← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 170

Sashe 67

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Saboda ba ni kadai Allah ya bawa ikon kula da ita ba, ni da ita duk a karkashin kiwonka muke Abiey”

Ummi ta amsa masa a gautsine.

“Abun da kike kokarin ki aikata na fahimtar da Nimra ba ni kadai zai shafa ba, ke da Ameer din za ku fi kowa cutuwa saboda rayuwarsa ce zaki rusa, ki haddasa masa bakinciki da ke kanki kuma ki butulcewa wanda yake dawainiya da shi tun yana karami har ya girma”

“Ban ce dole sai ta hanyar fada mata ina da alaka da Ameer ne kadai za a fahimtarda ita ba, amman kai me kake tsoro ne Abiey? Ban ce ka dauki dawainiyarsa ba ban bukaci komai daga gareka ba ni dai kawai ina son ďana a kusa da ni....!”

“That's it, daman na sani ai, amman babu yadda ban yi da ke ba a wacan lokacin akan ki aje yaron nan a hannunki kika ki, sai yanzu yaro ya girma yana rayuwarsa dabam zaki ce ki rusa rayuwarsa kuma ki rusa rayuwar mutanen da suke rike shi a matsayin ďa? Damuwata ba akan Ameer ne kawai ba har da matsalar da zaki jefa kanki a ciki ina jin tausayinki Zahra da abun da zai biyo baya”

Dr Zainab ta kalli Abiey ta kalli Zahra ta dafe kanta.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, yau Abiey da Zahra ne suke sa'insa? Abun da ban taba gani ba? Subhanallahi wannan abun yayi muni, Zahra ki yi shiru dan Allah karki sake magana”

“Har zuwa yaushe zan yi ta yin shiru Aunty Zainab? Shekara nawa a tare da Abiey? Ina da mafarkai da buri amman na rufe su saboda na samu zaman lafiya da mijina, shim ba ku taba tunanin kewa da kaunar uwa ga ďanta ba? Kai da ya aikatawa yarka haka ka ji zafi balle ni da ya kwanta a cikina wata tara da kwanaki na rike ka shi a hannuna na shayar da shi? Ko ka so Ameer ko karka so shi idan aka tsaga jinin Ameer sai an ga nawa a ciki”

Abiey ya girgiza kai yana murmushi takaici.

“Ba zaki gane ba ne Zahra, yaron da kike ta kokarin ki dawo da shi kusa da ke, ba shi da kirki ba ta inda zai girmamamu ko ya tsaya ya fahimce, ina gudun kar bakincikin ya zama mana biyu, domin ba ke kadai zai shafa ba har da ni, duk abun da ya same ki a tare za mu raba either na dadi ne ko akasin haka, sannan yanzu ba abun kunya ba ne ki zaunar da shi ki fada masa yadda aka yi kika rabu da shi? Bayan kin katse masa jindadin da yake a can?”

Ummi ta mike tsaye.

“Ba abun kunya ba ne, kuskuren da na aikata nake kokarin na gyara, amman kai abun kunya ne a gareka yanyanka su ji cewar ka ki ka taimaka min a lokacin da naje neman taimakonka, da ban aikata abun da zan kwanta a gado ya hana ni bachi ba...!”

Abiey ya hade fuska kamar be taba dariya ba, Dr Zainab ta yi saurin runtse ido tana girgiza kai.

WAIRA POV.

A cikin abubuwan da ta yanka ta bawa zomon karas ne kawai ya ci, sauran idan ta ba shi baya karba tana ganin haka ta mike tsaye tana shafa shi, can kuma ta dorashi saman kanta jin sonsa take kamar ranta, kawo mata zomon da malamin yayi ya tuna da yawa daga rayuwarta na baya, hannu ta saka ta cire ribon din dake kanta ta birjita gashin kanta ta dora zoman a saman kanta tana dariya, sai ta fara zagaya falon tana tafiya, har ta isa gurin kofa ta bude ta fito Maleek dake tsaye jingine da kofar ya juyo ya kalli zomon dake saman kanta yana mamakin yadda take rikonsa ko tsoro bata ji.

“Waira zata tafi daji”

Kallonta yake without asking ina ne dajin? Fita zata yi a gidan gaba daya or me take nufi? Bata damu da saka talkami ba ta nufi entrance din ta fara sauka, idonsa ya koma gurin kafafuwanta karamin guddugenta da take takawa tana sauka gurin gwanin sha'awar kafafuwanta ma sun fito sala sala kamar tsokar kaza, kallonta kawai yake har ta sauka ta nufi Garden a nan ya gane Garden take nufi da daji, samun kansa yayi ta saka wayar aljihu ya sauka gurin a hankali ya bi bayanta. Ko da ya shiga gurin har ta kusan raye icen kwakwa dake gurin, kansa ya daga yana mamakin yadda take iya hawan ice ba tare da taka komai ba, sai kafafuwanta da take tsalle da su da hannayenta da ta saka tana rike icen. Abun da ya fara zuwa masa a rai is saboda icen be gama girma ba ne saboda haka ne ba mata wuyar hawa ba, be gama raba dayan biyu ba ta haye sama riko dayan dake kusa da shi ta dira akai, can kuma ta samu sa'ar mika hannu ta riko icen mangoro ta koma kansa, yana tsaye a gurin kusan sai da ta hau duk wani icen dake kusa da kusa da juna. Masu yayan itatuwa ta tsinko ta jefo kasa sannan ta biyo ta sauko ta saka hannu ta dauka ta fara ci, sai da yayi kamar ya ce mata ta wanka kamin ta ci sai kuma wata zuciyar tace ina ruwanka? Cikinka ko nata? Yana kallonta har ta gama ci sannan ta nufi fanfon dake gurin ta kunan ta wanke hannunta ta tara hannayenta ta sha ruwan sai da ta koshi, kana ta nufi gurin da ta rufe zomon ta dauko tana masa magana da yarenta, gaba daya hankalinta be kai kan Maleek dake tsaye can gurin kofar Garden din yana kallonta ba domin ba a gurinsa hankalin nata yake ba. Ta tako ta fito cikin itatuwan ta nufo kofar fita a nanta tsaya tana kallon Maleek da tunanin ko ya ganta lokacin da ta hau itatuwan, dan tsoro da fargabar kar yayi mata fada ko ya fadawa Ummi ta yi mata ya saka ta kasa karaso gurin sai kallonsa take tana shafa zomon dake hannunta.

‘Waya koya miki, hawa itace? For how long kike hawan itace’

Wani salon iskanci da rainin wayo na kin son magana irin na Maleek, duk a cikin ransa yake mata wadannan tambayoyin kamar ance masa zata iya karanta abun da yake ransa ne. Ganin wannan ba zata fitar da shi ba ya saka shi tambayarta abun da ya saka ya biyota a gurin, domin tun a dazun da ta yi maganar abun yake cinsa.

“Waya fada miki Ummi zata mutu?”

Ta yi kasa da kanta kamar ba ita yake magana ba.

“Uh.. Hmm”

“Waira na sani, ta gani”

Cikin yanayin na jinin sarauta ya taka ta karasa inda take tsaye, sai ta yi baya ta jingina da wayar dake gurin.

“Waya fada miki? Ta ya kika san Ummi zata mutu?”

A take idonta ya cika da hawaye.

“Ummin tana da ciwo ciwon mai kashe Ummin ne, ciwon na mutuwa ne”

“Wane lalar ciwo ne?”

“Ban sani ba, amman bata fadawa kowa ba Ummin tana jiran mutuwa, Waira ma tana jiran mutuwa”

“Waye zai kashe ku? What kind of nonsense is this?”

“Ba karya ba ce, na gani da gaske Ummin tana da ciwo, kuma Ummin tana son ta ga Ameer”

Ta share hawayenta, maganarta ta masa wani iri ya kasa yarda gaskiya take fada ko akasin haka, amman da karya take ba zata fadi haka a gaban Ummin ba dazun har tana kuka. Sai da yayi kamar ya tambaya waya bata zomon dake hannunta sai kuma ya juya ya fice daga gurin, da kuzarinsa ya dawo part din Ummi yana kokarin hawa Stairs din Jabir da Mahmood suka sauko, kai tsaye dakin Ummi ya nufa, sai da ya suke ajiyar zuciya sannan ya kai hannu ta tura kofar ďakin ya saka kafarsa sai duk ya ji wani iri domin ba zai iya tuna lokacin da yake da kurciya ya shiga ďakin mahaifiyarsa ba, ko ciwo take sai dai ya gaisheta a falo ko bangaren mahaifinsa idan sun hadu. kamshin turaren jikina kamshin dakinta, jimke hannayensa ya fara yi thinking of ta ina zai fara, kamar wanda aka kama yana sata haka jikinsa ya fara rawa tun kamin yayi abun da be saba ba wato bincike...

35

THREE DAYS LATER...

Nimra ce kwance a cinyar Dr Zainab, kallo daya zaka yi mata ka san damuwa da kuncin zuciya sun saka ta a gaba, domin ta rame sosai kamar ba ita ba, kwana biyu bata iya cin komai sai ruwa su ma kuma idan Ummi ta matsa mata ne, gaba daya ta dauki damuwa ta saka a ranta, bata fita daga dakin kullum tana ciki idan an kawo mata abinci yadda aka aje shi haka za a dauko shi. Duk wani kokari da yar'uwarta Namra ta yi na ganin ta dauke mata hankali daga damuwa abun sai ya ci tura domin ba kadan soyayyar Ameer ya kama ta, tana taba jin som namiji kamar yadda take son Ameer ba, bata san yadda zata cire soyayyarsa a ranta ba ko da kau shekaru dari aka raba mata nan gaba, wani irin sonshi take irin son da take jin zata iya kai karar Abiey da Ummin a gurin wadanda za su barsu su ji maganarsu abarta ta auri Ameer.

“Nimra rayuwa ta yi haka? Dubi yadda kika maida kanki? Ni dai wannan zuwan be min dadi ba sam na ji abubuwa kuma na ga abubuwan da ban jidadinsu ba”

“Mommy yanzu babu yadda zaki yi ki lallaba Abiey ya bar ni na auri Ameer? Wallahi ina son Ameer, daman na san haka zata faru shiyasa na ce zan fada miki wata magana tun a farkon zuwanki na so na fada miki abun a sirrance saboda ki san yadda zaki shawo kan Abiey sai gashi komai ya lalace ya zo ta inda ba mu zato ba”

“Nimra abun da iyeye basa so hakuri ake yi, karka zafafa kace kana so, abubuwa da yawa ba alheri ba ne a garemu, ki yi wannan nazarin kuma ki yarda da hukuncin Allah”
Chapter 67 · 0% Book details