← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 61

Sashe 41

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mahreen ta fito wanka da mamaki taga har Maha ta gyaran ɗakin kuma tsaff har qamshi yake
Taɓe baki tayi dama haka kike kekam kaman me aljanu
Batace ma Maha uffan ba ta wuce dan ta shirya ta fita ta gaida kakus
Maha ma toilet en ta shiga sanda ta wankesa tass sannan tayi wanka itama ta fito
Kusan a tare suka gama shirya wa
Tabarakhallah Masha Allah kyau suka yi sosai kaman masu zuwa gasan kyau
Abaya suka sa ita Mahreen ta saka peach ita kuma Maha ta saka maroon gashi dukansu farare
Kar kuso kuga kyan da suka yi kyau har yana ɗiga.
Fita suka yi a ɗakin sun samu hayra itama ta gama shirya komi har tayo wanka abunta, dukan su suka yi ɗakin Kakus dan gaishe ta
sallama suka yi ta amsa tana ɗaurin ɗankwali
juyowa tayi tana kallonsu tana murmushi Masha Allah kaga larabawan jikoki na Allah dai ya rayamun ku ya maku albarka
Gaisawa suka yi duka tana qara sa musu albarka
Hayra ce ta shigo tace "Amarya kizo mu karya"
danqwalon hayra tayi dan fatarin kakarki amma ba niba uwaki ce Amarya ba ni ba dan jakan ubanki dama tare dani kike karyawa ko neman magana
Maha da bata iya yin shiru tace "ke dai stohuwar nan ba'a maki gwaninta ko kaɗan"
Takwara ke kuma ki fita a idona kamun na taso banson aikin masu tangaɗi da sanyin safiyar nan bazaki sani sinqin surutu kaman mai layiii ba
Ita dai Mahreen murmusawa take, tashuwa suka yi suka fice duka suka bar kakus dake qoqarin fitowa itama
Bayan duk sun fito sun zauna a dinning ɗin
Maha ce ta kalli hayra tace "yanzu yaya hayra dan jaraban tsohuwan nan itama a dinning take cin abinci mutum na tafiya kaman me tete"
Dariya suka sa duka na rabaki da surutun safe na kakus Maha, kinga dai ke takwaranta ko tom wallahi ba rage maki zata yi ba jaraban masifan ta na safe yafi na ko yaushe
Maha tace "yo to ni ina ruwana tamun na mata kalass"
Kakus ne ta iso wajan tace "ke hariratu ubanki Muhammadu ne mai jaraban masifa, ke kuma mai sunan aljanu ubanki kika rena dan jakar ubanki, tangaɗaɗɗun yara kawai masu sinqin reni".
ja mata kujera hayra tayi ta zauna
Tace "to ina su sojan mijina?
Kai amma dai yaran nan baku da kirki harda ke indo da nake wa kallon mai hankali cikin carbi, yanzu dan sikitin sinqin rashin mutunci shine har za kusa abinci a gaba baku nemo ƴan uwanku ba sufa sune maza suke nemowa ku ba abinda kuka iya sai ci bari kuji tom inga ɗan kwal uban dazai ci abinci anan su soja basu zoba ingwada masa nawa tagaɗin yafi nasa"
Maha ce ke qunquni, yauwa kin fara ai kenan da wannan zagin da bansan a ina kika koyo saba
Kallonta kakus en tayi, juyar dakai tayi nide ba inda zani atou
Hayra ce ta tashi taje sashensu ta qira ya Abdoul ta kuma dawowa ta qira ya habeeby
Ta samu ya Abdoul ya gama shiryawa fitowa yayi yayo dinning ɗin, shima ya soja dinning en yayo
Zaunawa ya Abdoul yayi a setin Mahreen wacce tunda yazo wajan ta sauqe kanta qasa dan dai yanzu kuma take jin kunyan sa
Saving nasu Mahreen da kanta ta tashi tayi ta sawa kowa nasa
Da tazo kan na ya Abdoul rasa mai zata sa masa tayi shi dai ya soja yana gani sai smilling yake kawai dan burgesa suke
A haka dai tasa masa ferfesun kayan ciki da tosted-bread da soyayyen qwai a gefe da kuma ruwan zafi
Kallon gaban Abdoul kakus tayi ta kalli gabanta daga soyayyan kwai da bread se ruwan shayi
Ajiye cokalin hannun ta tayi ta saka Salati
Sai duk suka ɗago suna kallonta shi dai soja ya fahimci nufin ta tun da ya kalli kallon da take wa plate ɗin gaban ya Abdoul dan haka mai zai yi inba dariya ba harda kama ciki
Itako Maha duk da kyawun da taga ya mata yana dariya hakan bai hana ta aika masa da harara ba tace a ranta "kaga Soja mugu bai san me akayi wa salatin ba yakama dariya dan baqin hali da nema mana surutu"
Kakus ce tace "oh Ni Mairama daso yanzu ke indo dan ɗiban albarka da kuma rashin storon Allah sunan ki kaman na mayun daa Kiga abunda kika sawa abdu kiga abunda kika samun nida gidan yarana da kuɗin yarana fa aka sayi komi amma dae Allah ya kyauta don haka ban isa ba bazaki samun bushashshen biredi kaman kunnen zomo ba da wannan abu kaman wainar kashin shanu sannan ki cikawa Abdu kwano ba tun da bana uwarsa ba
Nima samun ferfesun atou
Mai zasu yi a wajan in ba dariya ba dukan su kowa ta basa dariya dan duk sun ɗauka wani abun ne ya faru ganin irin salatin da ta rafka
Ya abdoul ne yace "haba amaryata kishi kike dani tom juyo muci tare"
Ɗan qwal uba banson yaudara kayi kaɗan nayi kishi da kai Ni dai tunda ba uwarka ce ta saya ba yaronane ɗan albarka ya sayo to maza azubamun banson tangaɗanci
Hayra ce dan ta kashe surutun ta tashi ta sawa kakus kaman na abdoul en har da chip's da suke ci suma
Ai kuwa tana loma ɗaya da ferfesun ta kurma ihu ta tufar
Yanzu dai ke ja'irar ƴar nan kasheni zaki yi wato ki huta wannan barkonon kike aikaman nasa a ƴan hanji na da nake maleji dasu to ta Allah ba taki ba
Ai nasan wannan yar albarkan sona take shiyasa bata saka mun ba
Maha ce ta turo baki ke dai takwara kin cika surutu abincin ma bazaki barmu muci a nuste ba dan Allah
Bafa kyau surutu anacin abinci so kike muci tare da sheɗan halan
Subhanallahi cubulle bakinki ya sari ɗanyen kashi Allah tsaremu haɗa hanya da sheɗan
A'uzubillah bismillahi
Yo kunga na koresa ai ba naci abinci na nayi shiru Allah zubo maki albarka cubulle.
Shi dai ya Abdoul duk abun da ake bayama jin su gaba ɗaya idonsa na kan Mahreen
Ita kuwa sai sunne kai take
Kakus ce tace "jarababben kallo dai ba kyau sai ya sanya mutum tangaɗi gwanda a nistu aci abinci yafi lada ko ƴar mutane ta sarara" ta faɗa tana hararan ya Abdoul
Murmushi yayi bai ce komi ba sanin sarai dashi take
Wayan Mahreen ne yayi qara alaman saqo ya shigo taga ya habeeby ta gani ya turo mata text
*qanwata ki barmun yaya haka ya karya mana karki zautasa da yawa kinji stohuwa ta fara banbami kar takai mana mazga*
Ɗagowa tayi suka haɗa ido da ya soja en dariya ya mata sai ta harare sa a wasa ta tura baki ta kau da kai da kallon kowa tana karyawanta ita ma
Sannan ya Abdoul ya ɗan nistu yana cin abinda ta zuba masa cikin nistuwa
Bayahn sun kammala kowa yayi hamdala
Main palourn suka koma dukan su
Hayra ce da Mahreen suka tattare wajan, bayan sun kai kitchen suka haɗa wanke wanken suna yi
Mahreen ta fita tabar hayra a kitchen ɗin zata ɗaura sanwa.

Gimbiya Mehwish itace bata koma cikin gidan ba sai yamma liss
Direct ɗakinta ta wuce tana shiga tai jefi da abun fuskan ta takwanta a gadonta tana faɗin "washhh Ammaa ta na gaji da tunanin ba nayi bacci yanzu kam before magrib....

𝘽𝘼𝙔𝘼𝙉 𝙎𝘼𝙏𝙄 𝙂𝙐𝘿𝘼 1

Rayuwa nata tafiya yayin da bawan Allahn da Daddyn Little ya buge satin sa ɗaya 1 ciff da sallama yau da ya kama Lahadi qafa kuma Alhmdlh sai dai ɗan abunda baza'a rasa ba
Ameerah da Daddyn Little sun gwada tambayan sa da mamakinsu kuma ya amsa masu tambayan
"Yace masu shi bauchi yake son zuwa" sai dai apart from haka bai faɗa musu komi ba dangane dashj sun haqura tun da ya yarda zai zauna har satin ya cika
A ɗan satin da yayi a gidan sosai suka shaqu da Ameerah in da take ta roqonsa karya tafi ya zauna dasu inyayi sai suje Bauchin tare suma akwai family house nasu a can
In ta faɗi haka baya cewa komi sai dai yayi murmushi kawai
Shi dai shirinsa yake zai tafi dan a lissafin sa bai wuce wata 2 bane yanzu ya ragemasa
Gashi be isaba bare yace ya samo abun da yazo nema.
Chapter 41 · 0% Book details