← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 61

Sashe 37

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni wallahi ba zuwa wajanki ba sai son gwale mutum ba'a maki kaman dangin maza danma sunanmu ɗaya, sai kuma ta marairaice fuska yanzu ni zakici wa fuska tom nidái ubana bai da jaka ato".
Hararan ta Kakus tayi yo in bai da jaka ai uwaki tana dashi dun haka jakar uwaki yarinya sai kace ƴar ifiritun aljanu yo fisabilillahi zaki shigo man gida ba ko sallama bare salati salon ki shigo mun da qunbasarun aljanun kanki ko tom ta Allah ba taki ba nida kika ganni nan qaunar Annabi SAW nake bani ba sheɗanun jinnu
Mahreen da ta staya abakin qofa tana jin su me zata yi in ba dariya ba har da kama ciki. Tura baki Maha tayi ta juya jin sautin dariya ganin Mahreen ce ke yi ta aika mata da harara ta riqe qugu
Amarya tace "haba takwara ta kece fa kika zo zaki diranmun a kah kaman dusten garin kudun can ko nace kaman aradu yo da kin yi sallama ai da banyi surutu ba ɗan ladan amsa Sallaman kike mun baqin ciki samun shi to wa'alaikissalam ko baki yi ba na amsa kuma na samu lada ja'ira kawai
Qara haɗe fuska Maha tayi tace "da baqin halinki irin na jikanki habebu" qasa-qasa ta faɗa tana kallon hanyan qofa ganin yana shigowa.

Wani mugun kallo ya jefa mata na (zamu haɗu ne yarinya zaki gane kuranki) yayi sallama ya wuce ciki abinsa ganin yayansu abdoul ya zauna a kujeran dake facing nasa
hairat dake tsaye a gefe guda murmushi kawai tayi dan tafi kowa sanin halin stohuwan da sambatu da masifa ( ƴar gidan kakus kenan kullum tana nan)

Mahreen ma qarasa shigowa tayi bayan tayi sallama tana barka ƴar stohuwa tamu mai ran qarfe fuskanta ɗauke da murmushi.
Murmushi kakar tasu tayi da bakinta duk goro ta amsa Sallaman kaga nutsasttiya yar albarka mai nemawa al'umman Annabi ladan sallama, Ni banma san mai yasa waccan salawaitun uwar taku bata mun takwara da ke ba mai hankali da zubin mutane ba tawa uwar mijin ta ita gata tangaɗaɗɗiya son dangin miji komiti sai tamun da wannar mai zubin ifiritan aljanun sai kace ance mata a tangaɗe nake ko taga ina tafiya ina layii
Soja baya dariya sai ta ɓaci yana jin abunda stohuwa tace ya sanya dariya ai wallahi kuwa an cuceki dan wannan mara kunyan tana tafiya tana layii ai sai ya kuma saka dariya.
Maha ta cika tayi fam sai ta fashe da kuka ta juya tayi hanyan waje wai zata koma inda ta fito
Ya abdoul da tun ɗazu suna rigimansu bai tanka masu ba dan yasan yanasa baki shima xa'a solle sa, tashuwa yayi ya riqo Maha yace "ina zaki Autan mu? bayan ke fa ba kowa yarinya mai kyau ki qyale kaka baqin ciki take kin fita kyau kuma da mijin ta bai mutu ba tasan tabbas zaki kwacesa yi haquri ki daina kuka yar Autan mu mai sunan manya duk ki fita harkan su kinji Nana Maryama uwar isa" kirarin da ya saba mata tun tana yarinya in tana borinta ya mata ai kuwa sai kuka ya koma dariya.
Yaya Abdoul Allah kai kaɗai ke sona nagode Allah da baka zama soja ba da shikkenan ba mai sona nikam
Soja na jinta bai ce komi ba, stohuwa ma taɓe baki tayi tace "kai kuma balagaggen gauro zamu haɗu da kai inba aikin tangaɗewa da layii ba wato da wannan aljanar kake haɗani wai ta fini kyau ba da yake kaima tangaɗaɗɗen ne" tayi qwafa ta gustiri goro.
Mahreen da kanta ke qasa ta gaida ya Abdoul, Soja ma ya gaidashi ya abdoul fatan mun same ku lafiya?
Amsa masu yayi duka fuskanshi yalwace da murmushi muna Lafiya Auntan Umma the only SOJA.
Hairat ma ta gaidasu duka suka amsa, taje ta kawo masu ruwa da abun sha.
Duk abunda Mahreen keyi idon ya Abdoul na kanta sosai yaga saurin girman yarinyar ga wani kyau da tayi kaman balarabiya "Masha Allah" shine abunda ya furta a maqoshin sa ya lumshe ido tabbas nikam Abdoul naga matan Aure zan huce gorin wannan magananniyan stohuwan.
Tashuwa kaka tayi tazo ta zauna gefen soja tana gyara ɗaurin ɗankwalin ta.
Kai kuma ɗan sinqin sikitin shishishigi shigilitu dan tsaɓar naka layiin yayi yawa shine ba zaka gaisheni ba sai shishishigi ina magana da takwara ta zaka mana shishishigi ɗan jakar uba in kuma kaima ubanka baida jaka to jakar uwaka Aminatu ni bansan ina kuka koyo wannan tangaɗaɗɗiyan hali ba yara duk a tangaɗe kaman ƴaƴan masu layiii
Ai Ka zo da wannan baqin halin naka na rena mutane da qin masu magana kowa ganin sa'an ka kake masa sai dai a fara maka magana ba dai ka farawa mutum magana ba badai kaga ka balaga har ka fara ɗaga abinda ke kashe mutane ba(bindiga) yo ma akan me zanga laifin cubulle na ai gaskiya ta faɗa baqin hali gare ka sai dai ja'ira wai irin nawa dan a tangaɗe take zata haɗa halina mai kyau da naka halin boko-haram ai nasan kai ka birkita cubulle na baiwar Allah ƴar albarka shiyasa tace haka
Hannu ta miqawa Maha dake zaune gefen ya Abdoul zo abinki kiyi shiru cubulle ta ƴar albarka irin arziqi farar haihuwa.
Hararan kakus tayi baza'a zon ɗin ba kuma ina komawa abbieyh na zansa ya sanjaman suna nima an fasa takwara dake masifatun stohuwa.
Lahhh kina so aji tsakaninmu ne cubulle? su mana dariya yi haquri kizo kinji duk zugani suka yi shiyasa amma ai babu yake a sa'an suna kuma dan qafan ubanki na hagu in ya fasa sanja maki suna sunansa ba habubakar ba sai na kaisa har kotu in shima a tangaɗen yake taya Allah zai rufamun asiri yace zai tonamun akace Kana da takwarori bakwai 7 kai ɗan aljanna ne in dai kana qaunan Annabi SAW yo to ina qaunan Annabi so yake ya rageman shiga aljanna dan sinqin layiin da ubansa Arɗo yake yi
Maha ta taɓe baki "ki dai qarata da wanda yake gefenki dan ba zuwa zanyi ba kuma ki zagi har da matan Arɗo in kinso amma kibar zagan mun Uba" ta faɗa tana qara mastawa kusa da ya abdoul
Mahreen duk a takure take dalilin duk ɗago kai da zata yi sai taga idon yayansu akanta, ganin kakus ta tsagaita masifan nata gaisheta tayi ta miqe tsaye
Amsawa kakus tayi da fara'a mai halin ƴan aljanna ya naga kintashi ina zaki? Kede ba ruwanki da layiii dan ba'a tangaɗe kike ba
tsohuwa mai ran qarfe zan shiga ciki ne na gaji danma Allah yasa ya Habeeby yana tsayawa mu sallata a hanya
Ai dai daɗi na da shi wataran ba dai son ibada ba kaman ubansa Haruna bini-bini antsaya ayi salati ayi sallah kaman sallau shikkenan afito lafiya yar albarka mai ran roba.
Sa dariya suka yi duka Mahreen tayi gaba abunta
Ya Abdoul yace "a'a fa itama na qarfen dai gare ta ba na roba ba dan muma muga yaranmu da jikokinmu yacce kika ga naki".
Kallonsa kakus tayi ta murmusa abinka da babba kowa agurin bai gane me yake nufi ba sai ita kuma dama ya tsammani hakan
Kakus tace "oho dai itama ai buhun baqin hali ke damunta in ba baqin hali ba ana hira ka tashi wai zaka shiga ciki ni na gode Allah ma da sunana ba indo ba yo mai ake da halin masu suna indo, ganin ba wanda ya kulata sai tayi shiru da mitan nata.
Soja ya kwashe labarin hatsarin da mijin Ameerah yayi ya bawa Kakus.
Kakus kuwa Salati ta kwaso ta haɗa da kabbara Allah sarki ni daso bawan Allah yaji jiki Allah dai ya basa lafiya ya kuma kiyaye na gaba shi auwalun kuma da wuya kaman na mai tangaɗi ko uban wa ya basa mota ma oho dai asara yaje zai hallaka rayuwan ɗan mutane, yo to inba ni ba da yin abu kaman mai yawo kai a kunce ba marufi da gangan zai buge mutum ne wannan ɗan albarka mai tausayi da imani Allah sarki auwalu ka yafeni Allah kare na gaba
Ameen duk suka ce kowa na storon tankawa surutun wannan stohuwa.
Duk tashuwa suka yi dan kowa yaje ya huta kamun magriba tayi
Maha ko ajikinta haka ta riqe wayan Soja tayi ɗaki wajan Mahreen.

Little ke buɗe murya yana ihu "wayyo aunci na unkui na wayyo an bicu" kallon sa Umma tayi ta girgiza kai lallai zaka koma gidan iyayenka tunda halin ɗan wani ka fara nuna mun Little, tura baki yayi nidai anbi aunci da unkui na, ta buɗe baki zata yi magana qira ya shigo wayan ta.
Ɗauka tayi ganin Gwaggon murmushi tayi ya amsa qiran suka gaisa kowa lafiya lafiya, Umma tace "Gwaggon yara ke kuma sai yaushe zamu ganki?
Dariya tayi ya kamar matar nan tayi kewan mijin ta ne ba ga yayana a gida ba karki damu na kusa zuwa
Umma tayi murmushi "tace yo ba dole ayi kewan miji ba kunje kun zauna abunku a jiddah shiru-shiru bakwa leqo mu kin hanani samun ladan sa maki tuwo kici.
hira suke cike da da zolaya da fara'a sai ka ranste qawaye ne ba matar yaya da qanwar miji ba
Ummeyh tace "Ummansu Insha Allah qarshen satin nan xan xo naga mataaye na ( da matan baba qarami) da kuma uwata da yayyuna uwa uba yarana"
Cike da jin daɗi Umma tace "Allah yasa kur kisa mana rai this time ma Gwaggon yara mu gama shirya tarba baquwa taqi zuwa, Allah tabbatar dai ya kuma kawo mana ke lafiya.
Nikam ya doter da jikin nata fatan jikan namu ya barta tayi lafiya?
lah kinga na manta ban faɗa maki ba mijinta ma ya buge wani bawan Allah suna asibiti yanzu haka ɗazu ma yayanki ya dubo su ya shiga Abujan.
Subhanallahi hastari dai to Allah ya sauwaqa ya kuma kiyaye na gaba
Umma tace "Ameen ya Rabbi Gwaggon su". Suka yi sallama ta kashe wayan maida duban ta wajan Little tayi Angon gilani yi shiru abinka anjuma zan kaika ko ba abokin ka ya dawo mana da car kaji, da qyar ta samu ya lallashu yai shiru ya daina borin.
Chapter 37 · 0% Book details