← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 61

Sashe 18

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babban filin da ya kasance na gudanar da bukukuwan wannan masarauta, a cike yake fam da jama'a. Baqi da ƴan gari sun hallara a wannan babban fili mutane ne a cike ba masaka stinke, ganin yawansu zai sanya ka tsammanin ba kowa da ya rage a wannan Masarauta, saboda irin tarin jama'a dake wannan fili.
Manyan baqi da ya kunshi Sarakunan garuruwan da suke makwaɓtaka, manyan mutane daga qasashe daban daban sun samu daman hallattan wannan gasan kasancewar yacce Sarki ya furta na ko daga ina kake zaka iya shiga gasan sai hakan ya bawa labarin wannan gasan zagayawa har garuruwa da dama wanda ba'a tsammani ciki kuwa har da Nigeria, baqi ta ko ina anzo dan kuwa kusan zuciyoyin kowa cike yake da ɗimbin mamakin qarfi irin na wannan ƳAR SARKI...
Mai martaba kaman ko da yaushe yana wajan da yake tanade dan zamansa tare da fadawan sa in ana gudanar da wani shagali a garin nasa, baqi kowa na zaune inda aka tanadar dan baqi manya da sauransu. Gefe guda kuwa GIMBIYA MEHWISH ne zaune a kujeran da aka tanada domin ita, kuyangun ta ne zagaye da ita da sauran bayi maza.
Sanye take da kaya blue wanda colourn ya tafi da yanayin halittan qwayar idon ta, kayan riga da wando ne, wandon ya kasance mai ɗan faɗi wanda ba'a ganin yanayin jikinta hakama rigan bai kama ta ba sai dai ɗamaran da ta ɗaura a qugun ta wanda ya ɗan bayyanar da shape enta, ta rufe fuskan ta da baqin veil kaman koda yaushe ba abinda kake gani sai qwayan idon ta wanda yakan burge duk wani mai kallon ta. Irin shiga da haɗuwan da Gimbiya tayi da kyawun da wannan shiga ya mata, indai kana Kallonta tom kallonta kaɗai ya isa ya hanaka nasara akanta don haɗuwa kam Masha Allah!!

Gefen waɗanda za'a gwabza dasu kuwa Anwar ne a zaune tare da muqarraban sa, shiri yayi irin na masu zuwa yaqi, sosai dai shirin ya masa kyau ya amshe sa. Qaqqarfan namijine wanda kana ganin sa kaga jarumi na gaske, shi kaɗai ne zaune a gefen masu gwabzawan da dukkan alamu ɗayan bai iso ba tukunna.
Mai magana ne yake jawabi da kuma mawa manyan baqi Barka da halartar wannan taro dan wasu ba'a ma taɓa tsammanin ganin su ba. Sarkin shela na tsaka da yin magana yaji wajan yayi shiru juyawan da zai yi wani kyakkyawan mutum kuma qaqqarfa ne yake shigowa cikin taron, shigowan nasa ne ya ɗau hankalin jama'a har ya sanya kowa kusan barin zancen da yake .
Tafiya yake cikin taqama da kuma nuna stantsar Jarumta, wani bafade ne yai masa jagora har wajan zaman da yake aka tanada dan shi, zaman sa ne ya baiwa mutane daman gane cewa shine ɗayan abokin gwabzawan Gimbiya, nan take waje ya ɗau surutu qasa qasa kowa da abinda yake cewa.
Sanye take da kaya mara hayaniya zaka ranste ba dashi za'a gwabza ba, (dan ko shirin sa na zuwa jeji yafi wannan) sai dai shigen nasa yayi bala'in masa kyau Kasancewan sa fari kuma dogo sannan qaqqarfan jarumin na miji.
Siririn tsaki yaja ganin yacce duk akabi aka zuba masa na mujiyoyi(idanuwa) sosai ya tsani yawan kallo ga qananun surutun dake tashi a wajan, wanda baya da ko shakka gulman sa mutane keyi, tsakin ya kuma ja yana magana a zuciyansa "Ni wallahi Umma ba don ke ba banayin wannan wasan yaran, yanzu gashi sai qareman kallo ake ana gulma na in aka cinye maki Ni shikkenan kin huta ai" stakin ya kuma ka yana qara murtuqe fuskan sa, dan karma a raina sa gashi wai zai yi gasa da mace qanwar bayan sa kayan reni "gaskiya Ni Umma baki kyauta mun ba" ya faɗa yana tura baki kaman yana gaban Umman tasa..
Dayawan mutane a wajan kallonsu ya koma kan Amjad, sakamakon ba kowa ne ya san sa ba, ko karatu ba'a garin yayi ba in ba dai kana shiga kasuwa da Sa'a ba tom sannan ne zaka iya cewa ka taɓa ganin sa, ƴammatayen wajen duk sun masa quri da ido.
Duk abun da ake ciki Gimbiya bata da labari kuma bata sani ba dalilin ta faɗa tunanin yacce zata damu ta kada su a agasan nan ko Papan ta zai bar batun auren ta yanzu, taɓatan da jakadiya tayi shi ya dawo da ita daga tunanin da ta faɗa, tana ɗaga ido Carab sai a kan fuskan Amjad, qare masa kallo tayi kamun ta taɓe baki "wannan mutum har mutum amma sakali sakalci da girman sa harda tura baki kaman mace a haka ya shiga gasan Gashi dai da zubin jarumai" bayan ta gama zancen ta a ranta taɓe baki ta kuma yi.
Jakadiya dake gefen ta ne ta murmusa tace "Allah ja kwanan Gimbiyar mu ƳAR SARKI KUMA JIKAN SARKI SANNAN DAI MATAN SARKI, wannan yarima namu na gobe yayi qoqari tunda har idon Gimbiyar mu ya sauqa a kansa." Girgiza kai Gimbiya tayi wanda hakan ya bawa jakadiya daman fahimtar Yaren uwargijiyan nata abinda take nufi.
Wasu ƴammataye can gefe ke surutu "ke fa mastala na dake rahama rashin hankali wallahi, bar batun hassada da kike wa Gimbiya yanxu ace kece a matakin datake ga wannan kyakkyawan halittar na tabbata bazakice haka ba, nifa wallahi da ace nice wallahil Azeem da kaina zan buɗe masa fuskan nawa, ai dai duk kyawun ta ba lallai ta kamosa ba" wacce aka qira da rahama ne tayi shewa hehehe! Lallai ma ita fa ƳAR SARKI CE ina zaki haɗa kyawun ta da namiji kede faɗi gskyh yamaki shiyasa kikace haka, murmushi tayi "rahama kenan, Allah dai ya bawa mai rabo Sa'a namu kallo ne amma duk da haka nide inaso yayi nasara" da Ameen sauran qawayen nata suka amsa....

Sarkin shela ne ya buqaci ganin Gimbiya da kuma ɗaya daga cikin masu gwabzawa da ita, Sarkin shela bai gama rufe bakinsa ba, anwar ya miqe ya fito don baiso Amjad ya fara ballema yaci dan tun da ya ɗaqa ido ya gansa yaji kishi ya rufe sa.
Bayan ya shiga Filin ya tsaya, Gimbiya ce ta shigo filin itama cikin takun ta mai ɗaukan hankali, tun da ta tashi har ta shiga idon Amjad da Anwar na kanta haka ma ɗokacin jama'an wannan fili duk kowa kallonta yake, Amjad ne ya kauda kai "yanxu in ba Umma ba wannan qaramar yarinya zan aura" stakin ya kuma ja ya kauda kai.
Anwar da Gimbiya Mehwish sun fara fafatawa, Faɗa Anwar keyi da gaske cikin qwarewa da kuma burgewa, abunda ya sanya har Gimbiya ta murmusa ganin Anwar faɗa yake bilhaqqi da gaske kaman ba wanda zai janye abun fuskan ta ba, duk ta inda ya juya in ya kawo sara tarewa take, ko halaman kai masa sara ba tayi ba kawai kare nasa harin take ba ta mai da martani ba. Tana yi tana kallon idon sa duk wani mostin sa da yanayin kai saran sa ta haddace,
Wasan da suke ya stuma jama'an wannan fili dan ba abinda kakeji sai ihu ana kiran sunan "GIMBIYA" da kuma "ANWAR" kaman ance ya kalli idon Gimbiyar karaf yasa idonsa cikin nata wanda hakan ya basu daman kallon juna sosai kallon da ya janyo wa Anwar shagala da kusan mancewa a filin gasa yake, Murmushin gefen baki Gimbiya tayi wanda rashin ganin fuskanta baze hanaka gane hakan ba ganin kwayar idonta kaɗai ya isa sanya mutum hasaso irin kyawun da murmushin ya mata!! lumshe ido tayi ta kuma buɗewa kaman mai jin bacci g kuma wannan haɗaɗɗen murmushi akan fuskan nata abun da bai wuce seconds ba ya gigita Anwar, yana ganin abun da tai da ido ya susuce be ankare ba ya jishi aqasa.(subhanallahi sannu!!)

𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 " 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖"𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 ba abun da kakeji yake tashi a wajan dai sunan GIMBIYA mutane na ihu suna qira.
Amjad dake zaune taɓe baki yayi ya kau da kai. Runste ido Anwar yayi, yana jin kaman ya buɗe qasa ya shiga dan kunyan da yaji ys lulluɓe sa!
Chapter 18 · 0% Book details