Sashe 31
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yace "kace dai sai na dawo dan baka yi alaman biyo ni kasuwa ba yau, Amjad dariya yayi bai ce komai ba ya wuce ɗakin sa. Yana shiga ɗakin nasa ya kwanta, a take bacci ya ɗauke sa. Amjad na barin wajan Abba ya juyo ya kalli Umma, Maryam Kinga ko, kema kinsan irin qaunan tsakaninki da ɗan kin nan ko bai ga idon ki ba tsaff kaman mai Aljanun Umman sa zai san mai ke faruwa, kidinga koyan haquri da ɓoye wani abun kinji meron ibro maman amadu. Umma dariya ta sanya, yanzu dai ka ɓata sunan kowa ban da na yarona, sunan sa Muhammad ba amadu ba. Tashuwa Abba yayi yana dariya ya shiga bayi dan wasta ruwa ya shirya zuwa kasuwa, Umma kuwa tashuwa tayi ta kama gyaran inda suka karya ta haɗa kwanukan wanke wanken ta kamun ɗan nata ya tashi ya gani yace zai yi. Abba shiryawa yayi cikin manyan kaya ya kafa hulan sa, har bakin qoga Umma ta raka sa tana masa adawo lafiya. Bayan tafiyan Abba Umma ta kammala komai nata, ta gyra gidan ta qara yin wanka, ganin har qarfe sha ɗaya 11am yayi kuma ta leqa Amjad haryanzu bai tashi ba, Hijab ta sanya ta fita a gidan. Amjad wajajan qarfe sha ɗaya da rabi ya tashi 11:30am, mafarkin da yayi ya tuna shi ya sanya shi jan guntun tsaki, magana yake a zuciyansa "ni dai wannan qwailar yarinya bata kai ta sanya ni wanka ba" fita yayi a ɗakin yana qiran sunan Umman sa, jin ya qira shiru bata amsa ba kuma bai ji qaran ruwa a bayi ba. ɗakin ta ya leqa ko tana ciki nan ma bata ciki, haqura yayi da neman ta ya ɗiba ruwa ya shiga wanka. Sai da ya yi kusan minti talatin a bayin kamun ya fito, shiga ɗaki yayi dan ya shirya sai ya jiyo sallaman Umman sa, fasa shiga ɗakin yayi ta tsaya. Amsa Sallaman yayi yace "sannu da dawowa Umma" yauwá jarumin Umma sannu da tashi kai ma. Umma ashe kin fita na tashi inata nemanki ban ganki ba, Umma murmushi tayi tace "jinjirin Umman sa makwabta naje yin barkatu anyi haihuwa naga kana baccinka mai daɗi shiyasa ban tada kai ba, sannun ka da tashi ko. "Tom Ummata ya faɗa" yana shigewa ɗakin nasa dan ya shirya. Bayan ya gama shirin sa fitowa yayi sanye da qananun kaya, Umma na ganin sa bakin ta yaqi rufuwa "jarumin Umma irin wannan kyau haka, a lallai surkata zata ga wanka yaushe rabon da kasa qananan kaya? Maha Allah yaron Abba ko a kasuwan maqiya wannan kyawun dole a yabe sa bare a na masoya. Sosa qeya Amjad yayi yana murmushi dan shi kanshi yasan tabbas yayi kyau, kyau enma irin sai idonka ya gane makan nan, Amjad yace "Umma sai na dawo, washe baki Umma tayi tace "a gaidamun surka ta dan nasan wannan wankan ba dai kasuwa ba sai dai masarauta. Allah tsaremun kai ya dawo da kai lafiya jarumin Ummansa. Ummata surkanki zata ji gaisuwa, ya faɗa yana dariya ya fice a gidan. bayan sa Umma tabi da kallo sai kwalla a idon ta! Allah karemun kai ya tsaremun kai a ko ina Amjad. Yana fita qofan gida, wani motor arsh color ya gani yana qoqarin parking a qofar gidan nasu, kallo ɗaya yawa Motorn ya kauda kai ya nufi hanya, horn mai Motorn yayi Amjad bai ko juya ba yaci gaba da tafiyan sa. Muryan da ya ke mararin ji ne ya jiyo sa anacewa "kai ɗan air shugaban marassa mutunci ba kaji ina horn bane" juyowa yayi cikin hanzari mutumin da ya gani ne ya sanya shi cewa "whatttt" mai muryan ne dai da yayi tsammani. Mai Motorn ne ya zo yayi hugging nasa ganin Amjad en yana tsaye ya kasa qarisowa. Amjad yace "Ahmad kai nake gani ko mai kama da kai? Wanda ya qira da Ahmad en ne yayi dariya yace "yes ni kake gani Jaaad. Ashe rai kan ga rai? kwana da yawa ba kai ba labarin ka shiru kawai ka manta da mutane. Sosai qeya Ahmad en yayi da key na motor da yake hanun sa, yanzu dai ina ka nufa? Ba wani waje mai nisa bane nan gidan Sarki zani. Amjad laifi kawa sarki ko me da rana tsakan nan i hope dai ba qasqantar da kanka kayi kana aiki a can ba? Murmushi Amjad yayi yace "long story ne Man but to cut the long story in to short zance zani gidan Sarki. Buɗe baki Ahmad yayi sai kuma ya kwashe da dariya, duk Wannan kyau naka a gidan Sarki kuma ya staya Ina fatan dai ba hadima ba ko ƴar aiki acan? Dafe kai Amjad yayi yace "You see mastalana dakai wallahi son dogon surutu and you know am having headache in long conversation. Yanzu dai Jaaad baka yi missing na ba da kake cewa har zan sa maka ciwon kai, mu shiga na gaida Umma sai in yaso muje gidan Sarkin tare ko giftawan ƳAR SARKI na gani, wani kallo Amjad ya ma Ahmad sanda ya haɗiye sauran maganan bakin sa bai shirya ba. Amjad yace "in zaka shiga ka gaida Umma ka je ka gaida ta ai zata gane ka, zuwa gidan Sarki kuma ina da qafa ban ce ka bini ba, tunda kasan hanya kaje da kanka. Ahmad jan baki yayi yai shiru bai ce komai ba, juyawa yayi zai shiga gidan yana cewa "Man you will never change, Allah taro ka zan je gidan Sarkin da kai na ai nasan hanya in ka dawo da dare zamu haɗu. Bayan Ahmad ya shiga gidan ɗaga kafaɗa Amjad yayi irin "i don't care" ennan yayi gaba abunsa.