← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 61

Sashe 29

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Gimbiya bata san mai yasa ba amma har cikin ranta tana cike da kewan ganin sa yau gaba ɗaya baizo ba, kuma mai martaba yace mata zai ke zuwa.
Sai dai abu ɗaya da ke kwantar mata da hankali shine ta yarda da cewan Insha Allahu zai cika alqawarin da ya ɗauka, kusan yau wuni tayi masa addu'an dacewa da Sa'an samowa mahaifiyar tata magani.
Bayan ta idar da Sallahn isha'i a ɗakin mahaifiyar ta, tana kan darduma kaman ance ta juya, sai hanun Amman nata ta gani yana motsi kaman tana son ɗaga hannun.
Da saurin gaske tayi wajan gadon, Bayan kusan sati gashi yau Ammaan nata halaman sauqin dai ya qara nuna wa jikin zai lafa, dan dama takan yi sati bata ko mosti, in jikin ya lafa kuma tashuwa ne da kuma cin abu bata iya wa amma zata yi magana har ta ɗan jingina da kanta, sai dai komai sai anmata duk da haka
Ta sameta ta buɗe ido amma bata iya magana, sai mosta bakin ta take alaman tana son yin magana amma ta kasa, Gimbiya tace "Ammaa Sannu" gyaɗa kai kawai tayi da murmushi a fuskan ta, sai kuma ta mai da idon ta ta rufe.
Ko ba komai taji daɗin farkawan mahaifiyar tata gashi har ta mata wannan murmushin nata da ke yaye mata damuwan xuciyan ta, "Allah baki lafiya mai ɗorewa Ammaah ta" shine abinda ta furta tana mai zama gefen maman nata tana ɗan daddana mata jikin ta kaman massage.
Har Mai martaba ya shigo ya samesu a haka, ganin ɗiyar tasa cikin farin ciki ya sanar dashi me ke faruwa ko bai tambaya ba, tabbas shima yana jin tausayin tilon ƴar tasu dan kwata-kwata batadan daɗin uwa ba, a maimakon uwa tayi hidima da ita, ita take hidima da uwar tata tunda tayi wayo.

Mai martaba yace "Ibnateey me aka bata? Tace "Papa ba komai fa. Masha Allah, Allah ya bata lafiya mai ɗorewa Alfarman Rasulullahi SAW. Da Ameen ta amsa
Zama yayi a gefen gadon ita kuwa Gimbiya ta sauqa qasa, mai martaba yace mata "ya kuka yi da Muhammadun? Nan Gimbiya ta kwashe yacce suka yi duka ta faɗa masa har da alqawarin da yace ya ɗauka, kuma Papa inaji a jikina Inshà Allahu za'a dace, Allah dai ya temaka. Mai martaba yace "Ameen ya Allah, Allah ya sa a dacen.
Nan ya qara da ce mata "in dai abun da ta faɗa da gasken shi take nema kan ga Auri mutum tom tabbas wannan ne mijin da take nufi akoda yaushe dan wannan ya haɗa fun yacce take so ma, Allah ya tabbatar maki da alkhaeri Ibnateeyh, da "Ameen, ta amsa tana tuno maganan su da jakadiya.

Mai martaba ne ya sauqe ajiyan zuciya yace "Amma akwai abun da yake damuna". Gimbiya ta kalli Papan nata cikin damuwa tace "menene Papa?
Murmusawa yayi ba komi karki damu kanki Ibnateeyh kai na ke ɗaure wa kawai, tabbas yana mun akwai mai irin fuskan sa da na sani amma abun da jimawa na kasa tunawa.
Ayya Papa ai dama haka ne yawanci ance ko wanne ɗan adam da masu kama dashi guda bakwai 7 a duniya, Tom may be shiyasa kake ganin hakan.
Haka dai hiran nata ita da mahaifin nata har dare yayi, ta tashi ta wa mahaifin nata sai da safe, ta wuce dan tafiya sashen ta tasamu ta kwanta.

Sai dai muce safiyar alkhairi jama'a.........

𝘾𝙝𝙖𝙠𝙬𝙖𝙠𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙁𝙞𝙡𝙢..
𝙆𝙪𝙣𝙖 𝙜𝙖𝙣𝙞𝙣 𝙩𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞𝙣 𝘼𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙙𝙖 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙩𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖 𝙘𝙚 𝙠𝙤 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙖𝙗𝙪 𝙙𝙖𝙗𝙖𝙣?
𝙏𝙖𝙪𝙨𝙖𝙮𝙞𝙣 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖𝙖 𝙙𝙖 𝘼𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙟𝙞 𝙯𝙖𝙞 𝙞𝙮𝙖 𝙟𝙪𝙮𝙚𝙬𝙖 𝙯𝙪𝙬𝙖 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖 𝙠𝙪𝙬𝙖?
𝙒𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙩𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙯𝙖'𝙖 𝙮𝙞 𝙨𝙝𝙞 𝙠𝙪𝙬𝙖?
𝙒𝙖𝙣𝙚𝙣𝙚 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙨𝙩𝙤𝙝𝙤𝙣?
𝙉𝙖𝙨𝙖𝙣 𝙩𝙖𝙢𝙗𝙖𝙮𝙤𝙮𝙞𝙣 𝙢𝙪 𝙙𝙖 𝙖𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙪𝙘𝙞𝙮𝙖𝙧𝙢𝙪 𝙯𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙨𝙖𝙦𝙖 𝙢𝙖𝙣𝙖 𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙬𝙖....

ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️

Nace ba jama'a muje zuwa, labari fa yanzu aka fara ✍️

💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa suka sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi!!!

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

💦💦💦💦💦💦💦💦

𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

_______________________________________________________________

🅿️ 35&36

💋💋 امى بتولة💋

WASHE GARI..
Chapter 29 · 0% Book details