← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 61

Sashe 12

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kan fafatawa suke tsakanin Yarima khaleed da Gimbiya Mehwish, sosai yarima Khaleed ya nuna Jarumta dan kuwa tunda aka fara gasan ba wanda ya nuna Jarumtan da ya nuna, ba tare da sun gaji ba dukansu. Ɗaga tokobin sa yayi da niyan kai mata sara kaucewan da tayi dan kare kanta, yayi amfani da daman ya kai hanunsa kan abinda tai rolling fuskan ta da niyan ya janye. Duk abinda yake Gimbiyar a ankare take, tana tare saran ta kuma yin qasa dan kaucewa hanun nasa domin hakan ne kawai kariyan da zata iya yi. Kaucewan da tayi ya sanya shi yin qasa ya faɗi domin da dukkan qarfinsa ya kai wannan harin, faɗuwan da ya janyo masa rashin nasaraa!!
haka duka ukun ta kaisu qasa. har Yarima khaleed!
Ba abinda kake ji yake tashi a wajan se ihun da jama'a suke yi suna qiran sunan Gimbiyar "𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼𝘼" "𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼" "𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼𝘼" 𝙎𝘼𝙄 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼𝘼𝘼 𝙈𝙀𝙃𝙒𝙄𝙎𝙃".
Iya sunanta kawai ke tashi bakin ɗauka cin jama'ar wannan wajan.
Fuskan ta ba abinda yake fidda wa sai walwalin murmushin ta!! Wanda inka tsaya kallon qwayan idanuwan ta ko ta kalle ka dasu tabbas zaka kusa sumewa! Ba tare da ta tsaya sauraron kowa ba ta wuce, dan mutumi mai magana ya tashi zai yi magana. Wucewa tayi dan nufan wajan da dokin ta yake tayi dan tafiya gida kuyangun ta suka rufa mata baya suna mata kirari! Sannan mutumin da ke riqe da Miche ma kirari yake Mata!
𝙈𝘼𝙇𝘼𝙈 𝙆𝘼𝙂𝘼 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼! 𝙆𝘼𝙇𝘼𝙉 𝙏𝘼 𝙆𝘼𝙇𝘼𝙉 𝘼𝙇𝙆𝙃𝘼𝙄𝙍𝙄! 𝙂𝘼𝘽𝘼 𝙎𝘼𝙇𝘼𝙈𝙐𝙉 𝘽𝘼𝙔𝘼 𝙎𝘼𝙇𝘼𝙈𝙐𝙉 𝙅𝘼𝙍𝙐𝙈𝘼𝙍 𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼! 𝙒𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃𝙄 𝙆𝙄𝙉𝙁𝙄 𝙌𝘼𝙍𝙁𝙄𝙉 𝘼𝙇𝙅𝘼𝙉𝙄 𝘽𝘼𝙍𝙀 𝙈𝙐𝙏𝙐𝙈! 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙅𝘼 𝙆𝙒𝘼𝙉𝘼 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼, 𝙏𝘼𝙆𝘼𝙒𝘼𝙍 𝙆𝙄 𝙇𝘼𝙁𝙄𝙔𝘼 𝙁𝘼𝙍𝘼 𝙈𝘼𝙄 𝙁𝘼𝙍𝘼𝙍 𝘼𝙉𝙄𝙔𝘼.......
Kirari kuyangun nata ma ke mata! Daga qafa tayi da niyan hawa dokin nata amma sai dai me? Muryan mai martaba Sarki ne ya ziyarce ta, abinda taji ya faɗa ne yasanya ta fasa hawa dokin domin ji tayi kaman sauqan aradu a kunnuwan ta!!
Bayahn Sarki yasa an miqa masa abun magana cewa yayi. "𝙄𝙉𝘼 𝙈𝘼𝙄 𝙈𝙐𝙍𝙉𝘼𝙉 𝙎𝘼𝙉𝘼𝙍 𝘿𝘼 𝙆𝙊𝙒𝘼 𝘿𝘼 𝙆𝙊𝙒𝘼 𝘼𝙐𝙍𝙀𝙉 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼 𝙈𝙀𝙃𝙒𝙄𝙎𝙃 𝙉𝘼𝙉 𝘿𝘼 𝙒𝘼𝙏𝘼𝙉𝙉𝙄 𝘽𝙄𝙔𝘼𝙍 5 𝙈𝘼𝙎𝙐 𝙕𝙐𝙒𝘼 𝙄𝙉 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙔𝘼 𝙔𝘼𝙍𝘿𝘼". Sarki na gama magana ta ji kaman an daskarar da ita a wajan gaba ɗaya ta rasa gane mema yake faruwa, ba tare da tabi ta kan dokin da tayi niyan hawa ba ta kama hanyan komawa gida da qafa. Abun yayi mugun razanar da ita amma bata ce komi ba dan ba abinda zata iya faɗa. Ta dai wuce jikinta na rawa idonta har yanayin sa ya sauya!!
Su ma hadiman nata ba yanda suka iya da ita tunda ran uwar ɗakin nasu a ɓace yake ba mai bakin magana. Haka su ke bin ta a qafan su ma suna mata kirari. Yayin da ita kuma take ji a ranta kaman ta rufesu da duka amma bata da ko bakin magana dan abinda ke damun ta!! Haka suka miqa hanya da qafa.....

(Mastowa nayi na ce, afuwan uwar ɗaki na! hararan da tamun ne ya storita ni har ban san sanda na ganni a 𝙉𝙄𝙂𝙀𝙍𝙄𝘼 𝘽𝘼).

🄱🄰🅄🄲🄷🄸
^^ Kakus ce ke magana "Harara wai ba zaki qira driver ya zo ya fitar masu da kayan nasu bane kam?" Hayra ce tafito kitchen tana tura baki! Tana qunquni akan sunanta da kakar tasu ke ɓatawa. Ficewa tayi tai waje, Ameera tace "Amarya ba kin gaji da mu ba dole kiyi-kiyi ki koramu ai". Salati Amaryan ta sanya yanxu dan kawai sharri da balagaggen rashin kirki da ke damunki yaushe mukayi haka dake takwara? Yanxu duk kukan da nake a zuciyata baki gani ba so kike nata birgima ko? Tom dan ubanki Haruna bazan yi ba. Wuce ma ki fice ku barmun gida dama na gaji da kallonki, dariya Ameera da mijin ta suka sanya!! Driver ya shigo ya ɗau kayan suka bi shi suka fice a part en. Mama hansatu da mama Saratu suka samu wajan da hayra, ban kwana suka masu su na Ameera ta gaida masu Umman yara. "Insha Allahu zataji mama" faɗin Ameera suna shigewa motor da Daddyn Little en. Sallama suka wa Kakus en tasu, driver ya tada motor se Amarya ta fara hawaye!! Ayya takwara ku yafe Ni in na ɓata maku har dakai Angon Amarya, Allah stare maku hanya ya kaiku lafiya Alfarman Annabi SAW, dukan su wajan amsawa sukayi da "Sallallahu Alaihi Wasallam" driver ya ja motor suka yi hanyan airport dan wuce wa KD saboda yau soja zedawo.
Haka suka rabu kakus harda sharan kwallanta tana "takwarata yar albarka yar aljannah se an kuma leqo mu ko kuma wataqilan sai na mutu a kuma zuwa. murmushi su Hayra da su mama hansatu suka yi a haba dai Amarya zasu kuma dawowa Insha Allahu. Tom Allah ya sa ta faɗa ta juya tayi hanyan sashin ta, suma sukayi nasu. Harara qawar Amarya zo ki ɗau ko man goro a ɗaki Qur'ani har na fara kewan takwara ta Allah Sarki, fece hanci tayi ta share qwalla!!

Qarfe 2 na rana ta masu a cikin kaduna garin gomna. Sun sami Umma da Abba yau kam a gida duka kasancewan yau shalelen Abba zai dawo ko aiki bai je ba. Sosai Abba Yaji daɗin ganin ɗiyar tasa da kuma mijin ta suna lafiya lau. Sannu da hanya su Abba suka masu bayan mai aiki ta kawo masu ruwa suka sha. Sallah ko wannen su ya tashi ya je yayi kamun suka dawo su ka zauna, hira suke yi kai kace Daddyn Little da Abba ba surukai ba. Shi kuwa Little yana maqale jikin kakar tasa.
Qarfe 4:00pm na rana yai masu a 𝙆𝘼𝘿𝙐𝙉𝘼 𝙎𝙏𝘼𝙏𝙀 𝘼𝙄𝙍𝙋𝙊𝙍𝙏.
dai-dai lokacin jirgin su yai landing a Nigeria cikin babban birnin Kaduna.
Sauqo wa mutane ke yi daga jirgin da yayi landing ɗin ɗaya bayan ɗaya
Leqa wa kawai Umma da Ameera keyi su ga ta inda ɗan autan nata zai fito, ita kuwa tilon qanin ta wanda bata da kaman shi a duniyar nan.
Wowww!! Shi ne abun da na furta kawai, Wani kyakkyawan saurayi ne kyakkyawa ajin qarshe. Sanye yake da T-shirt na sojoji da kuma army green jeans. fari ne amman ba sosai har can ba, kyakkyawa ne na qin daɗawa jikin sa ya nuna Jarumtan sa kana ganin sa kaga Soja don a dire jikinsa yake kana ganinsa za kai tsammanin ya kai shekara 30 aduniya(abunku da girman falo)
Ai kuwa Ameera na ɗaura idon ta a kansa da gudu ta je ta rungume sa ayoyo bruh, murmushi yayi!! sisto ƴammatan Daddyn Little ayoyo too, minstinin shi ta yi kaifa ka renani matsala na da kai. Turo baki yayi ya wuce wajan umma, Wayyoo ummana!!!! Dariya dukkan su suka saka "Allah shirya ka 𝙃𝘼𝘽𝙀𝙀𝘽" faɗin Abba. Da Ameen ya amsa yana hugging Abban nasa da Daddyn Little en. Ya je ya faɗa jikin Umman sa, ta ce "ah ah tashi ni kar ka karya ni a gaban nasii" Dariya yayi Umma kina so amun dariya ko? Amsan Little yayi a hanun ta yana "Umma ta bani yaro na, my Big broh ya akayi? Washe baki Little yayi unkui fafiya. Dariya yayi suka nufi motor dukan su driver ya ja suka yi gida.
Daɗi a wajan waɗan nan iyalin ba ya misaltu wa don ganin sojan nasu.....

Kar mu shagala fan's sunan littafin namu "𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀" daga Alqalamin Uwar Batoorl 🔥

𝙈𝙚 𝙢𝙖𝙞 𝙢𝙖𝙧𝙩𝙖𝙗𝙖 𝙠𝙚 𝙣𝙪𝙛𝙞?
𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙮𝙞 𝙙𝙖 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙈𝙚𝙝𝙬𝙞𝙨𝙝 𝙠𝙤 𝙠𝙪𝙬𝙖?
𝙈𝙚 𝘼𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙮𝙖𝙮𝙞 𝙞𝙙𝙤 𝙗𝙞𝙮𝙪 𝙙𝙖 𝙨𝙝𝙞 𝙟𝙪𝙮𝙖𝙬𝙖𝙣𝙨𝙖?
𝙁𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙖𝙝𝙖𝙡𝙞 𝙣𝙖 𝙜𝙖𝙣𝙞𝙣 𝙨𝙤𝙟𝙖𝙣 𝙣𝙖𝙨𝙪 𝙢𝙖𝙞 ɗ𝙖𝙪𝙧𝙚 𝙬𝙖 𝙣𝙚 𝙠𝙪𝙬𝙖?
𝘼𝙪𝙧𝙚𝙣 𝙜𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖𝙣 𝙯𝙚 𝙮𝙪𝙬𝙪 𝙣𝙖𝙣 𝙙𝙖 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙗𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙠𝙪𝙬𝙖?
Muna da tambayoyi da yawa waɗan da duka amsoshi su abun samu ne in muna bibiyan wannan labari

Muje zuwa fan's

Ku nishaɗantu, ku faɗakantu, ku wa'azantu, sannan ku dara🤣 daga alqalamin uwar batoorl takuuuuuuu ako da yaushe
Fatan alheri agare ku masoya alqalamin uwar batoorl a ko ina kuke a faɗin duniyar nan....

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮𝙪𝙠𝙖:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞,

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl✍🔥)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

_______________________________________________________________

🅿️ 27&28

💋💋 امى بتولة💋
Chapter 12 · 0% Book details