← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 170

Sashe 82

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A gurin ya tsaya yana kallon motar su Jabir har ya ja suka wuce, sannan ya faka tasa gefen titin. Daman fitowa kawai yayi daga gidan ba dan yana da gurin zuwa ba. Sosai ya zurfafa a tunani yana son gano inda ya san Waira ko ya taba ganinta amman ya kasa, kallon da yayi mata a mota ma yanzu ya ki ya fita idonsa, sai da yayi da gaske sannan ya iya focusing akan abun da ya kamata ace shi ne a gabansa ba tunanin kyaun wata yarinyar da bata san da zamansa ba, kuma karamar yarinyar kanwar kanwarsa ba ma babbar mace ba. Ac motar ya kara sannan ya dauki wayarsa dake aje a inda ya saba aje ya yi dialing number Ammynsa. Kiran farko bata daga ba haka ma na biyu da na uku sai da yayi mata na hudu sannan ta daga.

“Ameer my son how are you?”

“I'm good Ammy”

Ya kai hannu ya rage ac jin kamar baya bukatarshi kuma.

“Ammy wani abu nake son na tambayeki, i don't want you to lie to me, kin san na yarda da ke, karki rushe wanann amince da ke tsakaninmu, kuma karki dubi Daddy ko ni ki fada min abun da ba gaskiya ba please..”

“Mene ne haka zaka tambaye ni Ameer?”

“Daddy ya kira ki?”

Ta yi jim kamar mai son ya canja mata tambaya.

“Eh ya kirani”

“I know na tambaya ne saboda na tabbatar zaki fada min gaskiya ko akasin haka, seriously bana son ki fada min abun da ba gaskiya, idan kika min haka zai yi wuya mu sake shiri da ke, you know how much i love you ko? Kin san ke na kallo kamar uwata right”

“Ni din ma uwarka ce Ameer, tambaye ni duk abin da kake so na maka alkawarin zan fada maka gaskiya”

“Akwai wata mata da na hadu da ita dazun, ta fada min maganar ban da da maganarta ba sai dai kuma sunanki da ta ambata ta ce na aje na tambaye ki idan kina raye ya saka na ji kamar akwai kamshin gaskiya a ciki....”

Sai da ya fara bata labarin abun da ya faru tsakaninsa da Maleek duk kuwa da ya san Daddy ya fada mata komai, sannan ya dora da abun da ya shiga tsakaninsa da Nimra zuwa yau da Ummi ta fada masa wannan maganar.

“Me kika sani game da ita?”

“Ameer”

Ta kira sannanshi a a hankali, sai ya amsa yana duban agogon hannunsa.

“A ina kake?”

“Ina kan hanya”

“Tuki kake?”

“Aa”

Ya amsa tare da bude motar ya fito.

“A tsaye kake”

“Eh yanzu na fito mota”

“Nemi guri ka zauna”

Ya koma cikin motar ya maida gambun ya rufe gabansa na faduwa.

“Akwai wani makami ko wani abun da zaka iya yi ma kanka rauni a kusa da kai?”

Ya juya ya kalli wukar da ya dauko daga restaurant, wadda ya firgita Humaira da ita.

“Eh”

“Matsar da shi”

Ya kai hannu ya dauki wukar ya bude motar ya fita ya jefar da ita sannan ya dawo cikin motar ta saka wayar hands-free ya lakata a mazaunin ta dake cikin motar.

“Done”

“Yarona akwai ruwa kusa da kai”

“Akwai ruwa a motar Ammy just go on”

“Matar da ta fada maka haka fara ce?”

“Fara ce sosai”

“Sunanta Zahra right?”

“Ban san asalin sunanta ba, amman dai Ummi Nimra take kiranta”

“Ita da mijinta yan asalin garin Kano ne?”

“Nimra ta taba fada min haka”

“Wani labari zan baka da ya shafi rayuwata, kuma ya gurbata zamana da mahaifika, ya nisanta ni da kai”

Ya gyara zamansa a cikin motar.

“Ina saurarenki”

“Mahaifinka ya taba baka labarin shekarun da muka dauka ba mu haihu ba?”

“Ya fada min”

“Amman be fada maka miyasa ya rabu da ni ba?”

“Har yau be fada min ba”

“Ameer na kwashe shekarar da ta kusa goma a tare da Mr Bashir, Allah be bani haihuwa ba, na yi iya yadda zan iya ta bangaren asibiti na da hausa amman Allah be bani ba, sai a yanzu na gane ashe ba a rubuto ni cikin wadanda za a rabawa kyautar yaya a duniya ba, yan'uwan mijina suka tsangwame ni, ni ma kuma na matsawa kaina, idan na ga yaya kamar na sace nake ji, ko kukan jariri naji sai hankali ya tashi, Ameer akwai kunci da damuwa matuka a zuciyar uwar da bata taba amsa sunan uwa a bakin jininta ba, ni kadai na san irin kuncin da mace take ji a lokacin da take sha'awar dandana azabar zafin nakuda da dawainiyar daukar ciki. Hankali ya tashi matuka a lokacin da mahaifinka ya gabatar min da magana aure, ina ta jin tsoron kar wata ta zo ta haihu ya juya min baya, duk kuwa da kasancewar ban ga alamar haka a tare da shi ba, a lokacin idan na hana shi aure ban masa adalci ba, kuma yan'uwansa ba za su kyale ba, ina ji ina gani aka daura masa aure sai zuciyata ta kasa hakuri har na fara bin bokaye, duk mace da ta shigo sai a fitine ta ta kasa zaman auren, a haka har ya auri mace hudu dayar har bari ta yi amman ban barta ta zauna ba, sabida jna kaunar mijina sosai. Daga baya na samu wani likita ya ba mu shawarwari akan hanyoyin da zamu bi mu samu haihuwa, a ciki akwai dashen kwan haihuwar, bayan ta tabbatar mana da cewar ni da shi duk bama da matsala zamu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya so, sai na kasa hakuri shi kuma ya ki ya amince da zancen dashen kwan da aka fada mana, yace ya fi son haihuwar ta zo daga Allah kai tsaye”

Ta tsinke zancen da take ta dauki ruwan dake kusa da ita ta sha. Sannan ta cigaba.
Chapter 82 · 0% Book details