Sashe 32
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Umma na qoqarin hura wuta a kitchen ta jiyo sallama, amsawa Umma tayi ta fito tana waye ne? Ahmad na sunne kai yayi ya stugunna yace "Umma an wuni lafiya. Umma ta ce "lafiya Alhamdulillahi bawan Allah. Gaisawa suka yi Umma dai bata gane sa ba, bayani Ahmad ya mata, kamun Umma ta gane sa, wai wai wai Ahmad kana nan shiru-shiru ka manta da mutane kaman baka nan?
Umman ina nan sai a hankali ne da yake bana qasan gaba ɗaya, Umma tace "gashi abokin naka ya fita yanzu wai zashi zance da rana staka baku haɗu a hanya ba? Ahmad yace "Umma mun haɗu, ni nace zan qaraso na gaidaki" ayya Allah ya maka albarka ya gida ya su maman naku? Suna lafiya Umma suna gaida ku. Masha Allah haka akeso, ruwa Umma ta kawo masa ya sha ya mata sallama zai tafi.
Umma tace "yaro na har zaka tafi ba zaka tsaya muci abincin rana ba kan abokin naka ya dawo? Murmushi Ahmad yayi yace "Umma zan dawo anjuma da dare Inshà Allahu" Tom Tom ba komai Allah kaimu anjuman Allah maku albarka, "Ameen Umma" ya miqe ya mata sai anjuma ya fita, yana kan tunanin irin kallon da Amjad ya masa ɗazu ya rasa mai kallon yake nufi dan baisan abun da yace ba in banda maganan Gimbiya da yayi.
Daga kafaɗa yayi shima yace ohon maka in tayi tsami zanji..
Barka da jumaah masoya ayi haquri da wannan, happy friday garekuu daga uwar batoolerh takuu Ako da yaushe ✍️
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa suka sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙏𝙊𝙊𝙍𝙇 🔥✍
💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 37&38
💋💋 امى بتولة💋
Ahmad tada motorn sa yayi yaja ya tafi.
Umma ayyukan ta taci gaba da yi bayan ta kammala ta kwanta dan huta gajiya kamun mijin nata da yaron nata su dawo.
-----
Taxi da Amjad ya hau a iya inda baqin abun hawa ke tsaya wa in sun shigo cikin Masarautan anan aka stayar da shi.
sallaman mai taxi ɗin yayi, ya kama hanyan shiga cikin Masarautan a qafa.
motoci ke shigowa haraban Masarautan, da alama wani babba ne yazo.
Acikin jerin motocin ne wani ruwan toka qiran Benz ya tsaya dai-dai gefen Amjad, dogarin da ke jan Motorn ne ya fito yana cewa
"Barka da shugowa ranka ya daɗe, ka iso mu qarasa" ya faɗa yana buɗewa Amjad qofa, ba musu ya shige motorn ya zauna.
Gimbiya yagani zaune a motorn, abun ya basa mamaki daga ina take da safen nan? Tun kallon da ya mata na farko ya kau da kai bai kuma kallonta ba.
hakan da yayi ya matuqar ɓatawa Gimbiya rai dan taji daɗin ganin sa amma taso ya fara mata magana.
kau da kai tayi tana tura baki, amma takan juyo ta saci kallon sa. Amjad tun da ya juya ko mosta kansa bai sake yi ba, yasan kallon sa take dan yana jin yawon idon ta a jikin sa.
Har bakin qofan shiga ainafin cikin gidan motorn ya kaisu, shi ya fara buɗe qofan ya fita kamun Gimbiyar ta fito.
Dogarawan na kwasan gaisuwa, hanu kawai Gimbiya ta ɗaga tayi gaba hadimominta suka bi bayanta.
Ɗaga kafaɗa Amjad yayi irin i don't care ennan ya ɗauki hanyan da zai sadashi da babban palourn baqi.
Tasan da yana jiranta amma sanda ta watsa ruwa ta kuma shiryawa cikin kayan da zamu iya qiransa na shan iska ta yafa alkyabban ta tayi hanyan palourn da tasan bazai wuce yana can ba.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, amsawa yayi bai ko ɗago ba.
Waje ta samu ta zauna tana tura baki ganin har yanzu yaqi mata magana, daurewa tayi ta buɗe baki tace "malam in baka da abun cewa nayi gaba ni inada abun yi" ta faɗa tana juyar da kai gefe alaman dai da gaske take.
Murmushin iyaka leɓe yayi yace "Allah kiyaye hanya kya iya yin gaba".
Hararan sa tayi kawai batace uffan ba.
"Daga ina kike?"
Kaman daga sama taji anjefo mata tambayan kallon sa tayi, hankalin sa na kan Apple da yake tauna a hankali kaman ba shi yayi tambayan ba.
"Mai kike kallo nayi tambaya baki ban amsata ba? Ya faɗa yana kallon ta da idanuwan sa masu sanyata nistuwan dole, qarfin hali tayi tace
"Ai naga kaman ba dani kake maganan bane shiyasa" qara waro idonsa a kanta yayi, sai ta kau da kanta tace
"Daga ɗaki na nake" kallonta yayi ya girgiza kai kawai baice komi ba yaci gaba da taunan Apple nasa.
Ta rasa meyasa amma bata iya ɗauke idonta a kansa,
"Baiwar Allah kurwata tafi qarfinki irin wannan kallo haka" ya faɗa yana miqewa jin ana qiran sallah.
Basarwa tayi ta miqe itama tace "inka dawo masallaci ina garden" ta faɗa ta fice a palourn da kunyan kamata da yayi tana kallon sa.
Murmushi yayi yana binta da kallo har ta ɓacewa ganin sa kamun ya fice shima ya nufi masallaci.
Sashen ta tawuce ta kuma gyara kwalliyan ta taɗau wayanta a bedside drawer ta fito, jakadiya dake qoqarin shigowa ɗakin nata suka kusa cin karo, kaucewa jakadiyan tayi tana fadin "amun afuwa ranki ya daɗe ban kula bane" hanu ta ɗaga mata tace "a gyara mun shumfiɗa inada baqo sannan akai kayan marmari" ta faɗa ta wuce.
Juyawa jakadiya tayi dan aiwatar da aikin da uwargijiyan nata ta umurce ta dashi.
Yana fitowa masallaci hanyan da zai sada shi da lambun ya nufa.
Zaune ya tarar da ita tana danna waya, sallama ya mata sannan ya zauna, kallon sa tayi ta amsa Sallaman fuskanta ɗauke da murmushi.
Gyaran murya yayi kamun yace "nazo muyi sallama ne may be sai ranar Aure ki ganni" ɗago kai tayi tana wara idanuwan ta, "tafiya zuwa ina haka?" Ta faɗa cike da son samun amsa.
Zanje wani qasa ne amma ba mai nisa sosai ba, though ban taɓa zuwa ba bare nasan iya nisan nasa, akan batun maganin Ummanki and ba lallai na dawo yanxu ba so you should take care.
Ba zato ba tsammani yaji mutum a jikin sa, saurin janye jikinsa yayi a nata yana kallonta.
"Allah tsare hanya ya kaika lafiya Allah ya bada Sa'a Allah yasa a dace" ta faɗa tana share hawayen dake bin kuncin ta!!
Da "Ameen" ya amsa yana miqewa, i have alot to do so saqon gaisuwa zuwa ga mai martaba da kuma Ummanki sai Allah yayi dawowa na kuma.
Ganin tanason masa yarinta sai kawai ya wuce bai ko tsaya sauraran mai zata ce ba.
Miqewa tayi jiki a sanyaye ta nufi part na mahaifiyar ta.
Daganan kasuwa ya nufa wajan Abba, suka gama tsara komai na tafiyan nasa wanda zai yi gobe insha Allah, sune basu dawo gida ba sai magrib.
Da sallama duka abakin su suka shigo gidan Umma suka tarda tana sallah, buta Amjad ya kawo wa Abban sa shima ya ɗau nasa suka yi alwala, Abba yaja su jam'i suka gabatar da sallahn magrib. Sun idar bada jimawa ba isha'i ya shiga suka kuma miqewa tare da Umma suka gabatar.
Bayan sun idar da sallolin nasu Umma ta qara masu sannu sannan ta gabatar masu da tuwon daren nasu, tare suka ci kaman ko yaushe har suka kammala ta tattara komai ta kai kitchen.
Abba ne yace "tunda kana da tafiyan sassafe gobe in Allah ya yarda ga kamata duk muje ku kwanta dan kar ka makara, ko Amjad" maganan da Abba yayi sanda ya sanya wa Umma faɗuwan gaba amma ta daure! Murmushin qarfin hali tayi tace "gaskiya ya kamata kam Jarumin Umma ka samu ka dawo da wuri insha Allahu, Allah dai ya bada Sa'a Allah sa a dace.
Da "Ameen" duk suka amsa suka miqe dan kowa ya wuce makwancin sa, abinda ya damu Amjad bayan shigansa ɗaki ɗaya ne ganin yau iyayen nasa basu masa yacce suka saba ba amma sai yabar hakan akan kewansa da zai damesu yayi alwala yai addu'an ya kwanta dan samun yayi sammako.
Abba na shiga ɗakin ya kalli umma kawai y girgiza kai ya wuce ya ɗauro alwala ya kwanta. Tashuwa umm tayi daga tagumin da ta zuba taje ta ɗauro alwala ta tada sallah.
Sanda ta raba dare tana sallah kamun ta stagaita ta daga hannu sama tana hawaye tana addu'a, sai dai abinda tafe furta wa ne ya cika ni da mamaki....