← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 61

Sashe 38

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameerah suna isa gida a gajiye ta shiga wanka tana fitowa ta faɗa gado sai baccin gajiya, ganin bacci ya ɗauke ta murmushi yayi yace "mutum sai rigima an girma ba'a san an girma ba wai abaroki asibiti bayan zaman da kika yi ashe kina jin bacci wiffey case" ya shige bathroom shima ya wasta ruwa yazo ya kwanta gefen ta bacci yai gaba dashi.

Fitowa tayi daga toilet en ɗaure da wani babypink towel, gaban dressing mirror ta wuce direct mai ta shafa kawai tayi gefen da ma'ajiyan kayakin ta suke, riga da skirt na less ta jawo ta sanya amma skirt en yaqi shigan ta, kallon kayan tayi tace "abu baka fi 1 month da saya ba har ka masteni ya Rabb wani irin hips ne dani kaya su ta mawa mutum kaɗan" guntun tsaki taja tai jefi dashi ta jawo wani gown ta sanya ta rufe fuskanta as usual ta fito jakadiya ta samu tsaye a qofan tana jiran fitowan ta "Barka da fitowa uwar ɗaki na mai dogon zamani" hannu Gimbiya ta ɗaga is okay kije ciki in kin gyara akwai wani kawa a qasa ki bawa mai so okay.
Tana gama magana tayi gaba dan zuwa sashen mahaifiyar ta.

Umman Amjad da Abban sa kewan yaronsu suke sosai ba ɗan kaɗan ba Umma har da ɗan ramewanta
Suna zaune akayi sallama, jin anfara shigowa gidan sai Abba yace a qariso.
Ahmad abokin Amjad ne ya shigo sannu da zuwa Umma ta masa ya durqusa har qasa ya gaida Abba da Umma duk suka amsa da fara'a, Umma Amjad yana nan ne?
Abba yace "Amjad dai? Baku haɗu bane kan ya tafi ko bakasan zai yi tafiya ba?
Abba ban sani ba gaskiya jeji ya shiga ne ko Doha?
Murmushi Umma tayi yarona Ahmad wani jeji qasan gaba ɗaya ya bari fa baka da labari kenan ya tafi wani qasa acan wai Nigeria aka ce mata nake ga.
Buɗe baki kawai Ahmad yayi amma dai ba muyi hiran zai yi tafiya ba har na barin qasa ko da yake ma bamu cika haɗuwa ba, yanzu dai Umma a taimaka mun da layin sa da kuke waya.
"Amadu Ni da Umman taku duka wayan jagwal ne sai a hankali kawai" Abba ya faɗa yana murmushi,. Tom Abba amma mai yaje yi?
Umma tace "wannan yaron nawa sai a hankali wani irin abota kuke haka ni mairo wai bai faɗa maka abinda ya faru bane?"
Umma bai faɗamun wani abu ba gaskiya kinsan sa da rashin son magana bare dogon hira, taɓa baki Umma tayi to Allah ya shiryamun shi, Nan ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta faɗa masa.
Kama taɓa Ahmad yayi ya gyara zama "wato dai ranan abun da ya kaisa gidan sarki kenan shine bai faɗamun ba shine har da kishi kar na rakasa" abinda ya gama faɗa a zuciyan sa kenan kamun yace "to Umma Allah sanya alkhaeryh Allah basa Sa'a ya dawo dashi lafiya, dama zan koma ne inshà Allahu zan dawo nima in lokacin bikin yayi"
Ameen ya Rabbi yarona kaima Allah kaika lafiya Allah nuna mana lokacin da rai da lafiya
Miqewa yayi yace "Abba Umma sai wani lokacin" ya faɗa yana yin hanyan fita, da addu'an Allah kiyaye hanya Umma da Abba suka bishi har ya fice.
Umma ta juyo ta kalli Abba murmushi tayi tace "wannan yaro naka Allah ya shirya sa wai dan ma abokin sa ne".

Sai bayan magrib Ameerah suka koma asibitin
Sun same sa a kan darduma, jikin sa da sauqi
likitan ne ya shigo yace "Insha Allah gobe zai sallamesu in yaso su qarisa jinyan qafan a gida ko nan da sati 1 zuwa 2 ne kamun ya warke sosai dan qafan ne kawai yanzu damuwa amma b abinda yake damun sa"
Godiya Daddyn Little yai wa abokin nasa yace "Allah kai mu goben frnd".
Da Ameen likitan ya amsa kamun ya fice a ɗakin
Gaisawa suka yi duka da mara lafiyan suka masa ya jiki ya amsa da sauqi.
Har aka yi sallan isha'i suna can, sai da lokacin ya ɗan tafi ganin dare nayi suka masa sallama
Suka kamo hanyan gida.

Sai da suka yi sallan isha'i kowa ya taɓa hutu kamun suka tafi sashen kawun nasu wanda suke qira da baba qarami suka gaidashi da matan sa suka dawo kowa ya wuce dan ya kwanta don gajiyan bai tafi ba.
Soja ne yake ta laluɓa wayan sa amma shiru babu wayan ba labarin waya, fitowa yayi yaje ya duba har cikin motor nan ma babu waya, abun da ya faru ɗazu a hanya ne ya faɗo masa a rai tabbas ba ko kokonto yarinyar nan ce ta ɗau wayan nan.
Juyawa yayi ya koma ciki ransa a ɓace yayi hanyan ɗakin da yake na su Maha, da ya Abdoul ya haɗu yana zaune a palourn Kakus yana danna waya
Ganin Soja sai ya Abdoul ya tsayar dashi yace "our able army sai ina haka? Ya Abdoul ɗakin su Mahreen zan karɓo wayana
Ya Abdoul yace okay plss a turomun Mahreen ɗin tazo ina dinning area
Tom ya Abdoul.
Sallama yayi a qofan dakin nasu, Mahreen ce ta amsa ya Habeeby ka shigo
Shiga yayi ya bata saqon qiran da ya Abdoul ke mata, himar ta jawo ta saka ta wuce dan amsa kiran da ake mata.
Bayan fitan ta in da Mahreen ke kwance tayi ɗaɗɗaya ya nufa, yana zuwa wajan ba jinkiri kawai ya jawo ta qasa ji kake timmmmm!
Kaman a mafarki ta ji an buga ta da qasa ihu ta saka 'Wayyo Mutum ko Aljan na shigesu za'a karya"

Cewa yayi "qanin ubanki ne zaki tashi ne ko sai nayi ball dake? wai ke ina wasa dake ne kam da har zaki ɗauki wayana? Kin tashi kin ban wayana ne ko sai na harbe ki idiot kawai
Jin muryan sa kuma tasan halin sa tashuwa tayi a hankali tana hawaye dan tabbas ta bugu
Ɗauko wayan tayi ta basa tana Allah ya isa kuma sai Allah ya saka mun.
Sarai yaji me tace amma sai ya basar heɗe ransa yayi yace "ke me kika ce?
Tura baki tayi ni ba abinda nace
Qwafa yayi ya duba wayan yaga chajin shi bai ko sauqa ba alaman bata yi komi dashi ba kawai neman magana ne, tsaki yaja "Ni na rasa mai yasa bansa security a wayan nan ba" da ya gama seta mata zama yai hanyan waje dan ya koma ɗakin sa.
Bayahn fitowan Mahreen wajan zama ya abdoul ya nuna mata ya mata umurni da ta zauna dan samun su tattauna
Bayani yake ta koro mata daki-daki na yacce yai kewansu sun jima basu zo Bauchi ba
Sai da ya tabbatar ta sake dashi suna hiran kamun ya numfasa a yanayi na muhimmin magana ya dube ta yace "qanwata ki aramun duka hankalinki anan zamu yi magana mai muhimmanci kinji"
kallon sa tayi da murmushi tace "yayana in da qarin hankalin ma duka na ara maka ina sauraranka"
Nan ya kwashe duk abinda ke xuciyan sa abinda yake ji game da ita tun da ya ganta ya faɗa mata(hausawa suka ce abari ya huce shi ke kawo rabon wani).
Qanwa ta ina sonki so kuma na gaske son Aure wanda in son samu ne ayi bikin nan cikin wata 1 kai yamun nisa ma irin dai week hakan nan
Tun da ya Abdoul ya fara jawabi tayi qasa da kanta ta ɓoye fuska a hijab da ya kai aya ya buqaci da ta ɗago ta basa amsa taqi ganin ya masta ko takan wayan ta dake hannun sa bata bi ba tayi hanyan ɗaki har da ɗan gudun ta
Dede tana shigowa ɗakin shi kuma Soja zai fice a ɗakin kenan suka kusa yin karo
Ransa a ɓace amma ganin Mahreen tsayawa yayi ya dara yace "yarinya ta kamu kenan taga handsome yayana*
Wucewa tayi tana rufe fuska bata ce komi ba.

Duk abunda ke faruwa kuwa Hajiya kakus ta fito ɗaukan abun gurza goronta data bari a palourn sai ta tarar da draman da ake yi
Ganin duka jikokin nata na son junansu abun ba qaramin daɗi ya mata ba( a tunanin ta Soja ma hira yaje) haka taje ta kwanta da farinciki.
Ya Abdoul ganin ta gudu sai abun ya burge sa ya kuma qara masa qaunan ta "tabbas inason mace mai kunya" abun da ya faɗa ya miqe yana murmushi
Soja yace "yayana Allah kaimu musha biki"
Ya Abdoul da farinciki Yace "Ameeñ our able army"
Dariya soja ya kuma yi ya wuce wajan baccinsa, shima ya Abdoul fice wa yayi ya nufi nasa wajan baccin a sashin su, wanda yake dama da soja ne amma yace a sashen kakus zai kwana.
Ya Abdoul ko da ya koma ɗakin sa haka ya kwanta yana ta juye-juye shi dai har ga Allah yake son qanwar tasa kuma bai qi a ɗaura masu aure ko yanzu ba.
(haba malam abdu daga uhmn sai ehem ko a hand kake ne?
Kunga inko a hand yake ya hwaɗan nice ourmman batoolerh mai wuqa da nama sai nasa a aura masa ita yanzu)
ko ba haka ba FAN'S ?

Mahreen na shiga ɗaki ta samu Maha na sharar kwalla sai tace "menene ya sameki ko wani abun ya habeeby ya maki?
Maha kaman zata rufe addan nata da duka tace "Idon matambayi ne ya sameni, ba habeeby ba habibu mutum sai son jin gulma"
Kallonta Mahreen tayi tai murmushi ita dai tana farinciki bata da time na surutu da Maha
"Allah shiryaki" shine abinda tace tayi kwanciyan ta tana ta murmushi ita dai tana ji kaman ta jita a jikin yayan nata.
Mutumiyar kuwa Allah ya isa take jawa soja yafi cikin girgi.

Autan Umma yana komawa ɗaki kwanciya kawai yayi ko ta kan wayan bai bi ba ransa fess ya fara maganin renin yarinyar nan.....

Masha Allah jama'a sahiyar alkhaery

Mu dai mun riga mun tashi👯 sai kuma inda qarfi ya qare✍️

Muje zuwa
Masoyan 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀
𝘿𝘼𝙂𝘼 𝙏𝘼𝙎𝙆𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙌𝘼𝙇𝘼𝙈𝙄𝙉
👇
𝙃𝘼𝙍𝙄𝙍𝘼𝙏𝙐𝙒𝘼 𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙏𝙊𝙊𝙍𝙇

💋💋 امى بتولة💋
Chapter 38 · 0% Book details