← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 61

Sashe 57

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢 𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 𝟑𝟎𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 𝟑𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 𝟔𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 𝟕𝟎𝐩
𝟑𝐆𝐁 - 𝟗𝟎𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 𝟏𝟎𝟎𝟎

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 𝟑𝟎𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 𝟑𝟎𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 𝟔𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 𝟔𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 𝟗𝟎𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 𝟗𝟎𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......

Tura qofan tayi a hankali kaman mai storon wani abu ta shige, ganin baya palourn sai ta nufi ɗakin ta tura qofan a hankali shima.
Kwance ta hangosa a can qarshen gadon cikin bargo, da tsoro haka har ta isa wajan gadon ta tsaya a bakin gadon tace "ya habeeb wai kazo muyi dinner inji Umma".
Jikin sa na rawa har muryan sa yace "am not well koma ki kawomun nan".
Juyawa tayi zata fice a ɗakin, yace "and bance ki faɗawa kowa banda lafiya ba inma ba zaki iya kawomun abincin ba ki bawa mai hankali ta kawomun" ya qarisa faɗa yana jan bargon ya qara lulluɓuwa.
Duk da maganan da ya mata na mai hankali ta kawo masa ya qona mata rai! Amma tausayi da kuma irin zuciyanta na indai taga mutum ba lafiya ko kaɗan bata nistuwa bai bari ta ɓata rai ba bare ta masa rashin kunya juyawa tayi ya fice a ɗakin.
Dinning ɗin ta qarisa Abba ne ya ɗaga kai ya kalle ta yace "doter ya na ganki ke ɗaya? Ko yana zuwa ne?
A'a Abba yace wai na kai masa ɗakin sa acan zai ci.
Umma ce ta kalleta tace "doter kuma lafiyar sa qalau kuwa?"
Em e'e eh Ummeyh uhmn Umma eh lafiyan sa qalau yace kawai na kai masa ɗakin ne yana wani aiki ne a system nasa wai baison fitowa(batasan randa ta sharara qarya ba bashiri).
Umman tace "Fine tom Allah qara lafiya ki kai masa can ɗin".
Ganin yacce take abu a hankali Ummeyh tace "Maha lafiyanki kuwa baza kiyi abun kaman mai jini a jika ba ?"
Tura baki tayi ta haɗa komi a kan tray ta ɗauka ta juya bata ce komi ba, zata tafi Little ya sauqo a kujeran da yake zaune yace "Anci nima anbiki wajan unkui inci acan".
kallon sa tayi tai masa murmushi tace "no my boy sit and eat with your granny ko, uncle na aiki baison surutu, am coming now just kamun kayi 1 spoon ma na dawo sai muci tare okay.
Ba dan ya so ba sai dai da tace kamun yayi cokali ɗaya ta dawo sai ya ɗaga mata kai ya juya yana fadi cikin gorancin sa "anci ci camun abinci bifoi auncina a dawo".
Ita kuma ta juya ta wuce kai masa abincin.
Mahreen tace "dama rigiman da ya hana ka ci ya saka maka dan ba zan tashi ba".
Ummeyh ce ta kalle ta Ba shiri ta miqe ta saka masa suka ci gaba da cin abincin su.
Da sallama ta shiga palourn nasa har can cikin ɗakin, a qasa ta a jiye abincin.
"Yaya ga abincin ka tashi kaci" ta faɗa da alaman tausayi.
Yaye bargon da ke jikin sa yayi ya sauqo gadon yana duddurqusa wa yana kama cikin sa, zaunawa yayi ya jingina da gadon nasa.
Tana tsaye daga gefe idon ta har da kwalla duk tausayin sa ya cika ta.
"Sai nace kizo ki zuba mun ne? Kin zubawa mutum ido to li'eelafi quraishi" ya faɗa yana ciza leɓensa da alama cikin na damunsa sosai.
Duk abun da ya keyi bai dame ta ba mastowa tayi ta durqusa ta zuba masa abincin.
Tana gani in yasa hanu zai ɗauki spoon rufe ido yake alaman cikin nasa na damunsa , gyara zama tayi ta karɓi spoon en ta ɗiba ta kai masa baki.
Har da kaman bazai karɓa ba ganin cikin sa da kuma yunwan da yake ji buɗe baki yayi, haka ta dinga ɗiba dede-dede tana basa yana karɓa, har yaci dede ya kauda kai ya qoshi, ruwa ta ɗiba ta basa ya amsa da kansa ya sha ya maida kansa ya jingina jikin gadon.
Kallon sa tayi tace "magani fa yaya? A ina yake sai el na ɗauko maka."
Bedside drawer ya mata nuni da, tashuwa tayi ta ɗauko ta kawo masa. Amsa yayi ya sha ya miqa mata, ta karɓa ta mayar in da ta ɗauko.
Kwanukan ta tattare tace "Allah qara sauqi yaya" da Ameen ya amsa ita kuma ta fice a ɗakin.
Bayan fitan ta tashuwa yayi ya haura gadon yana jin relieve sosai, bayan ya kwanta ya lumshe ido wayan sa dake silence ne ya fara vibrating.
Miqa hannu yayi ya ɗauko wayan yai picking, bayan ya gama wayan ajiye sa yayi a gefe ya juya yai rub-da ciki yana tunanin wannan yarinya.
Bayan ta fita ɗakin, ta same su duk a palourn har sun gama cin abincin, wucewa tayi ta maida kwanukan ba tare da ta ci abincin ba ta dawo palourn ta zauna.
ana hira amma gaba ɗaya hankalinta baya wajan, "Wani irin tausayi ne da ita in dai mutum bai da lafiya haka take koma wa ko abinci bata ci sosai tun dai tana yarinya".
Abba ne yace "doter kinci abinci kuwa?" Ɗaga kai tayi eh naci Abba. "Tom me ke damunki doter? Naga kaman ba kijin daɗi ko halin da kuka saba sayarwa kukayo ke da yayan naki" faɗin Umma.
Umma lafiya ba komi kai na ke ɗan ciwo kawai, subhanallahi! headache ɗin ne kawai doter? Gidan ku da kawai ɗin tashi ki nemi magani kisha kije ki kwanta.
Tashuwa tayi tana faɗin "tom Umma ta" ta tashi ta wuce ɗakin su ko da ta shiga ɗakin direct kan gado ta faɗa ta kwanta rigingine(kanta na kallon POP na ɗakin). Gaba ɗaya ta kasa ko rinsta ido ma so take tasan wani hali yake ciki kuma yaya jikin nasa.
Chapter 57 · 0% Book details