Sashe 30
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qiran farko na asuba, Umma ta farka a ɗan razane har jikin ta na sassafo da zufa, salati tayi tana dafe qirji! Wannan salatin da tayin shi yayi nasaran tada Abba a bacci. Miqewa Abba yayi ya laluɓi hasken ɗakin ya kunna, kallon ta yayi yace "Lafiya kuwa maryama? Ko dai kinyi mugun mafarki ne? Umma ta kasa cewa qala sai kawai jingina da tayi da kan gadon ta rufe ido tana mai da numfashi! Miqewa Abba yayi ya fice yaje dan ya tashi Amjad amma ya samu har ya tashi, magana Abba ya masa "kayi alwala mu tafi masallaci ko" amjad dake miqa a kan madedecin gadon sa yace "Tom Abba na, yau fa ina Umma ta Bata zo tashi na ba" ya faɗa yana miqewa. Umman ka na can tana fama da rigima ta kusa yin jika bata san ta girma ba har yanzu. Dariya Amjad ya sanya! Yanzu dai Abba wannan abu da kake faɗa cin fuska ne, uwattawa ce ke rigima? Ɓata fuska Amjad yayi! Daga kafaɗa Abba yayi ya fice a ɗakin yana "da kai da Umman taka duk Allah ya taroku" ɗakin su ya wuce. Cikin lallami Abba ya fara magana "Mero ta kina son saka ɗan naki cikin damuwa ko? Kinga ganin ni naje tashin sa ba ke ba har yana tambayan ko baki da lafiya ne, in dai bakyason zuwan ɗan naki can qasar shikkenan ki faɗa masa nasan shi kuma in dai bakyso bazai je ba. Amma inason ki sani Alqawari ya ɗauka masu sannan kuma kece kika fara yarje masa maganan wannan gasa dan girman Allah da Manzon sa Maryam ki lallashi zuciyanki" ganin da alama har ran Abba ya fara ɓaci sai Umma ta sauqo a gadon faɗawa jikin Abba tayi, Abban jarumin Umma kayafeni amma kayi haquri wallahi Nima banson saka damuwa a rai na abunne ya kasa bari na, Mafarki nayi fa akan yaro na. Umma ta buɗe baki da niyan labarta wa Abba mafarkin sai Abba ya ɗaura yastan sa akan bakin ta yace "shiiiii, ya isa ba sai kin faɗa mun ba yanzu sallah zaki yi, ki sanar da Ubangijinki sannan kiyi wa ɗan ki addu'an nasara da ta kariya, kuma kada ki manta wani lokacin akwai sharrin shaiɗan, da yawa mafarki kan zama gaskiya amma wani mafarkin sharrin shaiɗan ne. Wani lokacin mukan kwanta a tunanin abu a ranmu Tom ba shakka wannan abun ya damemu har a mafarkin mu ya zo mana. Akwai kissar wani bawan Allah da yaje wajan Sheikh Ibrahim inyass(RA) yace masa "ance in kana yawai ta salatin Manzon Allah SAW Tom tabbas zaka gansa, me yasa kullum ina yi amma ban taɓa kallon sa ba? Sai Sheikh Ibrahim inyass yace masa "Annabi kake so ka kalla? Wannan bawan Allah yace "eh" Sheikh Ibrahim inyass yace masa "Tom yau in zaka kwanta inaso kaci abinci kawai kar kasha ruwa, ka kwanta haka ko mai ka gani a mafarkin ka kazo kaban labari. Wannan bawan Allah ya tashi ya tafi da yaje gidan sa dare yayi ya ci tuwo bai sha ruwa ba ya kwanta, washe gari asuban fari yaje wajan Sheikh Ibrahim inyass (RA). Sheikh Ibrahim inyass ya ce masa "bawan Allah labarta mun abun da ka gani a mafarkin naka. Bawan Allah yace "malam nayi yacce kace amma da na kwanta mai makon naga Annabi sai kuma nayi mafarkin inata shan ruwa kawai har dai na farka, murmusawa Sheikh Ibrahim inyass yayi yace masa "Tom in zaka kwanta da qauna da kuma begen son ganin Annabi SAW kaman yacce kaman ka kwanta da qishin ruwan nan Tom tabbas in kana qishin ganin Annabi wataran Manzon Allah SAW zai baka ruwan kashe qishin qaunan ganinsa". Tom inaso ki sani tabbas akwai mafarkin da suke gaskiya kaman labarin dake cikin (MAFARKI NAH littafin Uwar Batoorl) da kuma ( A MAFARKI NA littafin A'isha Mika'il) akwai kuma waɗan da suke ba gaskiya ba. Dogon ajiyan zuciya Umma ta sauqe tana mai jin nistuwa ya shige ta sosai, hamdala tayi ga Allah sannan ta ce "kar Jarumin Umma ya jira ka sosai Abban sa a samu a tafi masallaci" kallon ta Abba yayi yana murmushi yayi hanyan fita a ɗakin yana cewa "inma ya gaji jira ya zai yi ba uwar sa ce ke mun rigima ba ta tsayar dani, mutum har ya kusa yin jika ya girmi yin rigima amma yaqi dai nawa, dole ma na hana Amjad maki takwara dan rigiman masu suna Maryam in ya haɗamun ku har biyu zaku qarisa ni, ya qarasa faɗa ya bar ɗakin dan yin alwala ganin an kusa shiga salla. Murmushi kawai Umma tayi, tabi bayan mijin nata dan ita ma tayi alwalan ta samu jam'i. Fitowan Umma Abba kaɗai ta gani ya fara alwala, wucewa ɗakin Amjad tayi dan tasan halin sa sarai zai iya komawa ya kwanta. Tana shiga ɗakin nasa ta hango sa kan sallaya yana addu'a, tsayawa tayi har ya shafa kamun tace "kar dai jarumin nan yace mum har yayi Sallah? Tashuwa yayi yana murmusawa a'a fa Umma ta nafila nayi kamun Abba ya fito mu wuce. Umma ta buɗe baki zata yi magana Abba da ke tsakiyan gida yace "jarumin Umma ka fito mu tafi kar mu rasa jam'i. Bayan fitan su alwala Umma tayi dai-dai ana shiga sallah a masallaci, jam'i ta tasamu ta bi da aka idar lazumin ta tayi da addu'oeen ta kamun ta shafa, tashuwa tayi ta shiga aikin gida dan tasan in ɗan nata ya dawo ya samu tana yi zai ce zai taya ta. Umma tayi sharan ta da wanke-wanke san da ta ɗaura abincin karyawa kamun ta shiga ta gyara wa ɗan nata ɗaki ta sanya masa turaren wuta mai daɗin gaske. Cikin qanqani lokaci gidan gaba ɗaya yayi staff baka jin komai dai qamshin turaren wutan da tasa a ɗakin ta da kuma ɗakin yaron nata, sai kuma qamshin ruwan shayin da take dafawa. San da gari yayi haske tarr kamun Abba da Amjad suka dawo gida, sun shigo gidan lokacin Umma na banɗaki tana wanka. Abba ɗaki yayi, shima Amjad ɗakin sa ya wuce direct ya kwanta dan mai da baccin da bai yi ishashshe jiya ba. yana kwanciya ya rufe idon sa da zummar yin bacci, kyakkyawar fuskan Gimbiya da wannan murmushin ta mai mantar dashi ko sunan sa ke masa gizo, buɗe ido yayi ya kuma kullewa ita ɗin yake qara gani, laɓɓan ta da yafi ɗaukan hankalinsa da kuma kalan qwayan idon ta su suka hana sa sukuni, duk ya juya haka ya juya haka amma yana rufe ido ita ɗin yake gani tana masa gizo. Tashuwa yayi ya zauna a stakiyan gadon nass magana yake shi ɗaya "wannan kwailar yarinyan mai take nufi dani ne? Guntun tsaki ya ja! Fasa baccin yayi ya tashi ya fita a ɗakin. Umma da ke qoqarin shigowa ɗakin nasa da qiran sa ya karya tukun yayi bacci, ya kusa yin karo da ita, ja baya Umma tayi tana kallon sa tace "lafiya kake surutu kai kaɗai har ka kusa ya da ni? ina son nazo na ganki ne Umma ta. kallon sa Umma tayi da murmushi tace "kadai faɗa gaskiya ko Gimbiyar zuciyar taka kake tunani? Ɗago kan sa yayi da zumman kallon Umman tasa da mamakin ya aka yi ta gane abun da yake tunani, ganin yan da idon Ummansa ya kumbura sannan yayi ja kaman mai ciwon ido san da yaji gaban sa ya faɗi! Umma ganin ɗan nata ya zuba mata ido, nan take ta tuno da yacce idon ta ya kumbura tai saurin juyawa dan kar ya fahimci wani abu ya sawa kansa damuwa, sanin halin ɗan nata. Jarumin Umma biyo ni ka karya sai ka koma baccin ko kaje wajan Gimbiyar taka in kuma yau zaka tafi tom. Bin bayan Umman tasa yayi yana qara nazarin yacce ya kalli idon Ummansa mai ya same ta? Mai ya hana ta zuwa tada shi da asuba kaman ko yaushe? Zama yayi a gefen Abban sa a kan tabarman ta yacce zai ke kallon Umman tasa da kyau. Kunun tsamiyan da ya gani a kofi ya ɗeba ya fara sha, kallon sa Abba yayi yace "yau kuma kunu za'a sha kenan rogimammen Umman sa" Umma ta murmusa ta ce "a qyale mun yaro komai ma yake so in dai akwai tom yasha, Jarumin Umman sa sha abunka dama wa kai nai wa kunun. "Ummata tafiyan nawa ne har ya sanya idonki kumbura da ja haka? tambayan da Amjad ya jefowa Umman sa wanda bata yi tsammanin ji ba, Abba da ke shan ruwa zafi ajiye kofin yayi a take ya kalli Umma ya kalli Amjad, kamun Umma tayi magana Abba yayi saurin cewa "jarumin Ummansa idon Ummanka ke ciwo". "Abba ciwon ido dai? tun yaushe haka? Abba ka kalli idon Ummata fa yacce ya kumbura yayi ja kaman wanda yayi kuka, Abba akwai dai abun da Ummata ke ɓoyemun ko kuke ɓoyemun duka, ko dai Umma bata son tafiyan ne na haqura? Ya faɗa fuskan sa na nuna da gasken yake zai haqura. Umma tace "jarumin Umma idona kawai ke ciwo, ka karya ma kasamu kaje ka gano surkar ta in ya so sai kayi shirin tafiya. Shiru Amjad yayi bai ce komi ba, ba don ya yarda idon Umman tasa ke ciwo ba kawai yasan dai wani abu ne suka ɓoye masa, ya san Umman sa duk in yace zai yi tafiya na kwana biyu in dai ba jeji ba Tom hankalinta baya kwanciya har sai ya dawo, ya rasa mai yasa haka? Kuma bare wannan karon da zai je qasa ne wanda bai sani ba bai taɓa zuwa ba, iyayen nasa ma basu taɓa zuwa ba yasan dole bazai wuce hakan bane ya tada mata hankali! Ajiyan zuciya ya sauqe ya aje kofin dake hannun sa. "Umma ta Allah baki lafiya" ya faɗa yana miqewa. Kallon sa Abba yayi yace sai kuma ina Jarumin Umman sa? Abba bacci nake ji, yau baza'a raka Abba kasuwa ba kenan? Miqa Amjad yayi yace "Abba zan biyo ka in na tashi baccin, Umma tace "jeka abunka kayi baccin ka ɗan albarka Jarumin Umman sa. Murmushi yayi yace "tom Umma ta, Abba Allah kai ka lafiya sai nazo" Abba