← Book details Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 61

Sashe 26

Yar Sarki Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan shigan ta ɗakin ta, kwanciya tayi a kan qayataccen gadon ta da yasha shumfuɗi, a kwancen ta rage kayakin jikin ta a haka har bacci yayi awon gaba da ita.
Itace bata farka ba sai daf ana qiran Sallahn azahar, jin kanta na ciwo sakamakon kukan da tayi ɗazu sai ta nemi magani tasha taje ta wasta ruwa ta ɗauro alwala ta tada Sallah.
Ta idar da sallah ta shirya cikin riga da skirt ruwan kwai, irin kayan ƴan India. Bata sa ko ɗan kwali ba ta ɗau alkyabban ta ta sanya ta fice a ɗakin, a palourn ta tarar da Laure na goge goge, goggoji da ke jera abinci a dining en dake sashen ta takalla tace "ina jakadiya? Goggoji ta juyo har ta durqusa dan bata amsa sai ga jakadiya ta shigo, tana magana a waya. Ganin Gimbiya tsaye ba tare da ta kammala wayan ba ta kashe, durqusawa tayi Allah ja kwanan uwar ɗakina mai kike buqata? Gimbiya batace qala ba ta nufi hanyan qofan baya daga nan sashen ta wanda zai sada ta da lambun dake gidan sarautan nasu.
Ganin haka jakadiya ta yi sauri tabi bayanta, kamun Gimbiya ta isa har jakadiyan ta shumfiɗa mata darduman da zata zauna ta wuce cikin part en Gimbiyan da sauri. Gimbiya zama tayi ta yaye alkyabban ta dan tasha iskan dake kaɗawa a lambun mai daɗin gaske, jakadiyan ce ta kuma dawowa ɗauke da tray dake a shaqe da kayan marmari ta zo ta ajiye a gaban Gimbiya, kanta aqasa tace "Allah baki tsawon rai uwar ɗakina, shikkenan ko da wani abun da kike buqata? Sai yanzu Gimbiya ta buɗe baki tayi magana.
Shikkenan maimuna kina yin abu ne a cikin gidan?
Saurin girgiza kai jakadiya tayi a'a bana komi ranki shidaɗe uwar ɗaki na, okay kije ki gyara mun ɗaki sai kizo and bayan ke banson kowa ya shiganmun ɗaki bare har yace zai gyara mun toilet nasha faɗa maki amma inaga kina barin sauran yaran na shiga mun ɗaki. Ki gafarceni uwar ɗaki na, ban sanya kowa gyaran ɗakin ki ba sai dai jiya da dare da naje ɓangaren su Umma dan dubo jikin ta bansan ko akwai wanda ya shiga ba.
Gimbiya tace yayi kyau amma dai a kula dan banason qazanta, and ya jikin Umman? Fatan da sauqi?
Da murmushi Gimbiya tace eh uwar ɗaki na jikin da sauqi sosai ma, Insha Allahu zuwa wani sati inaji zata dawo bakin aikin ta ma. Allah kaimu ya qara sauqi ko Umma ta dawo, zata kula da sauran ɓangarorin da masu ayyukan gida amma sashe na ke zaki cigaba da kula dashi. Inshà Allahu uwar ɗakina Allah ja kwana, ta tashi ta juya dan komawa ciki ta gyarawa Gimbiya ɗakin nata.
Gimbiya wayan ta tajawo ta kunna data dan duba class da suke yi a online, tana yin master's a ɓangaren Islamic, Amma online master's. Tana dudduba class en tana shan kankana, sanda suka yi almost 1 hour suna class kamun aka gama, ganin ya qare class en yastine baki tayi ta kashe datan tayi jifa da wayan tana miqa, idon ta na sauqa akan apple da ke cikin bowl en kayan fruit en sai shi ya faɗo mata a rai, tun da ya tafi basu yi magana ba koya ya isa gida bata sani ba. Lumshe ido tayi ta sa hannu ta ɗau apple en tana ci a hankali, Sallaman jakadiya ne ya dawo da ita hayyacin ta.
Amsa Sallaman tayi, jakadiyan ta durqusa ɗan gefen ta kaɗan, nuni ta mata da kan darduman da nufin ta zauna, ba musu jakadiyan ta masto ta zauna tana "Barka da hutawa Uwar ɗakina" gyaɗa kai kawai Gimbiya tayi batace komai ba sanda ta ɗan ci kusan rabin apple en kamun ta ajiye ta juyo tana fuskantar jakadiyan, magana nakeso muyi dake shawara nakeso zaki ban, jakadiya tace "ina sauraranki uwar ɗaki na , nan dai suka tattauna......

Sai can yamma lis kusan magrib Abba da Amjad suka kamo hanyan dawowa gida, suna tafiya suna hira har suka iso gida. Da farin cikin ganin mijin nata da tilon ɗan nata ta tarbesu tana masu sannu da gajiya, ledan hannun Amjad ta amsa ta shumfiɗa masu tabarma, ruwan sha ta kawo masu suka sha ta miqo masu wani ruwan a buta, alwala suka yi suka fita dan zuwa masallaci ita kuma Umma ta shumfiɗa darduma a kan tabarman ta tada Sallah, ba ita ta tashi ba sanda tayi har da magrib.
Ko da ta idar naɗe darduman tayi ta maida, jera masu kwanukan abinci da komi tayi a babban taburman da ta shumfiɗa ta zauna tana jan carbi tana jiran dawowan su masallaci.
Umma na zaune na jan carbi can sai ta jiyo sallaman su suna shigowa gidan, amsawa tayi ta miqe ta maida carbin da hijab ɗaki ta dawo ta samu har sun zauna Amjad ya zuba masu abincin, tuwon shinkafa Umma ta masu da miyan ɗanyen kifi wanda yasha haɗi gashi Umma expert ce a iya girki.
Bismillah suka yi suka fara cin abincin, Amjad loma ɗaya biyu yayi ya cire hannu, kallon sa Abba yayi "yau kuma rashin cin abincin ya mosta kenan" Abba ya faɗa yana cigaba da cin abincin sa.
Umma ce ta kallesa tace "wai har ka ɗanɗano girkin surkar tawa yafi nawa daɗi ko kaqi cin abinci gaba ɗaya yau, nayi favorite miyan ka kuma kaci sau biyu kace ka qoshi tabbas zan maka ɗure Jarumin Umma. Murmushi yayi ba haka bafa Umma ta, Tom Jarumin Umma in ba haka ba yaya ne? Kaqi cin abincin Ummanka meeyasa? Hannu yasa ya fara cin kifin dan dama yana daga cikin abinda yake so ɗanyen kifi barinma dahuwan Umman sa.
Sanda suka gama cin abincin duk suka wanke hannu ya taya Umman tasa tattare wajan, ya kai mata kwanukan kitchen.
Dawowa yayi suka kama fira da iyayen sa
Abba ne ya dube sa yace "yauwá jarumin Umma nasan itakam ka faɗa mata ya kuka yi da mai martaba saura ni a faɗamun. Umma ta ɗan dara wato dai anfaɗawa kishiyanka, Tom dai yana dawowa yace zashi wajan baban sa ko abun karyawa na ma baici ba, dan haka daga ni har kai muna sauran sa ya faɗa mana ya suka yi dan nikam ma Allah ya gani yaron nan ya ɗagan hankali yacce na gansa ɗazu, kuma gashi sai yaqi cin abun karyawa na.
Murmushin yayi ya sa hannun sa ya kama kunnen sa Ummata a yafemun na ɗaga maki hankali, komai lafiya Alhamdulillahi sai abinda baza'a rasa ba. Abba yace "to muna sauraran ka mene baza'a rasan ba". Nan take ya faɗa masu yacce suka yi da mai martaba da kuma baqin da ya haɗu dasu acan, da maganan kyauta da maganan aiki da suke son yayi dasu komai duk ya faɗa masu.
Abba ne ya nisa yace "yanzu yaya ake ciki jarumin Umma me mai martaban yace maka akan maganan nasu?"
Abba ba abinda yace fa sai kawai wai nazo nayi shawara da Iyaye na akan aikin. Umma tace "to jarumin Umma karatun da kayi ina fannin likitanci me? Mai ya haɗa likita da aikin soja?
Murmusawa yayi, Umma ta sun san da hakan duka, amma Dukansu huɗun shuwagabannin sojojin ƙasashen su ne, Kinga kenan hakan ba matsala bane.
Ajiyan zuciya Umma ta sauqe tayi shiru ta rasa mai ma zata ce, Abba ne yace yanzu Tom kai ya kake gani maganan kyautan kuma mai Sarki yace?
Abba maganan kyauta za'a karɓa abinda nake faɗa maku yanzu haka insha Allahu gobe anbamu komi sai hidiman kuma sai biki yazo. Tunda dai duka kuma kun rasa abun cewa shikkenan Abba karku damu kanku daganan har zuwa randa muka yanke shawara sunce suna maraba da Ni. Sai kuma abinda ba za'a rasa ba nan ya kuma kwashe yacce suka yi da Gimbiya da yanayin jikin Sarauniyan da kuma alqawarin da ya ɗauka mata. Sai hawaye kawai Umma ta fara ta kasa cewa komi dan tabbas taji tausayin matar sannan ta tausaya wa Gimbiya. Abba ma bai ce komai ba, wanda hakan ke masa nuni da iyayen nasa na goyon bayan abun da ya yanke.
Umma tace "Allah bada Sa'a jarumin, Umma, Allah sa a dace, tabbas zan so haka kuma zanyi alfahari da hakan in har sanadinka Allah ya bawa Sarauniya lafiya, wannan na tabbata zai sa Gimbiya ta soka da ga mutuncinka fiye da tunaninka a rayuwa, ina maka fatan nasara akoda yaushe Jarumin Umma.
Abba ma kusan abun da Umma ya faɗa hakan ya faɗa, dan tabbas ya jima da jin labarin rashin lafiyar Sarauniyar sai dai bai ɗauka har yanzu jikin nata ba, "Allah bada Sa'a jarumin Umma, In yayi akwai rubutun da zan yi da kuma wani maganin anan zaka kai masu su fara aiki dashi kamun ka shiga jeji ka dubo maganin tunda kaga yanayin jikin fatan mu dai Allah yasa adace"
Da Ameen suka amsa shi da Umman sa. Nan dai hiran nasu bai yi tsayi ba ya tashi yace zai je ya kwanta dan yana son ya sammaka a zuwa kai masu maganin gobe sai ya shige jeji. Rakasa ɗakin nasa suka yi kaman koda yaushe Umman sa ta masa addu'a suka ja masa qofa suka fita.
(wolleh iyayen sannan na mugun qaunar sa da sonsa).

_____________
Chapter 26 · 0% Book details