dawo gida, ganin ko yace ya kwana ko ya qara gaba wahala zai sha, sai dai in ya koma gida gobe in Allah ya yarda ya kuma tafi wata gefen in ta kama ko garin ya bari indai zai samo wannan maganin.
Har ya juyo da dokin sa ya kama hanya dan ya komo gida kar dare yayi, kaman daga sama aka jefo mutumin sai kawai ganin sa yayi a gaban sa, ko kaɗan bai razana ba dan inda sabo ya saba da zuwan da wannan stoho yake masa ako da yaushe, bai storata ba sai ma hamdala da yayi dan dama ya kwaɗaitu da ya haɗu da stohon ko Allah zai sa ya taimaka masa da wani abun. Har zai sauqa a dokin nasa dan gaida stohon, wannan stohon ya dakatar dashi ta hanyar cewa "a'a yaro na ba sai ka sauqo ba" gaisar da stohon yayi.
Da murmushi a fuskansa ya amsa gaisuwan, yarona nayi nisa ne shiyasa baka ganni da wuri ba amma naji zuwan ka, shidai har ransa yana mamakin abunda stohon kecewa wataran kaman ya tambaye sa amma bakin sa sai ya masa nauyi.
Bude baki Amjad yayi da niyan zai faɗa wa stohon yacce ake ciki komai da komai, sai kuma stohon ya tari numfashin sa Yace "karka damu ko kaɗan yarona nasan komai yacce ake ciki, Inshà Allahu za'a yi Auren ku nan da wata huɗu sannan mahaifiyar ta zata samu sauqi sai dai akwai abinda zai faru wanda bana iya hangowa kuma bana ganewa sai dai nace maka ka dage da addu'a da kuma neman stari, Allah na tare da kai Inshà Allahu komai ya kusa zuwa qarshe, sannan ka kusa daina ganina, randa zamu yi haɗuwan qarshe a ranan zan sanar dakai haɗina da kai da komi, ina maka fatan nasara a rayuwan ka, ka riqe Umman ka da Abban ka da kyau, ko da kasamu wasu masu mastayin su nan gaba, wannan iyayen naka sune alkhaeryhn ka su suka maida ka mutum a lokacin da kake gaf da barin duniya.
Sannan ganyen da kake nema da iccen suna makarin ciwon jikinta insha Allahu, Allah qara maka baiwa da basira.
Amma sai dai akwai ɗan mastala ɗaya, mastalan shine ba zaka same su anan ba. Nayi qoqari tun kan kazo da maganan maganin ace na samo maka ko na aika an kawo maka, Amma bazai yuwu ba dole zaka shiga waccan qasan da nace maka NIGERIA, a garin Bauchi akwai wani jeji YANKARI a wannan jejin ne Inshà Allahu zaka samo duka maganin har kayo guzurin wasu.
Jinjina kai yayi yace "Nagode sosai baba nagode Allah saka da alkhaery. In ka samu tafiya Allah stare hanya Allah kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah yasa adace, suka yi sallama ya kamo hanyan dawowa gida abun da ba tare da ya ko waiwaya ba.
Shine bai isa gida ba sai bayan sallahn isha'i.
Ya zuwa direct wanka ya shiga yayi, ya ɗaura alwala anan gida yayi sallolin da wanda bai yi ba.
Rasa yanza zai yi ya faɗa wa Umman sa wannan magana yayi suna hira yana jinsu yayi shiru yana tunani, ya rasa ta ina zai fara yana storon kar Umman nasa ta hana sa.
Abba ne ya kalle sa yace "Jarumin Umma andace kuwa? Sosa qeya yayi Tom Alhamdulillahi dai kawai Abba, Umma na kallon sa tace "akwai Magana abakin ka na sani, menene ya faru Angon Gimbiya? Ganin Umman tasa ta ramfo sa qarshe dai ba yacce ya iya haka ya faɗa masu gashi-gashi sai dai bai basu labarin wannan stohon ba kuma bai ce masu shi ya faɗa masa ba, ɓoye masu yayi yace "wani bawan Allah ne maharbi kuma shima mai bada magani ya faɗa masa hakan" ya faɗa yana kallon Abban sa dan yasan tabbas yayi qasa da kai Umma zata gane ya ɓoye wani abun ko in ya kalleta zata gane.
Ba tare da Abba ya damu ba yace "Allah yasa hakan ne alkhaeri Allah sa kayi tafiyan a Sa'a Allah yasa adace" Umma ta amsa da Ameen, Sannan dan Allah inaso ka kula sosai Jarumin Umma kaga baka taɓa zuwa wannan qasan ba ka kula sosai, yanzu in ka tafi ta yaya zanke jinka?
Murmushi yayi ya sauqe boyayyen ajiyan zuciya dan bai tsammani Umman tasa zata amince da wuri haka ba, ya ɗau sai sunsha wahalan bata baki da fahimtar da ita shi da Abba, cewa yayi "Umma ai bazan daɗe ba Inshà Allahu bazan wuce sati ba" Tom Allah ya yarda jarumin Umma Allah baka Sa'a.
Duka suka yi Ameen
Yanzu yaushe ne tafiyan naka? Inshà Allahu Umma ta gobe ko jibi dai, Tom Allah nuna mana.
Ɗakin sa suka raka sa Umma tai masa addu'a da ahuta gajiya suka ja masa qofa suka yi nasu ɗakin.
Umma na shiga ɗakin ta zauna bakin gado tayi tagumi, Abba da ke bayan ta Murmushi yayi dan yasan tabbas za'a yi haka, ko shi yaji mamakin amincewar ta lokaci ɗaya amma yasan hakan baya rasa nasaba da tausayin Gimbiya da take ji.
Abba Zuwa yayi kusa da ita a bakin gadon ya zauna, jawo ta yayi ya haɗata da jikin sa yana bubbuga bayan ta alaman rarrashi "haba MARYAMA ta sarauniyar mata uwar Muhammadu matar Ibrahim, so kike kisa ɗan naki yayi qasa a guiwa? Kefa kikace ɗan ki jarumi ne ko kinason ki zama raunin jarumtar sa ke da kanki? Girgiza kai Umma tayi hawaye nabin idanuwan ta! Abban yaro na bazaka gane ba ko kaɗan ya nake jin wannan yaron namu a rai na, kullum addu'a ta ɗaya Allah yasa na mutu kamun ace yau ba yarona kusa dani, qaunar da nake wa yaron nan kusan kullum cikin zullumi nake inya fita zai dawo yace yasan gaskiya, kullum cikin mafarkin an rabani dashi nake, kullum cikin addu'a nake kamun wannan rana Allah ya ɗauki rai na! Kuka ta fashe dashi Abban yaro na inason yayi tafiyan nan dan tabbas inajin tausayin wannan mata da kuma yarinyar da marabin ta da Maraya mara uwa kaɗan ne. Abban yaro na kasani haka kawai zuciyata bata kwanta da tafiyar nan ba kuma inaji a jiki na kaman wani abun zai faru ko kuwa sanadin rabuwana da Amjad kenan, kuma kasan bszan iya ɗaukan haka ba daga randa akace an rabani da Amjad daga ranan nayi bankwana da farinciki har mutuwa na wataqila ma sanadin mutuwa na kenan!
Ajiyan zuciya Abba ya sauqe! Tabbas acikin magana Maryam ba qarya ko ɗaya ko kowa bazaiyi shaidan son da take wa Amjad ba shi zai yi shaida tun daga randa ta ɗaga idon ta ta ɗaura akan yaron nata tabbas yasan qauna ce na ɗa da uwa Allah ya sanya tsakanin su dan Amjad ma sonda yake wa Umman sa ako ina baya ɓoyewa.
Abba yace "MARYAMA ta inaso ki ɗago ki kalle ni, ɗagowa Umma tayi fuskan ta duk hawaye!
Abba yace ki kalli idona Maryam, kallon Abba tayi, Abba yace mata "Maryam wa ya baki Amjad? Umma tana sheshsheqa tace "Allah" Abba ya qara cewa "wa zai ɗauki ranki ko na Amjad ya rabaku? Umma ya qara cewa "Allah".
Jinjina kai Abba yayi yace Alhamdulillahi, Maryam nasan ke musulma ce kuma kin yarda da Allah sannan akwai samu akwai rashi akwai mutuwa akwai rayuwa, kuma duk kinsan mai qaddara wannan abubuwa Tom dan Allah kar maganan mu yayi nisa, kar Amjad yaji wani magana yasa kokonto a ransa ko kinason hakan ya faru? Da sauri Umma ta girgiza kai tace a'a. Tom Masha Allah inaso akoda yaushe kidinga binsa da addu'a, Allah ya ga son da kike masa kuma yaga sonda shima yake maki, Allah ne ya baki shi Inshà Allahu ba mai rabamu da Amjad sai mutuwa. Kici gaba da sa masa albarka kinji. Umma ta ɗaga kai, da qyar da qyar Abba ya lallashe Umma har suka yi alwala suka yi nafila, tilon ɗan nasu suka wa addu'an kariya da Sa'a sannan suka qara da godiya ga Allah da suka idar suka kwanta anan Abba yaci gaba da lallaɓa matan sa lallaɓa irin na masoyan gaske wanda soyayyan su bata stufa....
A ɓangaren Amjad kuwa shima a haka ya kusan raba dare ya juya haka da qyar dai ɓarawon bacci ya sace shi.
Chapter 28 · 0% Book details