← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 61

Sashe 10

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

^^^^A ɓangaren ita Gimbiya Mehwish. Har ta koma gida ranta a matuqar bace yake, sakamakon daman taɓa mata jiki da Yarima Fu'ad ya samu. Ta so ace faɗan ba na gasa bane da tabbas in bai mutu ba se ya rasa hannayen sa dan seta cire masa su.
Amma duk da haka ranta wasa! "ba wanda ya isa ya haye wannan gasan da na sanya ko ba su ba na sani" faɗin Gimbiyar.
( Ni ko uwar batoorl nace za dai ki sani amma baki sani ba kam dan nice nan oum batoolerh nasani, ni keda wuqa da nama)
^^^ Wasta ruwa ta yi. ta gabatar da sallahn ta, shiryawa tayi cikin dogon riga maroon tai rolling da milk veil har ta rufe fuskan ta kaman ko yaushe idanuwan ta ne kawai a waje, haka kawai ta ji ta sanya alkyabba. Black alkyabba ta ɗauko a closet ɗin ta, turawa tayi tai hanyan wajen ɗakin nata dan zuwa sashen da mahaifiyarta take, ta dubo ta. Tana fitowa kuyangun ta suka durqusa suna mata sannu, hanu ta ɗaga masu. Ganin tana tafiya ya sanya sauran ta shuwa suna ɗaga mata bayan alkyabban nata! Direct hanyan sashen Sarauniya suka yi dan sun san bata wuce wajan ko kuwa garden(lambu).
Suna zuwa dai dai qofan part en Sarauniya suka ja suka staya. "𝙏𝙖𝙠𝙖𝙬𝙖𝙣 𝙠𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙐𝙬𝙖𝙧 𝙜𝙞𝙟𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙢𝙪, 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙖𝙣𝙞𝙮𝙖, 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖𝙧𝙚 𝙜𝙖𝙗𝙖𝙣𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣𝙠𝙞 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙗𝙖'𝙖𝙙𝙖𝙡𝙞𝙮𝙖, 𝙖𝙨𝙝𝙞𝙜𝙖 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙖 𝙛𝙞𝙩𝙤 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖, 𝙮𝙖𝙧 𝙎𝙖𝙧𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙎𝙖𝙧𝙖𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖,𝙜𝙖𝙗𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙗𝙖𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙯𝙪𝙘𝙞𝙮𝙖, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙝𝙖𝙡𝙞, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙣𝙪𝙛𝙞, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙢𝙪'𝙖𝙢𝙖𝙡𝙖, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙖𝙙𝙖𝙡𝙘𝙞, 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙣𝙢𝙩𝙖, 𝙢𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖, 𝙛𝙖𝙧𝙖𝙧 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙝𝙖 𝙠𝙖𝙡𝙡𝙤," qirarin da amintattun bayin da ke gadin part en suke ma Gimbiya tun kan isowanta. Ɗaga masu hanu tayi, shigewa tayi bayan sun buɗe mata qaton qofan da kaman ba'a cikin gida yake ba. Tana shigewa suka rufe qofan yayin da kuyangun kuwa suka juya, dan ba'a basu daman tsayawa a qofan ba.
Da sallama Gimbiya ta shiga ɗakin da mahaifiyar nata take ciki, "Assalamu'alaikum" jin shiru ba'a amsa ba yasa yanayin ta ya sauya dan sanin da tawa Ammaahn ta ma'abociyar amsa sallama ce in dai bakin ta nada daman furta kalma. Qara sawa bakin gadon da Ammaah ɗin ta ke kwance tayi, a yacce ta ga yanayin jikin mahaifiyar nata, shi ya qara sa mata damuwa, dan ta so bata labarin abinda ya faru tunda bata samu zuwa ba. Zauna wa tayi a gefen Ammaahn nata, tana mata addu'aoe tana tofa mata har bacci ya ɗauke ta..

Bayan juya wan kuyangun, suna isa shashin Gimbiya ɗayar su ce tace laure kinga kyawun da Gimbiya tayi kuwa da ta sanya Alkyabba? Ni ko na gani hinde ai wallahi da Gimbiya ta san kyawun da Alkyabba ke mata da da dena yawo babu shi. Tabarakhalla Masha Allah, billahillzi laure in nayi aure na haihu sai na wa Gimbiya ta kwara ko zata samu ko da kaɗan a kyawun Gimbiya ne kuma Allah yasa kan lokacin an samu wanda ya buɗe mata fuska dan ko kallo ɗaya na masa da ido na zan kafta hoto na ajiye a zuciyata in nayi ciki nata tariyowa ina kallo. Dariya laure ta saka amma hinde ke dai Allah yaye maki da surutu kinga ma ba na tashi nayi aiki na kan ace gulman Gimbiya muke kin san jakadiya yan zu ta shigo ta sa mana ido. Carab tana rufe baki wata kuyanga ta shigo( wacce farkon labarinmu ta bamu labarin Gimbiya a taqaice) kayan jikinta ba irin nasu bane, "laure wai kukam me yake damun ku ne? Meyasa kuka maida gustiri stome aikin yin ku ne?" faɗin wacce ta shigon. Wacce aka qira da lauren mae zuba ɗazun tashuwa tayi tana jakadiya a yafe mu amma dama aiki zamu tashi yi yanzun. Juya wa kuyangar da laure ta qira da jakadiya tayi ta nufi ɗakin Gimbiya. "Hmmn hinde Wallahi wannan yarinya dan tana ganin itace jakadiya tana wa mutane abinda ranta ke so". "A'a laure gyara batun ki, dan dai uwar ta bata lafiya, ta zauna a matsayin uwarta, kamun ta warke take mana rawar kai. Ai uwar tata zata warke zamu koma dai dai maga qarshen rawan kan nata" faɗin hinde. Kema dai kya faɗa, ace wai da ita kaɗai aka yarda bayan uwarta, kin ga fa har sashen Sarauniya naga ranan ta fito abinda ko masu gadin ba shiga suke ba. Hinde tace "Ke dai qyale ta maga qarshen rawan kai".
Bayan wannan kuyangar ta shige ɗakin Gimbiya gyare-gyaren ɗakin tayi ta haɗa kayakin da za'a wanke ta share ta goge ko ina tass-tass har bathroom nata, ta kunna buner ta kunna wa ɗakin turaren wuta ta, ta fito da kayan wankin ta ja qofan ɗakin ta rufe.

^^^ Sai can Sarki ya shigo ɗakin, sallaman sa ne ya farkar da Gimbiya daga baccin da takeyi. Amsawa tayi tana "Barka da shigowa papa" amsa mata yayi yana mata sannu da gajiya. Murmusawa tayi "Papa ba wani gajiya fa". ai ɗiyata jaruma ce nasan ba lallai ta gaji ba dama. "Ya jikin Ammaahn taki"? "Papa ga Ammaah kam sai dai muce Alhmamdulillah" ta faɗa idon ta na kawo qwalla. Kallon ta mai martaba yayi yace "ba'a san jaruma da kuka ba Ebnateeyh, kiyiwa mahaifiyar ki addu'a shine sonki a gare ta ko bayan ranta balle da kuma ran ta, oya karki bari hawaye ya ɓaga stadadden fuskan ɗiyar kirkin mu ƴar albarka, ƴar Papa da Ammaah". Maida hawayen tayi ta murmusa kaɗan! Insha Allahu Papa zanke mata addu'a Allah tashi kafaɗunta ya yaye mata wannan ciwo. "Ameen ya Hayyum ya Qayyum, ko kefa ƴar albarka" faɗin mai martaba.
Bayan ya zauna gefen matar tasa. Kallon Gimbiya yayi yace "Ebnateeyh meyasa wai kika sanya wan nan buɗe abun fuskan naki a mazaunin zaɓan mijinki? Sannan ba tare da shawarin mu ba. Ko dai auren ne ba kyaso? Ba kya ganin ke kaɗai Allah ya bamu! Kina da labarin mace bata mulki kuwa? In ba kiyi auren ba ya zakiyi da mulkin? Ko dai ki kinaso mulkin a ɗaura wanine, bayan kinsan banda kowa nawa! Ni ni kaɗai haka na tsinci kai na kaman ke, ko na ce gwanda ke. Tun da ni ko mahaifiya ta baxan ce ga yacce take ba, banma san tana raye ko bata raye ba har. Ki ma kanki faɗa Mehwish, yin auren ki shi ne farin cikin mu ni da Ammaahn ki."
Kanta aqasa tana sauraron mahaifin nata, duk jikinta yayi sanyi da maganganun sa. Magana mai martaba ya qara mata "Ina jinki me yasa kika ce hakan ne a mazaunin zaɓan mijin aure ki?"
"Kayi haquri Papa" haka kawai tace kanta na a qasa har yanzu bata ɗago ba.
Can nisa tace "Papa ban sa gasan dan wani abu ba. farin cikin ku kai da Ammaah ta shine nawa. Na sanya gasan ne kawai dan na tabbatar، da jarumi zan aura, kuma tsayayye wanda ba wai nice zan tare masa komai ba, shima zai taremun a matsayin sa na wanda ke sama da ni. Wanda in ma ta kama ya mulki masarautan nan, nasan ba iya qarfin mulki ba har da cancanta na qarfin jiki da na zuciya yana dashi, wanda kuma zai yi adalci da qarfin sa ba zalunci ba, wanda zai mulki masarauta cikin amana da zaman lafiya kaman yacce Papa na yake yi. Amma in abinda nayi ya ɓata maka rai Allah ya huci xuciyan ka Papa, Allah baka haquri insha Allahu bazan sake wannan kuskure ba."
Ajiyan zuciya mai martaba ya sauqe! "Naji dalilan ki amma duk da haka baki kyauta ba kuma bakiyi dai dai ba, sai dai ba komai Ebnateeyh Allah maki albarka ya zaɓa maki miji nagari."
Ta amsa da Ameen, cikin ranta tana hamdala, dan tasan halin mahaifin nata sarai......

ƳAR SARKI CE

Daga alqalamin✍️

𝙐𝙬𝙖𝙧 𝘽𝙖𝙩𝙤𝙤𝙧𝙡 🔥

*******
* kai daga fara chan charas chas chas sai kace hasti duka matan dake wajan sun taso abun su chasssss..........
Muje zuwa my people
Ku nishaɗantu, ku faɗakantu, ku wa'azantu, sannan ku dara. daga alqalamin uwar batoorl takuuuuuuu ako da yaushe
Fatan alheri agare ku masoya alqalamin uwar batoorl a ko ina kuke a faɗin duniyar nan....

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮𝙪𝙠𝙖:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞,

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙐𝙬𝙖𝙧 𝙗𝙖𝙩𝙤𝙤𝙧𝙡 🔥

💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl✍🔥)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

𝙒𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞 𝙦𝙞𝙧𝙦𝙞𝙧𝙖𝙧𝙧𝙚 𝙣𝙚, 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙖𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙜𝙖𝙧𝙚 𝙣𝙖𝙨𝙖 𝙖𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙙𝙖𝙧𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙛𝙪𝙨𝙠𝙖𝙣 𝙖𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙩𝙖𝙪𝙨𝙖𝙮𝙞, 𝙨𝙖𝙞 𝙙𝙖𝙞 𝙗𝙖𝙗𝙗𝙖𝙣 𝙖𝙗𝙪 𝙢𝙖𝙛𝙞 𝙧𝙞𝙣𝙟𝙖𝙮𝙚 𝙨𝙝𝙞𝙣𝙚 𝙛𝙖𝙙𝙖𝙠𝙖𝙧𝙬𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙠𝙚 𝙦𝙪𝙣𝙨𝙝𝙚 𝙖 𝙘𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙙𝙖𝙧𝙖𝙨𝙞 𝙣𝙖 𝙧𝙖𝙮𝙪𝙬𝙖.
𝙄𝙣𝙖 𝙛𝙖𝙩𝙖𝙣 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙦𝙖𝙧𝙪 𝙙𝙖 𝙙𝙖𝙧𝙪𝙨𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙠𝙚 𝙦𝙪𝙣𝙨𝙝𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣𝙨𝙖. 𝙎𝙖nn𝙖𝙣 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙗𝙖𝙢𝙪 𝙙𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙖𝙢𝙛𝙖𝙣𝙪𝙬𝙖 𝙙𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙖𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙖𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙠𝙤𝙮𝙖 𝙖𝙘𝙞𝙠𝙞.
𝘼𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙠𝙚 𝙗𝙖 𝙙𝙖𝙞 𝙙𝙖𝙞 𝙗𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖𝙛𝙚𝙢𝙪 𝙖 𝙠𝙖𝙣𝙨𝙖.

𝙎𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙧 𝙬𝙖 𝙜𝙖𝙧𝙚𝙠𝙪 𝙢𝙖𝙨𝙤𝙮𝙖 𝙩𝙖𝙧𝙚 𝙙𝙖 𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙘𝙞𝙣 𝙢𝙚𝙢𝙗𝙚𝙧𝙨 𝙣𝙖 𝙇𝘼𝙁𝘼𝙕𝙄 𝙜𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙢𝙘𝙞.

***
yau take rana ta qarshe ga masu gasa a masarauta!
Yau take sojan umma zai dawo!
Yau take Ameera uwar little zata taho Kaduna garin gwamna itama tabar kakus da sinkin sikitin tijaranta!

Muje zuwa cikin littafin namu mesuna 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
Dan jin ya abubuwan zasu kasance, wa zai lashe gasa?
Waye soja?
Sannan Ameera na komawa?
Muje labari kai tsaye masu karatu!!
***
_____________________________________________________________

🅿️ 25&26

💋💋 امى بتولة💋
Chapter 10 · 0% Book details