← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 170

Sashe 59

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can kuma ta yanke kiran tunawa da ta yi da Ummi ta tafi, kusan tun da take a rayuwarta bata taba shiga tashin hankali irin wannan ba, bata saba yi na Ummi karya ba a lokacin da ta koyi yin karyar kuma ba ta yi zaton asirinta zai tonu ta wannan hanyar mafi muni ba. Shigowar Ameer ya saka ta mike tsaye da sauri ta nufi inda yake shi ma ya nufota.

“Ya aka yi haka ta faru?”

“Ban sani ba, wata kila wani ya fada ma mata ne, ko kuma ya kawo ta nan”

“Na so na tararda da ita da sai na yi mata bayani ko yanzu zamu tafi gidan tare zan fada mata komai”

“Wane irin bayani kuma? Ameer are you okay? Zan yi magana da ita tukuna”

Ya kama hannunta.

“Nimra ina fatar kin shiryawa wannan, daman soyayya dole akwai kalubale balle kuma irin ta mu da muka boye, amman ni I'm ever ready to marry you, ban san miyasa iyayenki suka tsane ni ba, but i trust you na san zaki iya shiga ko wane irin hali saboda ki ga soyayyarmu ta daure haka ne?”

Ta daga mishi kai.

“Good kamar yadda zan iya aikata komai akanki, and ina tunanin wannan dama ce a gareki da zaki bayyana musu wanda kike so, kuma ki fada musu cewar ba zaki auri kowa ba sai wanda zuciyarki take so, matukar suna kaunarki na tabbatar za su bar mu mu auri junanmu, kuma ki daina wannan kukan haka ba wani abun tashin hankali ba ne, zamani ya zo da an daina abubuwa da yawa, yanzu an waye ba kamar da ba ne zuwan dakin saurayi ba wani abun ba ne, kawai dai boyewar ne ina tunanin zai zama laifi a gurinsu, shi ma kuma laifinki ne domin tuntuni na yi ta neman ki ba ni damar bayyana kaina a matsayin masoyinki kika ki, i hope ba zasu ce za su raba ni da ke ba Nimra, saboda zan iya mutuwa idan iyayenki suka aikata haka, domin ni na dade da fadawa iyayena cewar ke nake so kuma sun goya min baya”

Ya rairaice mata yana ta saka mata maganganu a cikin kai kamar gaske, ita kam jikinta ya dauka kuma ta yarda har sonsa da tausayinsa sun karu a zuciyarta.

“Zan yi magana da Ummi zan fada mata gaskiya, kuma na san tana da fahimta zata fahimta amman Abiey...”

“Idan har uwa zata fahimta me zai hana uba ma fahimta matukar yana son farincikin yarsa? Ko dai ance na yi ma iyayenki wani abun da ban sani ba ne Nimra”

Ta girgiza kai.

“Aa bari na tafi”

Ta saki hannunsa ta nufi dakinsa ta dauko jakarta ta fito ta mayafinta ta saka talkaminta ta fito ta dauki wayarta dake kan kujerar falo ta sumbanci Ameer sannan ta fice. Binta yayi da kallo sai da ta fice sannan yayi murmushi.

“Now iyayenki za su ji zafin da mahaifina ya ji a lokacin da kuka yi sanadin da ya koreni, bari mu gani ke ma korarki za su yi, ko kuma za su ba ni dama na fito neman Aurenki ne? Not just them Maleek ma would feel the pain....”

Abun da ya faru a yau ba karamin faranta nasa rai yayi, ko ba komai ya samu dama ta biyu da zai kuntatawa iyayenta da ita Nimra da yake ganin an hada kai da ita an cutar da shi.

UMMI's POV.

Daker ta tuko motarta ta dawo gida, a harabar gidan ma ta dade zaune a motar sannan ta bude ta fito tana tafiya kamar marar lafiya ta shiga falonta. Hanne akwai ta samu a falo tana zaune tana kallon Plasma girkin data dora kuma yana Kitchen, Hanne ta mike tsaye da sauri tana yi ma Ummi sannu da zuwa hankalinta a tashe ganin hawaye a fuskar uwar ďakinta.

“Sannu da zuwa Hajiya, lafiya?”

Ummi bata iya amsa mata ba ta haura sama tana tafiya daker sai ka ce mai ciwon kafa, saman bed dinta ta fadi zaune. A yau kam sai ta ji tana kewar mahaifiyarta fiye da kullum, wasu kalamai da tarbiyar da mahaifiyar ta dage akansu take tunawa, ashe haka iyeyenta suka ji? Musamman ma mahaifiya domin ita ko da ta tashi bata san natan mahaifin ba, sai dai mahaifiyarta ta sha wahala akanta saboda ta yi rashin jin magana a lokacin da take da kurciya, kuma mahaifiyar na yawan fada mata cewar idan ta fita bata da kwanciyar hankali har sai ta dawo, ita kiriniya ce kawai take yi sai jan magana, wani abun ma ba ita take aikatawa ba faruwa yake yi saboda wautarta da shiririta, a wacan lokacin na su tashin akwai matukar kurciya da rashin wayo, kamar na yaran yanzu ba, da wasu suke fin iyayen ma wayo. Ita ba ďakin wani take zuwa ba, amman hankalin mahaifiyarta yana tashi ina ga ita data kama Nimra a gidan wani.

“Ashe haka kike ji Mama? Allah ya miki lullube kabarinki da rahma ya yafe miki”

Ta mike tsaye ta cire hijabinta ta nufi inda wayarta take ta dauka ta kira Abiey, ringing biyu ya yanke kiranta ya kira da kansa.

“Hiayatee....”

Sai ta yi shiru kamar ba zata amsa ba.

“Are you there?”

“Abiey... Wallahi a yau ina jin kewar mahaifiyata fiye ko yaushe, na san na girma amman ina jin kamar ace tana kusa da ni na raba jikinta na ji sanyi kuma na fada mata damuwata, duk girman mace tana bukatar uwa ko uba a kusa da ita, ko dan ta kallesu kawai ta ji sanyi a ranta, kuma ta kara kyautata musu”

“Hiayatee, yanzu aka kira ni daga makarantar su Waira wai ta yi fada da wata suna neman mahaifinta, amman zan kira Maleek ko Mahmood su tafi, gani nan zuwa gida yanzu nan”

Ya yanke wayar, kusan shi ne abokin shawararta a duk abun da ya shafe ta, idan bata fada masa damuwarta ba waye zata fadawa? Shi ne kadai mutumen da ya ke gane abun da take so tun kamin ta furta. Wayar dake hannunta ta fara ringing tana dubawa sai ta yi arba da number Yaya Maryam, yayarta the one and only sister she has, wacce suke uwa ďaya uba ďaya, yar'uwar da suka sha wahalarta a tare da Mama lokacin da kurciyata take cinta.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikissalam, Zahra Lafiya kike?”

“Ba kalau ba Yaya Maryam ina kewarku”

“Miya faru? Abiey ya kira ni yace na kira ki ko hankalinki zai kwanta kin kira kina masa maganar Mama, hankalinshi duk ya tashi”

“Yaya Maryam, yau na ďanďana wani ďaci da uwa take ji idan Yayanta suka mata karya, ina cikin wani irin bakin ciki na uwar da ta bawa yayanta tarbiya aka rusa, sai dai kuma a yanzu yanke shawara nake”

“Fada min abun da ya faru?”

Ummi na cikin labarta mata abun da ya faru ta ji an yi knocked a kofar dakinta Nimra na kiran sunanta..

“Ina zuwa”

Ta yanke wayar tana kallon Nimra data turo kofar ďakin ta shigo idonta a kasa domin tana jin kunyar hada ido da Ummi, ba dan fuskarta dake nuna alamar kuka ta yi ba, da ta rantsewa Ummi akan karya cewa gurin Saloon ta tafi albashi daga baya sai ta bayyanar mata da Ameer a matsayin wanda take so.

“Da ace kina da kunya kamar yadda nake gani a idonki, da Ubangijinki ya kamata ki fara kunya, kamin ki aikata abun da kika aikata, da kin ji kunyar yin karya da kuma shiga gidan wanda ba mijinki ba ki taba jikinsa ki sumbance shi ki cire tufafinki a gabansa ki bar shi ya aikata abun da yake so da ke”

A lokacin ďaya ta saki jakar hannunta da mayafinta da wayarta ta fadi kasa ta kama kafar Ummi.

“Aa Ummi na yarda na ina zuwa gidan, ina rika hannunsa ko taba jikinsa ko sumbantarsa amman Wallahi na rantse miki da sarkin da babu abun bautawa da gaskiya sai shi ban taba aikata zina ba, ban taba yarda wani namijin ya san yi a matsayin ƴa mace ba, Wallahi ban aikata ba Ummi”

A tsakanin yarda da yar'uwarta Ummi ta samu kanta, ba zata yi saurin yarda da maganar data fada mata a yanzu cewar bata aikata zina ba, domin a baya ta yarda da ita kuma ta same da wannan halin, kuma ba zata karyatata kai tsaye ba, domin ta yi mata rantsuwa da Allah.

“For how long kike tare da shi? Waye shi? Miya fada miki ya yaudare ki kika watsar da tarbiyarki? Miyasa ba zaki fito ki fada mana kina son aure ba? Akwai abun da muka rage ki da shi da kika tafi gurin wani ya baki?”

Ta girgiza kai tana kuka sosai.

“Ba ku rage ni da komai ba Ummi, idan na fadi haka na yi karya kuma na ci amanarku”

“A yanzu ma kin ci amanarmu Nimra miye rage? Kin yi komai kin daka kin tankade kin shanye”

“Ummi ki dubi girman Allah ki yafe min”

“Ki fada min wanene?”

Ummi ta daka mata tsawa sai ta jikinta ya dauki rawa domin bata taba mata fada haka ba.

“Idan baki fada min ba, shi Abiey idan ya zo sai ki fada masa”

Nimra ta matsa baya da sauri tana girgiza kai.

“Aa Ummi ba zaki fadawa Abiey wannan maganar ba, ba zaki fada masa abun da na aikata kai tsaye ba, wannan a tsakaninmu ne, ba zaki fadawa Abiey haka ba dan Allah Ummi”

“Toh wanda ya koya miki karya ya yaudara yace ki zo ki koya min ko?”

“Ummi dan Allah ki rufa min asiri, karki fadawa Abiey wannan maganar”

“Idan kika ga ban fada masa ba, to na mutu kamin ya iso ne”

Tana jin hakan ta tashi da sauri ta dauki wayarta ta jakarta ta fice daga dakin. Dakinta ta shige ta maida kofa ta rufe ta saka key. Cikin hanzari irin na magidanci mai damuwa da iyali Abiey ya shigo gidan, kamin na isa ďakin da matarsa take har ya matsu. Ko sallama be yi ba ya tura kofar ďakin ya shiga.

“Madam Lafiya”
Chapter 59 · 0% Book details