Sashe 11
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
^^Zaune suke suna karyawa. Ummace tace "Abban jarumin Umma wai yau ba zuwa kasuwa ne kam?" Wanne zuwa kasuwa kuma Maryama ai sai an qarqare wannan gasa a ido na Insha Allahu. Murmusawa Umma tayi! Tace "Ni ko naji haushi da Jarumin Umma bayanan, dan naso ayi gasan nan a idon sa". Ai ko bayanan dole ma na basa labari Maryama, dan nasan ɗan ki ko yana nan ba lallai ya yarda yaje wajan taron can ba, mutum sai kace ɗan aljanu bakason shiga jama'a bakason magana da mutane. Umma ce ta haɗa fuska tace "nifa Abban jarumin Umma ba nason cin fuska ɗan nawa ne ɗan aljanu? Tom ashe ni da kai aljanu ne. Dariya Abba yasa! Allah baki haquri Sarauniya Maryama ta Abban jarumi daga ke ba qari! Ɗan ki ɗan mutane ne ba aljanu ba kyakkyawan yaro mai kama da Umman sa. Ba shiri Umma ta murmusa!! "Yauwa ko kai fa mijin Maryama daso". Yanzu dai tunda ɗan ki baya nan tashi na tayaki ayyuka mu samu muje wajan taron nan da wuri dan so nake in ga qaqa zata kaya, ya zasu qare. Umma ce ta miqe tana cewa "Tom Abban ɗana, Nima dai inaso naga mace mai kamar mazan nan ya zata qare gasan, dan da ace yarinyar nan namiji ne ba mace ba, wannan Masarauta ba zata kuka ba dan anyi rashin mai martaba sarki. Amma ita ɗin ma muna mata addu'an samun miji na gari alfarman Annabi SAW!!
🄼🄰🅂🄰🅁🄰🅄🅃🄰🄽 🅀🅄🄱🄰🄸🅂🄷
** inji malam ba haushe yace "𝙙𝙪𝙠 𝙖𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙖𝙠𝙖 𝙨𝙖𝙬𝙖 𝙧𝙖𝙣𝙖 𝙩𝙤 𝙩𝙖𝙗𝙗𝙖𝙨 𝙯𝙖𝙞𝙯𝙤, 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙙𝙪𝙠 𝙖𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙮𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙠𝙤 𝙩𝙖𝙗𝙗𝙖𝙨 𝙯𝙖𝙞 𝙮𝙞 𝙦𝙖𝙧𝙨𝙝𝙚". Kuma 𝙌𝙖𝙧𝙨𝙝𝙚𝙣 𝘼𝙡𝙚𝙬𝙖 𝙌𝙖𝙨𝙖!!
Yau take Ranan fafatawan nasu na qarshe a gasan. Ranar da tayi dai-dai da ranar Asabar(Saturday), Rana ta uku kuma ranar qarshe a gasan.
As usual(kaman ko wacce rana) wajan da yake ake yin gasan, ya cika sosai-sosai fun tunani! Kasancewan yau ne rana ta qarshe kowa nason ganin ya abun zai qare, wa zai yi nasara? Za'a samu mai faɗar da Gimbiyar kuwa? Daga waɗan da aka fara dasu har waɗan da ba suga farkon ba yau sun hallara taro yayi taro jama'a ba masa stinke, kaman ba kowa a cikin Masarautan bayan jama'ar wannan fili dan cikan wajan.(mai karatu kawai ka kwatanta hakan iya ganinka dan taro yayi taro)..
Umma da Abba ma har sun hallara suna maqale a wajan( shi kuwa gogannaku baima san mai ke tafiya a garin ba dan tsabar miskilancinsa da rashin shiga hayaniya ko jama'a gashi kuma yana daji).
Sarki na munbari wajan zaman sa da fadawan sa kaman koda yaushe. ƴaƴan Sarakuna dukkan su kowa na wajan da yake na zaman sa shi da muqarraban sa, da waɗanda sukayi da waɗanda ba suyi ba, dukansu sha biyu 12
Yarima Ahmad
Yarima Abham
Yarima Khalil
Yarima Suhail
Yarima Fu'ad
Yarima Ammar
Yarima Jawad
Yarima Waheed
Yarima Jaay(jabir)
Yarima Khaleed
Yarima Mu'azz
Yarima Abdoul. Duk ko wannen su na mazaunin sa.
Gefe guda kuwa wanda yake an qawata shi da ado gwanin burgewa da sha'awa! Gimbiya ce a zaune a wani haɗaɗɗen kujera da yaci ado, ado irin na sarauta, sanye take da kaya irin na mayaqa da ɗamaran ta hallau da rolling nata da ya rufe mata fuska, kayan nata daga sama har qasa Black ne,wanda ya amshi fatar ta kasancewar ta fara. Jakadiya na gefen ta a durqushe da kuma sauran kuyangu wanɗanda daga cikin su na hango, Laure da Hinde, sannan dogarai da suke staye gefe suna mata kirari.......
Mutumin da ke riqe da Miche(abun magana) ne ya tashi yai magana, kaman ko da yaushe, sannan ya gaida manyan-manyan baqi da kuma sauran jama'a. Magana yaci gaba da yi kamar haka:- "Kaman yacce muka sani duka, yau shine rana ta qarshe a wannan gasa namu wanda aka ɗauki stawon kwanaki uku anayi, kuma duk wanda ya cinye bi ma'ana ya samu nasarar buɗe fuskan Gimbiya tom shine ya lashe gasa. Sannan insha Allahu shine mijin Gimbiyar mu kuma Sarkin mu na gobe, kaman yacce kuma muka sani duka ƴaƴan Sarakuna sha biyu 12 ne suke gasan, sannan a yanzu uku ne kawai suka rage waɗanda ba'a fafata da su ba, a yanzu kuma za'a soma gudanar da gasan wanda muke sa ran yau za'a gama da yardan Allah, ga wanda ke da abun cewa tom fili domin sa, in Kuma babu tom zamu iya cewa, Allah bawa mai rabo Sa'a. Bissalam". Wasiqa aka miqawa wanda ke magana da Miche ɗin, kawar da Miche en yayi a bakin sa yace "wasiqan Menene?" Dogarin da ya kawo yace "saqo ne daga sauran yaran sarakunan da suka rage" to shikkenan ba mu isar da saqon wasiqan nasu. Buɗewa yayi ya karanta, sai da wasiqan ya isa wajan mai martaba yace ba komi sannan aka dawowa da mutumin wasiqan. Magana ya fara yi kamar haka:-
Assalamualaiki ya ke Gimbiyar wannan Masarauta tamu mai albarka, ƴaƴan Sarakunan da suka rage suna neman wata alfarma, acewan su tunda gasan da mutum ɗaɗɗaya akeyi, tom alfarman da suke nema shine a yanzu su ukun da suka rage, Yarima Khaleed، Yarima Mu'azz, da Yarima abdoul. Suna son su gudanar da gasan lokaci ɗaya ma'ana su ukun duka za'a fafata dasu a take, sannan suna fatan mai martaba Sarki da kuma Gimbiya zasuyi na'am da wannan alfarman da suke nema.
Jama'a ne suka fara surutu ko ta ina suna cece kuce kowa da abinda yake faɗa, "wasu na faɗin hakan baiyi ba, wasu na faɗin hakan ba dai-dai ba, wasu na faɗin haka ne ya kamata," kowa dai da abinda yake faɗa a nasa ra'ayin. Magana mai shelan yayi(wanda yake magana dama) "kowa yayi shiru jama'a, mai martaba Sarki ya amince da wannan buqata naku Yarima Mu'azz, Yarima abdoul, Yarima khaleed. Haka zalika a ɓangaren Gimbiya tayi na'am da buqatan ku, fatan nasara" ya faɗa yana neman waje ya zauna.
Sarki da yaji abunda mai shelan yace, lumshe ido kawai yayi! yana addu'an Allah ya sa wani a cikinsu su ukun yayi nasara, shiyasa ma yayi na'am da wannan buqatan nasu.
Ita kuwa uwar gayyar, ko a jikinta sai ma daɗi da taji komi zai qare yau Insha Allahu, dan tafisu jin daɗin amincewan Sarki kuma tafisu jin daɗin shawaran da suka yake, ko ba komai itama zata huta da shirmen nan. Idanuwan ta ta lumshe faɗi take a ranta "Ni MEHWISH ba dai mutum ya same ni dan wai shi jarumi ba sai dai dan ya cancanta ko in yamun, amma duk da haka ina burin auren jarumin jarumai, Allah ka tabbatar mun da alkhaeryh,amma a cikin waɗan nan bana jin akwai mijin aure na ni Ƴar Sarki Qaseem."
Haka aka shiga filin dagan domin fafata gasan, su ukun ne kaman yacce suka buqata ita kuma ita ɗaya, mai busan da ke nufi zasu iya farawa ne ya busa.
Sun fara faɗan abun gwanin burgewa ga daɗin kallo, dan kuwa faɗa suke bil haqqi, su uku sun dage ɗayan su sai yaci nasara. Ranta wasai take yin wannan faɗa ba ko alaman ta damu da kasancewan su har su uku ita ɗaya. Wani ne acikin su ukun ya nufi abun fuskan nata da biyan ya janye ganin kaman hankalinta yafi karkata kan Yarima Khaleed da yake jarumine na gaske kuma mayaqi yasan salo-salon faɗa da dama. Ai kuwa karaf ta kaiwa takobin nasa sara dan tana ankare da su dukan su ji kakeeee qasss qaqassssssssssssss har sai da takobin nasa ya ɗan lanqwashe, Jin saran da tai wa takobin nasa yayi kaman a hanunsa ta kai saran, dan sanda yaji kaman qashin hanun sa ya goce saboda qarfin saran. A haka suka ci gaba da fafata wa, ko wannen su na qoqarin samu ya kai hanun sa fuskan ta, koda da takobi ne. Yarima abdoul wanda aka kaiwa takobin sa Sara shine ta fara kaiwa qasa! Yarage Yarima Mu'azz da Yarima khaleed, ci gaba da fafatawan suka yi ba ji ba gani. A haka takuma kai yarima Mu'azz qasa! Ya rage filin su biyu Gimbiya MEHWISH da Yarima KHALEED. Fili domin su.......
🄳🄰🄹🄸
Tafiya yake akan dokin sa shi kaɗai, ba tare da jin storon girman jejin ko wani abu ba, tafiya dokin nasa ma yake a hankali, kalle-kalle yake yi, wanda da alama wani bishiyan yake nema, karatun Qur'ani yake yi qasa qasa yana tafiya akan dokin nasa, dai-dai wani babban bishiya da rasa gane na menene ya tsaya da dokin nasa, sauqa yayi ya shafa kan dokin yana masa magana "besty ka jirani ko ba na sari bishiyan nan nazo mu koma gida yau muga Umma" karkaɗa bindi dokin yayi yana miqar da kan sa, murmushi Amjad yayi yace "that's my besty dama nasan ka da jin magana, mintuna kaɗan ina dawowa." Qara sawa wajan bishiyan yayi ya sari jijiyan ya kuma sassaka bayan sannan ya ɗiba ganyen. Juyawa yayi ya koma inda yabar dokin nasa, a inda ya barsa nan ya same sa da murmushi ya shafa kansa ya haye saman sa yace "besty mu tafi ko" kaɗa bindi dokin yayi ya juya dan su koma gida. Juyawan da sukayi ido biyu yayi da......