Sashe 39
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 45&46
💋💋 امى بتولة💋
Kasancewan yau Sunday ba aiki da sassafe Ameerah ya haɗa kayan karyawa suka shirya suka nufi asibiti.
Isan su asibitin direct wajan abokin nasa ya nufa ita kuma Ameera tayi ɗakin da mara lafiyan nasu yake
Da sallama ta shiga ɗakin ya amsa mata
Wajan gadon taje ta zauna kamun ta gaida shi
Yaya na fatan ka tashi lafiya ya qarfin jiki?
Lafiya Alhmdlh jiki da sauqi sosai
Masha Allah haka muke so yayana Allah qara afuwa
Ya amsa da Ameen daga haka bai qara cewa komi ba Ganin haka itama bata ce uffan ba
Suna zaune shiru Daddyn Little yayi sallama ya shigo
Amsawa suka yi a tare ita da mara lafiyan
Gaisawa suka yi da Daddyn Little ya masa ya jiki? Yace "da sauqi sosai"
Ameerah ce tace "husby har ka karɓo mana Sallaman?
A'a wiffey ban same shi ba kinsan yau Sunday ba lallai yazo da wuri ba ga kuma munyi sammako
Tace "Tom shikkenan sai kazo nasa maku abun karyawa"
Sauqa tayi ta shumfiɗa masu babban darduma ta jawo kondon kayan karin ta zuba masu peppe chicken da chip's sai soyayyen kwai ta haɗa masu tea kowa da cup na sa.
Yayana ka sauqo ku karya ko
Ba musu ya sauqo a gadon suka zauna tare shi da Daddyn Little kowa ya ɗau spoon
Chips en yaci kaɗan sai kuma peppe chicken, a jiye cokali yayi ya ɗau cup na tea yana kurɓa
Daddyn Little ne yaci abinci sosai da ya gama ya ɗau tea shima
Suna gamawa ta masto ta tattara wajan sannan ta koma ta zauna
Bayan wasu lokuta Daddyn Little barin danna wayansa yayi ya maida aljihu, miqewa yayi yace "ba na koma wajan likitan nan ko ya zo" Ameera ta amsa adawo lafiya to
Office na likitan ya nufa cikin sa'a kuwa dai-dai isan sa qofan office ɗin lokacin likitan ke isowa shima, da murmushi suka kalli juna Daddyn Little yace "kai man wanne irin likita ne kai haka ka tsaya soyayya kabar mu a asibiti tun qiran asuban farko".
Dariya ya saka wato dai freind sammako kuka yi gaskiya sannu da qoqari Nikam inacan manne da matata sai yanzu aka barni na fito
"Ɗan iska Zaka ji dashi ai Nikam buɗe mana qofa mu shige" Daddyn Little ya faɗa yana dariya
Tare suka shiga office ɗin da sallama, likita ya zauna a wajan zaman sa shi kuma ya nema wajan zama ya zauna
Gaisawa suka yi suka ɗan taɓa hira kamun Daddyn Little yace "kaga frnd sallame ni nasan zaka je duba Patience's naka so kar na ɓata maka lokaci a sallamemu mukam.
sallama ya rubuta masu sannan da sauran magungunan da ake buqata na game da qafan nasa
bayani ya masa yacce za'a sha da na shafawa duka sannan ya kamata ya kai sati a gida kamun ace ya fara fita sai dai yana da kyau ya dinga mosta qafan yana ɗan takawa dan zai fi saurin warke wa ko bai cika sati cif ba
Daddyn little yace "bakomi doctor Insha Allah za'a kiyaye fitansa yanzun fatan mu dai Allah sa ya warke da wurin
Musabaha suka yi ya kuma yiwa abokin nasa godiya yai masa sallama ya fice a office ɗin
Wucewa pharmacy dake cikin asibitin yayi dan ya sayo maganin da aka rubuta a hanya ya haɗu da Abba ya shigo qara duba marar lafiya kamun ya wuce don jiya bai samu komawa ba.
Tare suka je pharmacyn aka basu maganin duka da suka je wajan cashier Abbane ya biyan kuɗin duka yace Daddyn Little ya bari
Suna gama biya suka koma ciki wajan su Ameerah
Gaishe da Abba yayi suna tafiyan sannan ya masa godiya Allah qara arziqi Abba l
Ameera ganin Abba sai taji daɗi sunkuyawa tayi ta gaida Abban nata ya amsa da fara'a yace "sannunku da qoqari mamana"
Gaisawa suka yi da mara lafiyan
Ya masa ya jiki? amsawa yayi da sauqi Alhaji
Umma ya qira bayan sun gaisa sai ya bawa Ameerah wayan
Karɓa tayi ta gaisa da Umman, tambayanta mai jiki tayi tace "da sauqi sosai har an sallamemu"
Umma tace ta basa wayan su gaisa
miqa masa tayi "yaya na ga Umma ku gaisa"
Amsan wayan yayi ya kara a kunnen sa, lumshe ido yayi bayan Jin sallaman Umman Ameera
Bai san meyasa ba jin muryan wannan baiwar Allahn na rage masa kewan Umman sa.
Gaisawa suka yi tace masa "yanzu ya jikin naka yaro na?
ya amsa da sauqi Alhamdulillahi
Addu'oee tai masa sosai wanda yasa shi Jin daɗi fin tunani gaba ɗaya sai yake jin kamar Ummansa ce.
"Ameen ya Hayyu ya Qayyum Nagode sosai Umma Allah saka da alheri"
Suka yi sallama ya miqawa Ameerah wayan
Sallama itama suka yi tace" ga shinan Umma ba na miqa masa"
Daddyn Little ta miqawa wayan tayi amsa yayi suka gaisa da surkar tasa
yace "Umma bakomi Allah qara girma mungode sosai"
Ya miqawa Abba wayan bayan sunyi sallama
Abba kara wayan yayi a kunne ya fita a ɗakin.
Ameera tattara komi da suka zo dashi asibitin tayi Daddyn Little na taya ta yana kwashewa ya kai masu motor
Bayan sun kai komai motor Taimaka wa mara lafiyan yayi yana ɗingisawa har suka isa in da motorn nasu yake Parke, suna isa yabuɗe masa murfin back seat ya shiga ya zauna.
Sallama suka yi da Abba, escorts nasa suka tada motor sae filin jirgin dake garin Abuja
Gaba Ameerah ta shiga Daddyn Little ya shige mazaunin driver ya jasu sai gida
Hira suke sama-sama a motorn suna sako sa shi kuwa yayi nisa a tunaninsa baya amsawa hiran nasu ma (dama shiba ma'abocin surutu bane).
Driving yake a hankali
Juyowa yayi ya tambayesa bro akwai abunda kake buqata mu tsaya mu saya kamun mu wuce gida?
Girgiza kai kawai yayi bai ce komi ba
Ameerah ce tace "husby ka tsaya musai koda fruits ne to"
Tsayawa suka yi suka saya da yawa kaman masu sari, aka sa masu a boot en motorn suka biya suka qarisa gida
Suna isa mai gadi ya buɗe masu qofan yana ranka ya daɗe sannunku da dawowa amsa masa yayi
Parking space ya isa yai parking motorn
Ɗakin da suka shirya already don shi a balconyn gidan Daddyn little ya temaka masa ya kaisa har ɗakin
Ɗakine madedeci mai ɗauke da duk wani abunda mutum zai buqata a ɗaki
Gado,walldrop,resting chair,mirrow, bathroom dis and that ETC.
Komai na ɗakin blue color ne
A bakin gadon dake ɗakin suka zauna duka yace masa "sannu bro, sannan ya ɗaura da basa haquri akan abunda ya faru tsautsayi ne ya yafe sa".
Murmushi kawai yayi bai ce komi ba dama Daddyn Little yayi tsammanin haka
Mutumin bai fiye magana ba sai dai wani lokacin gwanda in Ameerah ce yakan amsa mata jefi-jefi
Bayan taga wucewan su itama cikin gidan tayi
mai gadi ne ya jido kayakin dake motorn duka ya biyota dashi sallama yayi ya jiye masu komi a palourn.
Tana shiga ɗaki ta wuce direct dan ta watsa ruwa ganin yanayin garin ana zafi
Bayan Daddyn Little ya masa sallama wucewa yayi cikin palourn nasu ganin bata nan ya wuce ɗaki dai dai ya samu Ameera ta gama shirin shiga wanka tana tsaye ɗaure da towel sai kawai taji an rungumeta ta baya
Ajiyan zuciya ya sauqe ya lumshe ido yace "wiffeyh wankan zaki shiga ki qyaleni bayan kinsan na gaji ba iyayi da kaina zanyi ba" ya faɗa da alaman shagwaɓa.
murmushi tayi kai mutumin nan kai fa yanzu ka wuce wanka da yaron ka kuma ga wani ajiyan a ciki kaga ai sai dai awa yaran ka badai a maka ba
Sa hanu yayi zai kunce towel en au wato nine ma mutumi bama za kice husbyn ba ko
Bige hanunsa tayi kai fa ka tsufa yanzu Baban Little
kutt nine na tsufa a guje tayi banɗakin tana addu'an shiga toilet
murmushi yayi! Allah ya barmun ke Ameerah ta Allah sa na rigaki mutuwa dan bana jin zan iya zama da kowacce mace bayan ke Allah maki albarka
Shima banɗakin ya shiga, wankan suka yi tare suka fito fuskansu da murmushi daga gani kasan qaunan junansu suke sosai basa fatan abunda zai rabasu in ba mutuwa ba.
Shirya junansu suka yi, suka faɗa gado tare Ameera tace "washhh baban su little na gaji" bakinta ya kaiwa cafka in baki daina ceman babansu ba sai na cire maki baki yarinya
Kissing junansu suka fara
Janye bakinta tayi tana murmushi kwantar da kanta tayi a qirjinsa tace
"Husby yanzu ya za'a yi da bawan Allahn nan? sa hanunsa yayi yana shafa kanta nima kaina abunda nake tunani kenan wiffey ban san ko zai yarda ya zauna damu har ya samu lafiya sosai ba, gashi bai son magana bare muji ko zai faɗa mana ko kaɗan ne dangane dashi.
Amma kasan me husby ni wallahi sai fuskansa kemun ɗan yanayi da na Abba
Dariya Daddyn Little yasa amma dai wiffey bakisan kama ba to kina ga mutum kaman balarabe kice yana kama da Abba shikkenan kinga anyi 1-1 kema kin zama tsohuwan idonki bai gani har gwanda na amaryata akan ke
Hararan sa tayi a wasa ni dai ka dai na haɗani da wancan stohuwan da ta gama zamanin ta
Hiransu suka cigaba dayi a haka har bacci mai daɗi ya ɗauke su .
A nasa ɓangaren ma haka ya lallaɓa ya shiga bayi yayi abunda zai yi ya fito ya kwanta dan ya huta wa zaman asibitin da yayi na kwanaki.
Abba sun isa airport inda suka shige jirgi suka kama hanyahn KD