← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 61

Sashe 60

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ce tsaye a tsakiyan palourn hannunta riqe da mayafi da kuma jakan ta waya a kare a kunnen ta tana cewa "wai kai Auta ba za ka fito bane sai mun tafi?" Daga ɗaya bangaren soja yace "Umma ina fitowa yanzu tashuwa na bacci ne shiyasa". Umma tace "ko ma baka tashi baccin bane ka fito yanzun nan inba haka ba zan saɓa maka" kitt ta kashe wayan. Ummeyh dake sauqo wa daga step's ce ke cewa "gaskiya ana takurawa yaro na tunda ba binmu zai yi ba abarsa ta huta mana". Umma tace "Gwaggon yara ki qyale wannan yaron naki ko kaɗan baya ji wallahi ni na rasa ma ya zan yi dashi wai dai ace yaro ka fito ka gaida iyayen ka ko ba za ka bisu ba ai ka musu addu'an a dawo lafiya amma kwata-kwata habeeb ba ya ji". Ki sa masa albarka kawai Umman yara. Hmmn! kawai Umma tace tayi shiru. Dai-dai Abba ma ya fito iso palourn shima Soja ya iso, kallonsa Umma tayi ta kau da kai tace "wai ina su doter ne suma ko ba za su mana a dawo lafiyan bane?" Tana gama rufe baki Maha da Mahreen suka shigo palourn su ma. Maha ce ta fara stugunnawa ta gaida iyayen nasu kamun Mahreen ma ya gaishe su, Umma qara kallon soja tayi ganin bai gaishe su ba kuma shi ya fara zuwa palourn, qawafa tayi. Soja gaisar da Abba da Ummeyh yayi kamun ya gaida Umma ko kallon sa ba tayi ba bare yasa ran zata amsa. Ummeyh tace "ataimaka dan Allah da Manzon sa a amsa mana" kamun ta amsa gaisuwan sama-sama. Maha tace "yanzu Abba tafiya za kuyi ku barmu mu kaɗai a gida?" Murmushi Abba yayi yace "doter may be yau ɗin nan zamu dawo in bai samu ba kuma zuwa gobe Inshà Allah ku dai ku kula sosai kunji" Mahreen tace "Inshà Allah Abba Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" duk aka amsa da Ameen. Waje suka nufa duka har parking space suka raka su, Umma da Ummeyh suka shiga baya soja ya shiga mazaunin driver Abba ya zauna a kujeran gefen sa, Soja yaja motor suka fice a gidan. Kaduna state airport suka nufa, ko da suka je Private jet da yake kusan mallakin Abba wanda wajan aiki aka miqa masa dan tafiye-tafiyen sa, shi suka shige jirgin nasu ya ɗaga sai Bauchi shi kuma Soja ya ja Motorn ya juyo gida. Abdoul ya ɗan sha tafiya dan anguwan da ya masa kwatancen musan qarshen gari, ko da ya isa sanda ya qara qiransa ya haɗa sa da malam liman ya masa kwatancen da kansa da qyar har da tambaya kamun ya samu ya gane gidan, yana isa parking yayi a qofan gidan ya ɗau waya ya qira Amjad. Qiran Abdoul ya shigo wayan sa ɗagawa yayi yace "ka iso ba? Dan naji qaran motor". Abdoul yace masa "eh ina qofan gida" Malam liman qira ya kwaɗawa ecleemah. Da tazo yace "ta ɗau jakan Amjad ta kai waje" Amjad yace "Allah gafarta malam tayi hutawan ta zan ɗauka, Qanwata ki koma ciki abunki zan ɗauka". Ecleemah bata saurare sa ba tabi umurnin mahaifin ta jakan ta ɗauka tayi hanyan waje malam liman da Amjad suka rufa mata baya. Qofan back seat Abdoul ya buɗe mata ta saka jakan da ta ɗauko kamun ta juya idonta cike da qwalla tace "yayana Allah tsare hanya ya kaika lafiya" tana gama faɗa ta shige gida bata tsaya ko jin me Amjad zai ce ba. Bin bayanta yayi da kallo har ta shige sau kawai yaji wani irin, maganan malam liman ne ya sanya shi Juyowa da barin kallon qofan shiga gidan. Malam liman yace "yaro kaga kalman da ake cewa baqo raɓa ko gashi a jiya zuwa yau har za muyi kewanka kaman kar ka tafi amma kuwa ba dama sai dai mu bika da addu'an Allah kaika lafiya Allah kuma yasa andace kenan" Da Ameen Amjad ya amsa sai yayi qasa da kansa kawai. Malam liman suka gaisa da Abdoul cikin girmamawa sai yace wa Amjad "bawan Allah ka shiga ku tafi tafiyanka ba na ɓata lokaci ba" ya buɗe baki zai yi magana sai malam liman ya ɗaga hannu yace "karka damu da komi kai dai ka shiga kuje" juyawa yayi ya shiga mazaunin gefen driver Abdoul ya zagaya ya shiga mazaunin driver suka wa malam liman sallama Abdoul yaja motor, malam liman yana ɗaga masu hannu har Motorn nasu ya ɓace a layin nasu gaba ɗaya. Juyawa malam liman yayi ya shige gida cike da kewan baqon nasa na kwana ɗaya wanda kuma yana tunanin qara haɗuwan su wataqil sai kuma a qiyama. gaisawa Abdoul da Amjad suka yi wanda tun da Amjad ya shiga Motorn yake jin gabansa ya tsananta faɗuwa, Abdoul kallon sa yayi sai yace "bros ina muka nufa?" Amjad yace "airport zaka kaini" Abdoul ya kuma kallon da ya kalli hanya yace "haba dai airport ba zaka je gida ka gaida Amarya ba? Am Amaryan ina nufin kakata gaskiya ya kamata kaje ka gaida ta inba dai kayi booking Flight na safe ba". Amjad yace "nop banyi booking Flight ba yanzu dai in munje zanyi sai na jira, Amarya kuma inka koma kace wani jikanta na gaida ta sai wani lokacin zanzo". Murmushi Abdoul yayi ai tunda ba kayi booking jirgi ba gaskiya daganan sai gida ba wani airport da zamu ai in bankaika gida ba yau ba mai kwata na a hannun masifaffiyar stohuwar nan, kwashe yacce suka yi da Amarya yayi ya faɗa wa Amjad yana dariya. Amjad sai da ya Murmusa jin rigiman stohuwar sai dai kuma har yanzun faɗuwan gaban sa na yawaita, da Abdoul ya dage ba yacce zai yi qarshe yarda yayi ba dan yaso ba amma bai qudiri aniyan kwana ba yana zuwa ya gaida mutanen gidan su Abdoul ɗin zai kawo sa airport ya samu ya shirya komi na tafiyan sa yau ɗin nan. Abdoul ne jin yayi shiru yace "bros ya kayi shiru? Maganan tafiya yau fa kabar sa dan anan kam ba lallai ka samu Flight direct to Qatar ba sai dai ko in zaka hau na Abuja daga can to sai ka samu na Qatar kaga kuma duka long process ne gashi yanzu rana ya fara ka bari kawai anjuma kayi booking anan sannan mijin Ameera ya maka na Qatar ɗin in yaso d sassafe ka tafi ko in ansamu na dare sai kabi na Abuja da yamma da dare kuma ka hau na Qatar ɗin" Amjad ba yacce ya iya haka ya aminta suka nufi GRA. Amarya sashen baba qarami ta shiga tana bambami, kai jama'a Allah raba ɗan mutum da wahala yo in ba wahala da tangaɗi ba ace wai jikanka ya mai da kai birin wasa ai wannan ba ko kaffara uwar sa ke kista masa hmm! Shi uban kuma da yake maloho tangaɗaɗɗe baya iya stawatar wa an mallakesa ni Mairo na shiga uku an raba ni da yara na. Baba qarami da ke zaune a palourn mama hafsatu yana aiki a system nasa kasancewar yau yayan sa na hanya shiyasa bai fita aiki ba, muryan mahaifiyarsu da ya jiyo ne ya sanya shi rufe system ɗin ya miqe ya nufa hanyan babban palourn da yasan bazai wuce tana can ba. Tarar da ita yayi tsaye tana share hawayen da babu shi da gefen hijab nata, baba qarami na isowa har qasa ya durqusa yace "Gwaggo ina kwana antashi lafiya?" Wani kallo Amarya ta masa sai kuma ta fece hanci tace "yanzu ba dan ubanka mijina bane kuma ya rasu bawan na kwance cikin rahamar Ubangiji yo da sai nace dan jakar ubanka, amadu ban kwana ba kuma in mutuwa nake na rashin lafiya ba to ba ruwanka,kullum faɗi nake ka riqe azkar da salatin Annabi za ka fi qarfin duk wanni stubbace-stubbace amma dan tsabar lalacewa da tangaɗewa yaron nan ba kayi, amadu baka neman albarka" baba qarami dake stungune a qasa ba abinda yake cewa sai "Gwaggo ayi haquri a yafeni". Mama hafsatu da ke qarasowa palourn ne tace "Alhaji ai ba haquri zaka bada ba tambayan me kayi zaka yi" Amarya kallonta tayi sai tayi qwafa za tayi magana sai baba qarami ya riga ta "ke Hafsa banson rashin hankali". Amarya tace "a'a karka sona amadu ba laifinta bane ai komai tace kai ka nuna masu ba dai baka neman albarka ba?" Mama saratu ta qaraso palourn itama tace "Gwaggo Barka da shigowa ki zauna mana". Kallonta itama Amarya tayi sai kawai ta sa kuka "yanzu amadu fistaran da kuke shuka mun kai da matanka har ya kai haka? Wai ni da gidan Yaro na sai ance na zauna da uban wani ya gina masa gidan to banson shishishigi shigilitu, amadu kai dai Allah staremun kai amma mata sun mallake mun kai ai daɗi na da Haruna kenan bawan Allah gashi dai mace ɗaya gare sa kaman mahaifin sa amma yafi qarfin gidan sa yanzu dan stabar ba mai ganin girmana a gidan nan ace yaranku ma kun hure masu kunne sun fistare qafafunsu sun ɗauko baqin halin ku" baba qarami jin haka to yasan tabbas wani abun Abdoul ya mata dan in hayra ce ba mai jin tsakanin su suyi faɗan su su shirya acan ba mai ji amma in ta shigo tana faɗa tom indai yara ne Abdoul ne ya mata abu ko kuma Autan ta Jamila. Ajiyan zuciya baba qarami ya sauqe yace Gwaggo kiyi haquri Insha Allah zan ɗau mataki kiyi haquri ki zauna, Amarya kujera ta samu ta zauna har da ɗaura miqe qafa tace "tunda kana neman albarka har da haɗa ni da Allah tom na zauna Allah maka albarka amadu na Allah yasa ka gama da duniya lafiya yanzu dai amadu kaji storon Allah kaji storon haɗuwa da shi wai ace ba za ka yiwa yaranka faɗa ba ka nuna masu nice uwarka nice na haifeka sai sun kyautata mun nasa maka albarka kamun suma zasu samu kasa musu albarka su gama da duniya lafiya" ayi haquri Gwaggo Insha Allahu za'a gyara. Ai nasan zaka gyara amadu wai ni zancewa Abdu ya jira ni na ɗauko lufaya muje aikin ladan tare amma wannan
Chapter 60 · 0% Book details