Sashe 57
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ummi dakinta ta fara dubawa sai ta tarar har Dr Zainab ta yi bachi, gudun kar ta yi motsi mai karfi ta tasheta ya saka ta shiga a hankali ta bude bathroom ta yi wanka tare da wanke baki sannan ta fito ta dauko kayan bachinta ta saka ta fito tana ta kamshin turare. Dakin Namra ta fara budewa ta leka saita same ta ita kadai tana bachi, daman can ta san Namra ba zata kwana da kowa a dakinta ba, idan har wani zai kwana akan gado daya da ita kara ta kwana akan kujera, ita dai bata son ta motsa ta ji wani a kusa da ita. She has so many rules and regulations na banza da take sakawa kanta just to be unique. Ac dakin Ummi ta rage ta ya janyo mata kofar ta maida ita a yadda take. Sannan ta nufi dakin Nimra abun ka da mai son jama'a sai ta same ta ita da Juwairiyyya suna kwance a gado daya, sai dai da alama Nimra bata shiryawa bachi ba, domin wayarta ta fado kasa hannunta kuma yana lilo a gefen gadon ga wutar dakin a kunne ba kamar Nimra da ta kashe nata ba. Ummi ta karasa ta duka ta dauki wayar sai ta ga missed calls biyu daga heart emoji guda uku, ga kuma wani sako a saman screen din wayar.
(𝑫𝒐𝒏'𝒕 𝒕𝒆𝒍𝒍 𝒎𝒆 𝒌𝒊𝒏 𝒚𝒊 𝒃𝒂𝒄𝒉𝒊 𝒕𝒖𝒏 𝒚𝒂𝒏𝒛𝒖 𝒌𝒊𝒏 𝒃𝒂𝒓 𝒏𝒊 𝒅𝒂 𝒌𝒆𝒘𝒂𝒓𝒌𝒊, 𝒈𝒂𝒏𝒊 𝒂 𝒏𝒂𝒏 𝒔𝒂𝒊 𝒋𝒖𝒚𝒊 𝒏𝒂𝒌𝒆 𝒂 𝒃𝒆𝒅 𝒊𝒏𝒂 𝒔𝒉𝒂𝒌𝒂𝒓 𝒌𝒂𝒎𝒔𝒉𝒊𝒏 𝒕𝒖𝒓𝒂𝒓𝒆𝒏𝒌𝒊, 𝒃𝒚 𝒕𝒉𝒆 𝒘𝒂𝒚 𝒌𝒊 𝒔𝒂𝒏 𝒊𝒓𝒊𝒏 𝒌𝒂𝒓𝒚𝒂𝒓 𝒅𝒂 𝒛𝒂𝒌𝒊 𝒚𝒊 𝒈𝒐𝒃𝒆 𝒎𝒖 𝒉𝒂𝒅𝒖 𝒊 𝒂𝒍𝒓𝒆𝒂𝒅𝒚 𝒎𝒊𝒔𝒔 𝒚𝒐𝒖, 𝒊 𝒄𝒂𝒏'𝒕 𝒘𝒂𝒊𝒕 𝒇𝒐𝒓 𝒚𝒐𝒖𝒓 𝒉𝒖𝒈 𝒂𝒏𝒅 𝒌𝒊𝒔𝒔 𝒌𝒊𝒏 𝒔𝒂𝒏 𝒃𝒂𝒏𝒂 𝒈𝒂𝒋𝒊𝒚𝒂 𝒅𝒂 𝒌𝒆 𝒊 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒚𝒐𝒖 𝒔𝒘𝒆𝒆𝒕 𝒅𝒓𝒆𝒂𝒎)
Wani irin tashin hankali da fargaba irin na uwa mai ƴaƴa mata ne ya bayyana a fuskar Ummi, jikinta ya dauki rawa as well as zuciyarta dake bugawa, she can't believe ta ga sakon nan a wayar ƴarta ƴar ma Nimra wacce zata rantse idan aka saka mata yatsa a baki ba zata ciza ba, a cikin sakon babu abun da ya fi daga mata hankali kamar inda yake cewa ta san kalar karyar da zata yi su hadu? Su hadu a ina? Ina suke haduwa? Why not ya zo gidansu idan sonta yake? Wani ta hadu da shi yake mata wayo haka? The hug and kiss part ma abun tashin hankaline, Nimra zata iya rumgumar wanda ba mijinta ba har ta sumbance shi? Bayan wannan sai kuma me? Ummi ta kalli Nimra dake sharar bachinta hankalin kwance bata san abun da ke faruwa ba. A hankali Ummi ta aje wayar a gefen gadon ta juya ta nufi switch din dakin ta kashe sannan taja kofar a hankali ta fice, gaba daya jikinta yayi sanyi, tunani kala kala ya fara zuwa mata har da wanda be kamata ta yi ba a lokacin, tafiya kawai take tana saukowa basa not knowing downstairs take saukowa har sai da ta ji Waira kira sunanta.
“Ummi ta shanye tea”
Ta kalli saitin inda take ta sauke wani uban ajiyar zuciyata ta kai hannu ta dafa zuciyarta, tunanin mai kokarin gurbata mata tarbiya ƴa take, kawa ta hadu ita marar tarbiya ko kuma saurayi? Amman idan kawace ya akayi bata san da ita ba a matsayinta na uwarta? Sai a yanzu take gane maganar da hawasa suke cewa mai ƴaƴa mata hannunsa a kirji yake har sai ya aurar da su, idan kuma ya aurar ba ya rufe ƙofa. Ta bawa Yayanta yarda 100% saboda tarbiyar da take ganin ta yi musu hakan ya saka wanin abun bata damuwa ta zafafa bincike kwakwaf akansu ba.
“Waira zo muje ki kwanta dare yayi sosai”
Waira ta taso ta nufo inda Ummi take sai Ummi ta rike hannunta suka haura sama, ta shiga da ita dakinta ta bude wardrobe ta dauko mata kayan bachi ta aje mata akan gado.
“Shiga ki yi wanka ki yi brush zan jira ki a nan”
“Tohm”
Ta nufi bandakin, Ummi ta zauna baki gado tana ta tunani kala kala, for how long alakarsu take da wannan mutumen waye ma shi? Mace ne ko kuma namiji, domin a yanzu a wane hali da mata suke neman mata yan'uwansu, maza ma su nemi maza yan'uwansu, miyasa ko da rana ďaya bata gabatar mata da shi a matsayin saurayinta ko wanda take son aure ba? Ita dai saninta a yanzu babu mai zuwa zance gurin Nimra kara ma can da ana zo jefi jefi amman ban da yanzu, balle ta yi zargi wani ne a cikin masu zuwan. Bata son ta munana mata zato hakan ya saka ta fara kokarin yakar zuciyarta ta kawar da abun a ranta. Waira ta yi wanka ta yi brush kamar yadda Ummi ta koya mata idan zata kwanta sannan ta fito ta saka kayan bachin Ummi ta nuna mata turare, sai ta nufi inda turaren yake ta dauka ta fesa a jikinta.
“Baby Waira kin san miyasa mai miki lessons be zo ba yau?”
“Aa no aa”
Ta fada har sau uku a kokarinta na bin umarnin Ummi na amsa mata da baki ba da kai ba.
“Be fada miki komai ba a jiya yace ko ba zai samu zuwa yau ba?”
“No be fada mata”
“Mini”
Ummi ta gyara mata
“Mini komai ba”
“To zo ki kwanta”
Ta hau ssman gadon ta kwanta gefe nesa da inda Yesmin take kwance, sai Ummi ta bude wani karamin kwando ta dauko safa ta saka mata a kafa.
“Kin gani da ace addininmu kike yi sai na ce ki yi addu'a kamin ki kwanta, saboda ki samu tsari wani abu ba zai cutar da ke ba, mutum ko aljani ko wani ƙwaro mai cutarwa”
Waira dai bata ce komai ba sai sauraren Ummi take, can kuma ta ja blanket ta lulluba, sai Ummi ta kai hannu tana shafa kanta tana ta tunani har bachi yayi gaba da ita, sannan ta tashi ta ja windows din dakin dake bude ta rufe ta kashe musu hasken dakin taja kofar ta fice. Da tunanin abun da ta gani a wayar Nimra ta kwana a ranta, har mafarkin abun sai da ta yi tana ta tunanin yadda zata bullowa abun. Hanne ta shirya abun karyawa da taimakon Ummi, bayab ta gama shiryawa mijinta nasa abun karin domin baya cin na masu aiki, sanin wannan ya saka ta rike wannan al'adar ta yi masa girki da kanta a kullum ko da kuwa ruwan tea ne.
Ya baro bangarensa ya dawo bangaren Ummi yayi breakfast tare da yar'uwarsa suna ta hiran baya, kowa da kowa yana falon ana karin safe idon Ummi yana kan Nimra she just can't believe ace Nimra ce aka turawa sakon jiya, ko da yake hausawa sun ce ka yi naka ka barwa Allah sauran, domin tarbiya a yanzu duk yadda ka yi sai idan Allah ya tsare maka kawai. Ita kuma Waira nata idon yana kan Ummi tana tunanin abun da ta gani jiya har yanzu zuciyarta cike da tausayin Ummi, Maleek kuma nasa idon suna kan Waira a sirrance kallon da take yi Ummi ne yake ba shi mamaki, da haka kuma wata ilar ta ja shi ya fara kallace surarta.
Bayan kowa ya gama karyawa Ummi ta saka suka kwashe kayan suka kai kitchen, Maleek da Mahmood da Namra suka yi shirin tafiya aiki. Daman Waira tuni ta yi shirya a uniform dinta na makaranta school bus ta wuce da ita ita First fita a gidan sannan Maleek da Mahmood, daga baya Namra ita ma ta fice. Jabir kadai aka bari a gidan sai Umar da Nimra, shi ma be dade ba ya fita tare da Dr Zainab da Umar zuwa gurin wasu yan'uwansu da suke cikin garin Abuja.
Misalin 12pm Ummi na kitchen tana hada ma Waira cake Nimra ta shiga sanye da doguwar rigar material sai black hula dake kanta, jikin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon Ummi.
“Ummi me kike yi”
“Cake”
Ta amsa mata ba tare da ta juyo ta kalleta.
“Waira ake yi ma ko? Toh a saka da mu, Ummi ina son zan tafi gurin saloon din nan jiya ban samu ba, amman yau na yi da ita zata gama min da wuri”
Shiru Ummi ta yi kamar ba zata amsa ba, tana ta kallon harabar gidan da take hangowa ta windows din kitchen din sai kuma ta juyo ta kalli Nimra.
“Miyasa ba ayi miki ba a jiya?”
“Akwai jira ne sosai kuma da kika kira ni cewar Mommy ta zo sai na fasa na dawo gida”
Ta daga mata kai.
“A dawo lafiya”
Har ta juya ta fita sai kuma ta juyo ta ce
“Ummi lafiya kike yau kuwa?”
“Me kika gani”
“Na ga kamar kina cikin damuwa yanayin ki ba kamar na kullum ba”
“Daman akan samu hakan ai a gurin ko wace uwa, wata rana farinciki wani lokacin kishiyarsa karki damu tafi inda zaki je Allah ya tsare”
“Ameen”