← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 170

Sashe 108

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aa nan din ma gidanku ne, sai dai ka yi kora ba wai a koreka ba, kawai ina damuwa da Waira ne ka yi hakuri”

Ba ce mata komai ba ya juya ya fice daga falon, windows ta nufa tana leken motarta, ta saka hannu ta rike curtains din idonta na bin motar da kallo har sai da har ya bar gurin da idonta suke iya gani. Fitar Ameer da minti biyar Maleek ya shigo falon ta kofar da Ummi ta fito dazun, wato kofar dake sada mutum da part din Abiey.

“Ya fa tafi da ita”

Ummi ta saki curtains din ta juyo ta kalleshi.

“Miye damuwarka da hakan ne Maleek?”

“Amman dai kin san abun da ya faru da Nimra”

“Abun da ya faru da Nimra kamar ya? Fyade yayi mata? Soyayya ce kawai shi ma kuma na tabbatar da ace ya san haka zai faru da ba zai aikata ba, kuma ita ma hanyar mutuwarta ce a haka, ko da ba Ameer ba dole wani zai yi sanadiyar bugawar zuciyarta”

“Idan kuma fansa ya zo dauka fa, zai iya amfani da Waira sabo...”

Wani irin kallo Ummi ta watsa masa da ya saka shi kasa karasa maganar.

“Fansa? Ka taba ganin ďan da ke daukar fansa a gurin uwar ta dauki cikinsa ta yi nakudarsa ta haife shi? Ka taba gani? Me yasa zuciyarka bata raya alheri akan ďa?”

Maleek ya gyara tsayuwarsa a yanzu ya san duk wani abu da zai fadawa Ummi ba lallai ne ta fahimta ba, amman shi a baibai yake kallon abin domin ya fi kowa sanin waye Ameer, ba kamar ita da a yanzu take saninsa ba. Ummi ta nuna shi da yatsa.

“Ka cire idonka akan Ameer, ka kawar da kanka ga barin kallon alakar dake shiga tsakaninsa da Waira, ina son farincikin kowa a cikinku, kuma ina iya karantar abun da ke idon Ameer, na da yakini da tabbacin ba zai taba cutar da Waira ba, Ameer ya canja a yanzu sanin da kai masa a ad ba shi ba ne, dan Allah kar ka bari shaidan yayi tasiri a zuciyarka ya dasa maka kiyayyar dan'uwanka”

“Ni bana kiyayya da Ameer, kawai ina fadar halinsa ne, kuma ke nake tausayi idan Ameer ya aikata abun da baki yi tsammani ba zaki fi kowa shiga damuwa da bakinciki”

“Ba zai aikata ba ina baka wannan tabbacin, ka saka ranka a inuwa domin a yanzu zai dawo da zama a gidan nan ne, dole ne ka dauke idonka daga alakarsa da Waira wata kila alakar da kake tsammani ba itace a gabansa ba”

Ya hade yawu har ta yi kamar zata wuce sai kuma ta dawo ta kalleshi

“And bari na maka wani gargadi wannan ya zama karo na karshe da zaka aibatanta Ameer a gaban mahaifinka, kalaman da ba su dace ba, kokarin nuna yana son bata tarbiya wasu, duk bana so, uwa bata son a aibata ďanta, zaman a gidan nan ina son na ba shi farincikin da ya rasa ne, na kusanto da shi a kusa da ni, idan baka taimaka min na samu haka ba, to karka yi kokarin bata min rai”

Tana gama fadar haka ta nufi hanyar stairs, Maleek ya runtse idonsa sosai har sai da ta haye sama, sannan ya bude idon, ya san ba zata fahimci abun da yake kokarin nuna mata ba, shi dai kawai yana tsoron kar Ameer ya lalata rayuwar Waira ne, hakan zai kara jefa Ummi a damuwa, amman tun da bata gani zai dauke ido akansu kamar yadda ta fada, daman can ma miyasa ya kula? Me yasa ma ya tsaya magana da Ameer din? Why ya shiga part din Abiey a fusace yana fada akan Ameer ya sumbanci Waira? Ya rike hannunta? Miye damuwarsa ma da haka. Daga gurin ne ya daukarwa kansa alkawarin ko Ameer zai kwantar da Waira a gabansa ya yanka ta da wuka ba zai nuna ya gani ba ma balle har yayi magana, ko da Ameer zai nemi yin lalata da Waira a gabansa idonsa ba zai ce uffan ba. Bayan ya daukarwa kansa alkawarin ne ya nufi kitchen a fushin zuciya da bacin rai da be san na minene ba, ya bude fridge ya dauko ruwa ya nufi gurin da aka aje cups ya daga container din ya dauko glass cup ya aje ya zuba ruwan ya dauka ya sha, ya sake zuba wasu ya sha har sau uku still zuciyarsa bata sauka a daga hawan da ta yi ba.

“You should act mature mana Maleek ina ruwanka a ciki? Ido zan saka musu ai kamar yadda ta nema ni na san Ameer sai ya saka ki zubar da hawaye Ummi”

Ya daki gorar ruwan da karfi har sai da ta fadi kasa, magana yake da kansa cikin wani irin fushi da zafi rai da fushin zuciya marar misaltuwa.

AMEER POV.

Yana tukin yana kallon Waira dake gefensa tana share kwalla, be ce mata komai ba tun da suka shigo motar ita ma bata ce masa ba ko inda yake bata kalla ba, gashi ta dan bata fuska alamar fushi take, fushin da be san na minene ba. Rage wutar motar yayi ya faka gefen titi ya kashe motar yayi relaxing akan kujera yana kallon dayan gefen titin. Hakan ya saka ta juyo ta kalleshi sai ta ga ba ita yake kallo ba.

“Me yasa muka tsaya a nan?”

Ta tambaya a cikin wani yanayi mai kama da shagwaba da bata ma san tana yi ba. a juyo a hankali ya kalleta.

“Kuka na ga kina yi, shiyasa na tsaya har ki gama kukan, idan kuma bakin zon zuwa ne sai na maida ke, ni ban shirya tarbar wani karin bakincikin akan wanda nake ciki ba, bana son kukan kowa akaina a yanzu”

“Ba saboda kai nake kuka ba”

“Saboda wa?”

Ta yi shiru, sai ya kai hannu ya riko fuskarta ya juyo da ita yadda zata fuskance shi da kyau.

“Waira saboda na katse miki sarka ne? Ko saboda na yi magana da Maleek”

“Duka ne, ina son abun da Sulem ya ba ni, kuma ni bana son kana fada da Ya Maleek bana so ko kadan”

“Amman kina kallo a gaban idonki, shi ya fara fada min maganar banza, and ni bani da wani kuduri na lalataki ko rayuwarki, Allah ya sani ba ni da wani mummunar manufa akanki”

“Minene mummunar manufa?”

Ya kawar da kai.

“Manta kawai”

Sai kuma ya juyo ya kalleta.

“Zoben ki kuma zan siya miki wani bana son an sake ganinki da duk wani abun da ya shafi wani, bana son wata mu'amala tsakaninki da kowa, ba saboda Ummi kawai na dawo gidan nan ba, har saboda ke, so please don disappointed me”

Ita dai kallonsa kawai take ba dan ta fahimci mnufar zancensa ba.

“Amman Sulem shi ba a gidan yake ba, sau biyu kawai ya taba zuwa, kuma ya ba ni kyauta ne”

“Miye alakarki da shi?”

Ta yi shiru tana murza yatsun hannunta, so take ta tuna alakar dake tsakaninsa da ita.

“Shi ne wanda yake min sauki lokacin da ka barni a daji nan, shi yana so na baya min kamar yadda sauran mutanen suke min ba, kuma yana lalabani yana ba ni abubuwa kuma yana min magana mai dadi”

Ya sauke numfashi tare da kai hannu ya kunna motar.

“Ba dan'uwanki ba ne, baki da alaka da shi, Waira baki da alaka da kowa a yanzu sai ni”

“Kai ma ba dan'uwana ba ne!”

A wani irin dum maganar ta fado masa a kune ta fara rawa a kirjinsa. Ya dan karkato kamar zai kalleta sai kuma ya fasa ya cigaba da tukin motar.

“Ni ina son Sulem, Sulem ba ya min fada”

“Miye abun fada a cikin magana ta? Gaskiya na fada ai, waye silar zuwanki garin nan ba ni ba?”

“Amman ai a daji ka bar ni, baka taimaka min ba lokacin da maciji ya cije ni”

“That's was my mistakes, amman na taimake ki mana, na dauko ki saka ki a motar Nimra”

“Baka yi ba, Sulem ne yayi?”

“To a ina kika ga Sulem din?”

“Ni ban sani ba, amman shi na gani a gidan Hospital kuma shi ne yake min da sauki ba kamar saura ba”

“Shi fa likita ne kawai, amman ba shi yaje daji ya dauko ki ba, ke dai kawai kin farka kin ganki a asibiti ne, ya taimake ki ne saboda an ba shi kudi ba free yayi miki ba?”

“Ba a bashi kudi ba”

“Waya fada miki?”

“Na gani ai, babu wanda ya bashi kudi, kuma da iyayensa suka masa fada sai ya dauke ni ya kai ji wani gurin muka kwana a can, be bar ni ni kadai ba, kuma da masu bakin kaya police aka ce su kawo ni a nan be min fada ba, ni ina son shi”

Ya daki sitiyarin motar da karfi

“Haba Waira ina da fushi sosai, karki saka raina ya bace mana, don't make me angry, kar na fadi wata maganar da zata saka ranki ya bace har Maleek ya yi kwatance da haka”

“Toh ka daina min fada, gashi ka daki mota next ni zaka daka kamar Ya Maleek”

Ya amsa da sauri.

“God forbid ni ba zan taba dukanki ba, ba wannan ranar fada kuma na daina, zan siya miki sarka mai tsada sosai ki saka a wuyanki ba zobe ba, ba a saka zobe a wuya”

“Ni Sulem ya saka min ina so”

“Wannan Sulem din dan'iska ne”

Sai ta ji kamar ta fashe da kuka saboda ya zagi Sulem, ita duk mutanen da take kauna bata son a taɓa su.

‘Idan mutum yana kyautata miki shikenan ya zama masoyinki? Zan rufe idonki da kyautata har sai kin manta kowa a rayuwarki’

Ya saka a ransa sannan ya kalleta yana murmushin ya ce

“Yi hakuri, Sulem mutumen kirki ne, yanzu idan mun koma saka miki zobenki a wuya shikenan?”

Ta daga masa kai.

“Okay Smile”
Chapter 108 · 0% Book details