Sashe 24
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ameera da Daddyn Little mutan Abuja jirgin su yayi landing lafiya, taxi ne ya kwashesu sai gidan su dake anguwan Asoo road a cikin garin Abuja. Sun yi isan yamma wanda hakan ya sanya bata yi girki ba bayan sun huta suka tafi eatery suka ci abinci suka dawo, da wuri suka kwanta dan gobe Daddyn Little na da morning meeting a wajan aiki kuma ya kwana biyu bayanan.
Yana aiki a 𝘾𝘽𝙉 (𝙘𝙚𝙣𝙩𝙧𝙖𝙡 𝙗𝙖𝙣𝙠 𝙤𝙛 𝙣𝙞𝙜𝙚𝙧𝙞𝙖).
𝙒𝘼𝙎𝙃𝙀 𝙂𝘼𝙍𝙄.....
Amjad bayan sunyi Sallahn asuba sallama ya wa Abban sa, daga masallacin bai koma gida ba hanyan gidan Sarki ya kama dan amsa qiran mai martaba, tafiya ne mai ratan gaske tsakanin su da gidan sarautan, dan gari ne guda Masarautan nasu.
Masarautan qubaish cikin jihar Al-khawr a qasan Qatar.
Gimbiya ba itace ta farka ba sai qiran farko na asuba, janye jikinta a na mahaifiyar ta tayi taje ta ɗauro alwala ta tada sallah.
Mai martaba ne ya shigo ɗakin da zummar tada su Gimbiya suyi Sallah, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo tarar da Gimbiya yayi akan sallaya tana nafila, ganin haka sai ya juya da niyan fita a ɗakin, mai ya tuna sai kuma ya dawo zama yayi bakin gadon ya jira ƴar tasa ta idar da raka'atainil fijir. Ko da ta idar durqusawa tayi ta gaida sa, sabahul khair papa, mai martaba yace "sabahul Noor ibnateey, khaifa antee khaifa Amma ki? Nahnu bi Khair papa, khaifal umur? Ibnateey umur sai shukran Lillah... Bayan sun gama gaisawa mai martaba yace "inkin idar da sallah anjuma inason ganinki kamun gari ya gama waye wa" ya faɗa yana miqewa dan fita zuwa masallaci. Tom Papa Allah kaimu adawo lafiya Allah amshi ibadunmu, da Ameen mai martaba ya amsa ya fice a ɗakin. Gimbiya carbi ta jawo ta fara lazumin ta kamun a shiga sallah.
Amjad ya iso gidan sarautan lokacin gari yayi haske, yana isowa qofan fada dogarayen dake wajan suka miqe suna gaida sa, fuska a sake ya ɗaga hannu ya amsa. Wani a cikin dogarayen ne ya masa jaroga har zuwa qofan shiga palourn baqi na mai martaba, suna zuwa qofan dogarin yace "ranka ya daɗe za'a maka iso ni iya nan ne mastaya ta, afito lafiya" yana gama faɗa ya juya ya bar Amjad tsaye a wajan. Yana tsaye wani dogari yazo ya masa iso har cikin palourn baqin, palourn mai girma ne yana ɗauke da set na kujeru 2 sai TV dake maqale a bangon palourn sai fridge babba a gefe, akwai toilet guda biyu a palourn da dai sauran su, palourn ko a Saudi albarka kenan.
Wani qofa dogarin ya nuna masa, yace "ranka ya daɗe wannan qofan zaka shiga mai martaba na ciki, afito lafiya ya masa" ya juya ya fita a wannan palourn. Kallon ɗayan qofan yayi ya tunkare sa, sallama yayi a bakin qofan sanda aka amsa masa kamun ya tura qofan ya shiga palourn.
Mai martaba ne a kishingiɗe sai wasu mutane guda huɗu a palourn, girman wannan palourn ya ninka wanda ya wuce domin kuwa wannan set na kujeru uku 3 ne aciki, sannan ga kumbo a jere a qasa set huɗu 4. Mai martaba na kishingiɗe a shumfiɗeɗɗen carpet da aka jera kumbon akai riqe da carbin sa, sauran mutane huɗun suna zaune a qasa da alama tattauna wa suke.
Zaunawa yayi a qasa shima ya sunkuyar da kai ya gaida mai martaba cikin girmamawa mai martaba da murmushi a fuskan sa ya amsa yana "ka saki jikin ka yarona Muhammadu" qara yin qasa da kai Amjad yayi ya kuma gaida waɗannan mutane suna cikin girmamawa, duk suka amsa da fara'a.
Mai martaba ne yayi gyaran murya kamun ya fara magana "Yarona Muhammadu waɗan nan da kake gani baqi ne da suka samu halartan wannan gasa da kuka yi jiya, sunji daɗin irin salonka kuma sun yaba da kwarjinin ka da jarumtar ka, wanda hakan har ya kwaɗaita masu neman wata alfarma a wajanka da kuma qarin kyauta na yabawa bajintan ka, nan mai martaba ya kwashe yacce suka yi da mutanen, abubuwan da suka faɗa da kuma daga inda suke duka ya faɗawa Amjad en, sannan ya faɗa masa amsan da ya basu, yanzu sun buqaci ganin ka dan amsa a bakin mai shi yafi daɗi, yanzu dai muna sauraran ka Muhammadu, mai martaba ya faɗa yana mai da kallon sa kan Amjad wanda kansa ke sunkuye.
Shirun da Amjad yayi shi ya qara burge Mai martaba dan ko ba komi tunanin babba da yaro ba ɗaya ba, yasan tabbas abun da ke ran Amjad bai wuce son shawartan iyayen sa ba. Mai martaba ya nisa yace "ya kayi shiru Muhammadu ?
Amjad Ya buɗe baki zai yi magana corp. Abeed ibn Zayd ya tari numfashin sa yace "ina ganin a barsa yayi shawara na, mu zamu tafi inyaso ko mai ya yanke daga baya a sanar damu mai martaba amma maganan kyautan goben nan Insha Allahu komi zai iso sa, hidiman biki kuma Allah nuna mana lokaci duk abin buqata za'a yi.
Mai martaba yace "shikkenan hakan za'a yi Allah mai daku lafiya, muna godiya sosai sosai". Amjad sai lokacin ya ɗago kan sa, godiya ya musu sosai da addu'oee.
Bayan sun kammala maganan Sallaman mai martaba suka yi duka suka miqe dan su samu su wuce akan lokaci, qara godiya Amjad yayi ya bisu da addu'an Allah stare hanya.
Bayan fitan su mai martaba yayi qiran wani dogari, da dogarin ya shigo ce masa yayi "a qiramun Gimbiya ta iso" amsawa dogarin yayi ya bi ɗayan qofan ya fice.
Ko da ya fita ya samu Gimbiya a main palourn sashen mai martaba a zaune don dama already mai martaba ya qira ta a waya jira take a mata izin isa ciki. Dogarin durqusawa yayi, yace "Allah ja kwanan Gimbiya Allah baki tsawon rai mai martaba na maki iso" gyaɗa kai kawai tayi ta miqe ta nufi palourn ko da ta isa bakin qofan janye abun da ta rufe fuskanta tayi ta kama handle en qofan ta murɗa ta shiga.
"Assalamualaikum" ta furta yayin da take shiga palourn, jin muryanta ya sanya shi ɗagowa, kallo ɗaya ya mata ya kau da kai. Amsa Sallaman suka yi shi da mai martaba, ganin sa a palourn ya sanya ta jin haushi buɗe fuskan ta da tayi, ba yacce ta iya haka ta qaraso ta zauna a wasa kusa da mahaifin nata, bata ko kalli inda Amjad yake ba tawa mahaifin nata Barka da hutawa ya amsa.
Mai martaba kallon su yayi duka biyun ya ga kowannen su gefe yake kallo kuma ba mai alaman yiwa ɗan uwan sa magana, girgiza kai yayi faɗi yake a ransa "duk zaku yi ku bari zaku dedeta kanku ba wanda ya sani".