Sashe 46
Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdoul ne zaune a ɗaya daga kujerun dake palourn kakar tasu, kujera me zaman mutum ɗaya 1 yana danna wayan sa. Hayrace tazo tawuce sa tana "Babban yaya sannu da zama halan yau kazo gadin kakus ne?"
Ke dai bari kawai boɗɗi Kakus hukuma ce sai da rarrashi, tace "tom nide nayi kitchen yaya kamun ta fito ta balbaleni ban gama girki ba rana tayi
Dariya yayi yace "keda kakus kam sai Allah kullum faɗa amma bata iya kwana bata ganki ba wataqil in mun aurar dake tare mijin ze aureku" Caraf sai a kunnen Amarya wacce ke fitowa yanzu daga ɗaki tace "Yo inba sinqin shishishigi shigilitu da sa ido irin naka ba ina ruwan ka tsakanina da baiwar Allah, Allah ne ya haɗa jininmu atou kuma qarshe ko mutuwa tare zai ɗauke mu bare miji da daman wannan dolen sa ne in dai ba'a tangaɗe aka haife sa ba ba mai raba mu" wucewa kitchen Hayrat tayi ba tace qala ba sanin halin kakar tata, ai kuwa dai bata stira ba dan kakus bin bayanta tayi da harara tace "kinanan a wajan kaman tangaɗaɗɗen budurwan kaza, ai da karma kije kiyi girkin yo ai ni dole ma na biki gidan miji kar kije kimana abun kunya tunda de baza kiyi abuba sai ance kiyi dan tsabar layiii" da ta gama ɓaɓatun zama tayi a kujera me ɗaukan mutum 2 tana bismillahi ni jikan mutum 4, Abdoul ne ya kalleta sannu da fitowa uwargida ta bayan ke babu wata sai dai amarya ya qarisa yana dariya
Da har ta washe baki sai kuma ta stuke bakin kallonsa tayi tace "Yau ɗan nan har yaudaran yakai haka a gabana kake faɗan sai de amarya? Tom jeka na yafe maka ka kawo badon halinka ba ɗan kwal uba"
Murmushi yayi shiyasa nake yinki amarya uwargida, gaisheta yayi ta amsa tana tambayansa ya aiki ya kishiyanta?
Murmushi yayi ai maganan kishiyan naki ma shi ya kawoni Hajiya Kakus tamu، Yauwa dai ango ai ni nafison haka kuyi aure tun da raina inga yaranku Allah raya ku ya baku zuri'a mai albarka, nifa so nake kan na mutu naga har da tattaɓa kunne na kaga ƴar albarka takwarata matar auwalu har cikin na biyu gare ta kaga da yardan Allah in ta haifi mace kan na mutu zan aurar da yarinyan, Murmushi Abdoul yayi yana jin shirmen kakan tasu bai ce komi ba shi dai .
Yauwa to wacece kishiyar tawa ma tukunna insan wacece ta shirya kishi da mairama daso, Murmushi yayi yace "wata baiwar Allah ce nutsaststiya kyakkyawa ga hankali ga ilimi ga tarbiya ga asali ga ga ga........."
Me amarya zata yi in ba dariya ba Abdu lafiyan ka ko dai duk ta tangaɗar da kai ne ta zautar mun da ango tun yanzu ta mallakemun kai, murmushi yayi haba de ai ni dake mutu ka raba, Tom irin wannan lissafowan haka ko kunya na baka ji ba yo ma ai ka rage dan ganin idona kar nayi kishi nace a'a ko, Murmushi yayi ai kema kinsan kin fita komi amarya uwargida kuma duk a wajanki ta gado su, washe baki tayi Allah maku albarka jikokina Allah sanya alkhaeri, da Ameen ya amsa yace "Kakus ba kowa bace face...
Maganan hayra ne ya tsaida shi tace "ya Abdoul yi sauri ka faɗa na matsu naji wacece akewa yabo ba kunyan kakus Allah yasa dai wacce nake tsammani ne"
Danqwalan ta kakus tayi to ƴar kwal uba haɗasu kasa rabasu bazaki shiga tsakanin mu ba kuma baza'a faɗa ba tafi ki bamu waje gulmammiya kawai, taɓe baki hayra tayi tace "in tayi tsami za muji" ta wuce abinta
Yace yauwa kakus AISHA ce fa MAHREEN
Guɗa Kakus tayi tare da kabbara tace "ALHAMDULILLAHI Allah nagode maka ni mairo, amma naji daɗin wannan batu Allah maku albarka Abdu, a Yauwa kaga ina ma wayana ne laluɓosa tayi ta miqa wa Abdoul tace "gashi dannamin layin ita uwar tasu tunda ta balaga ta balage garin su ba abinda ake koya masu sai tangaɗi bata neman albarkan uwarta to ni uwarta zan nemi albarkanta ƴar jakar uba kawai"
Qiramun ita in bazata zo ba ni zan iya zuwa har qasan masu layiin inba ma tsabar tangaɗe wa ba asawa gari sunan mutum wai fa sunan uwata sunan garin nasu tom dai bazai hanani qira ba, qasan kulu masu tangaɗaɗɗiyar hali suna koyawa yaran mutane fitsara da rena iyayensu wannan baqin halin har ina ni Mairo ɗan nan qiramun ita da wuri
Karɓa yayi haba kakus surka tace fa kibar zaginta nikam
Au ashe surkar ka ce? tom ban sani ba hanani faɗan abunda nayi niyan faɗa dan kwal ubanka jai'ri kawai ina ruwanka ni da ɗiyata inma me nace wani ya haifarman ita ba dai nice na haifi abata, shekara nawa ban sata ido ba ba dole abun ya dameni ba tunda zuciyata ni ba irin na ƴan kasar su bane, ita fa kaɗai gareni ɗiya mace, tom don haka karka shiga tsakanina da ƴata yar albarka
Murmushi yayi dama abunda ya sashi saka baki kenan ta dena mita gashi hartasawa ummeyhn tasu albarka
Numbern Ummeyh ya dubo ya qira, yana shiga aka kashe aka qira.
Miqawa kakus wayan yayi Kinga ma ta kashe ta qiraki gashi kuyi magana to
Yanzu dan tsabar ka renani baka ganin girma na ni uwar ubanka shine bazaka ɗaukan mun qiran ba na ɗauka da kaina dan jakar uwaka bazan ɗauka ba to
Ɗauka yayi da sauri gudun kar qiran ya yanke "Assalamu Alaiki gwaggo"
Amsawa tayi ah ah yaron gwaggo sai yau ake jinku kenan nasan yau ma albarkacin uwata aka qiran ko?
Sunkuyar da kai yayi yana sosa qeya ayi haquri Ummeyh abubuwan ne sai a hankali, Ummeyh taace "Bakomi yaron Gwaggo" gaisawa suka yi yace mata "ga kakus" ya miqawa amarya wayan
Amsa wayan Amarya tayi bayan ta karkata ɗaurin kwalinta
Sallama Ummeyh tayi kakus tace "bazan amsaba dan gidanku wato de Jamila kin girmi neman albarkan uwaki sede ni na nemoki bazaki iya zuwa ki ganni ba bare gaisuwa kema kinbisu kun taru kun tangaɗe kunzama tangaɗaɗɗu masu layi to yayi kyau ni Mairo bazan maki baki b Allah shiryaki y maki albarka, amma nasan wannan balaraben mijin naki baze hanaki zuwa ba dan hankali garesa ga sanin girman iyaye tunda dai yaron nan habu har yamun takwara, Ammade Allah ya shirya mun ku wallahi.
Ummeyh najin ta bata ce komi ba har ta gama magana sanin halin mahaifiyar tata "Kiyi haquri Gwaggo Insha Allahu bazan wuce kwana 2 ba zaki ganni" Ummeyh ta faɗa cikin ladabi
Yauwa dai yar albarka ko kefa ni shiyasa nake sa maki albarka kullum ko baki nema ba dan kinfi sauran jin maganata Allah de ya maki albarka ya rabaki da tangaɗewa har abada
Ta amsa da Ameen suka yi dan hira sama-sama can suka yi sallama kashe wayan tayi ta aje, qwalawa hayra qira tayi "Harirtu qawar kakus kawo man ruwa nasha ƴar albarka bakina sai zikiri yake duk sun bi sun sani surutu kaman kanari"
Hayran ta shigo da sallama ta miqo mata ruwan ta karɓa tasha, Abdoul ne ya murmusa yace "yanzufa kika koreta gashi da kanki kin qirata" hararan sa kawai Amarya tayi bata ce masa komi ba. Abinci hayra ta shirya masu suka wuce dinnig kowa ta zuba masa, cin abincin suke bame cewa komi
Sede kakus da bakinta baya shiru kana ganin bakin kasan akwai abunda yake son cewa..
Bayan ya turo mata layin ɗauka tayi ta qira amma sede be shiga ba ta gwada yakai sau uku 3 amma baya shiga akashe take ji, hankalinta ne ya tashi sosai dan haka kawai take jin kaman ba lafiya ba, dafe kai tayi tana ambaton sunan Allah "Ubangiji yasa ba wani abun ta sameka ba yarona" sai kuma tunanin ɗan ta yafaɗo mata rai nan take hawaye ya cika idonta jin kaman mostin mutum ya sanya ta saurin sharewa ta seta kanta, Mahreen ce ta shigo palourn zuwa wajanta tayi da sauri tana cewa "Ummanmu lafiya? Mai ya faru?"
Murmushi tayi bayan ta ɗago kai tace "lafiya lau doter kawai na qira wani layine auntynku Ameera suka turomun sai de bai shiga ba" Mahreen tace "to amma Umma tagumi ba kyau ki dena kinji Insha Allah lafiya lau layin kuma zai shifa kibari anjuma ko gobe ki gwada inyaso in bai shigaba sai ki qirasu ki faɗa masu ko zasu qira maki layin ko Umma"
Shikkenan doter ina Auntan Ummeyh fa? Tana can ɗaki da waya banmasan me take ba, Umma tace "to je ki qiramun ita" tashuwa Mahreen tayi tana to Ummanmu
Wucewa Mahreen tayi ɗaki dan qiran Maha, Umma Qiran aminiyar ta ne ya shigo wayanta ta ɗauka suna gaisawa da alama magana me muhimmanci suke yi.
Mahreen bayan ta shiga ɗakin ta samu Maha akwance tana danna waya, fisge wayan tayi tace "wai me kikeyi ne awaya kam maha?" Turo baki Maha tayi tace "ni don Allah ki bani kar ki batar dani inda nake abu ya ɗauko daɗi" Kallon fuskan wayan tayi ta kalli Maha mene wannan kuma? littafi ne? Maha tace "eh novel ne wallahi Adda kuma me shegen daɗi"
Kallonta tayi tace "ooh kekam da novel bansan waya koya maki karantawan ba ma ni Indo"
Allah kema Adda Mahreen in kin fara karanta littafinnan ba zakiso ki tsayaba ga abun tausayi ga darasi aciki ga daɗi kuma ayya barin ma maisunana ta cikin ɗayan littafin abun tausayi bakiga Yacce mamanta take treating nata ba, Kallon Maha tayi tace "to yanzu dai faɗamun sunan littafin dai ko"
Guda biyu 2 ne aka turomun masu shegen daɗi kekam ma ba'a gama labarin ba tukun ɗayan dai sunansa JAHILCI KO AL'ADA ɗayan kuma something maita ne ko me na mance amma Adda kinji daɗin littafin nan kuwa wallahi ya burgeni, murmushi Mahreen tayi ai kuwa zan karanta nima ba na samu zama
( KUMA FAN'S KARKU SAKE A BAKU LABARI DOMIN KUWA DA ƊUMIN SA YAZO
JAHILCI KO AL'ADA?
VERY SOON ZA'A SAKE MAKU SHI
𝙊𝙪𝙧𝙢𝙢𝙖𝙝𝙣 𝙗𝙖𝙩𝙤𝙤𝙡𝙚𝙧𝙝🔥 𝙛𝙤𝙧 𝙡𝙞𝙛𝙚 )
Tom yanzu tashi muje Umma ce tace na qiraki, tare suka fice a ɗakin sukai palourn wajan Umma..