Sashe 136
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tashi ta shiga bandaki, sai ya bita da kallo kamin ya dauki rabbit din ya fara shafawa yana laka shi da jikinsa jin yake kamar Waira yake tabawa saboda ta saka hannunta ta taba gurin. Tana fitowa daga bandakin ya maida idonsa a inda suka fi yi masa dadin kallo wato fuskar Waira, shigar da ta yi bandakin ta wanke baki da fuska sai ya ga kamar ta kara kyau da kwarji, sanyin ruwan dake fuskarta sai ya ji kamar ta tafi ya lashe su. Gaban madubi ta nufa ta dauki ribbon ta daure gashin kanta sannan ta nufi kofa kamin ta isa har ya riga ta bude mata kofar kamar wata sarauniya. Tana fara saukowa stairs din sai ta tsaya ta juyo ta kalleshi.
“Ba zan iya cin abinci a can ba kowa yana nan”
Wani iri take ji a yanzu, daman can tana ganin kanwarta da ta Abiey bata jika ba, a yanzu kuma tana ganin Ummi kamar tana tsoronta ne ko kuma ta tsaneta saboda abubuwan da suke faruwa.
“Na kawo miki daki?”
Kamin ta bawa Ameer amsawa suka hango Abiey na magana ba dan ya ji abun da suke fada ba sai dan ya fahimci damuwar Waira.
“Sauko mu tashi zamu yi mun gama ai, idan ganinmu ne zai hana ku ci a nan”
Ta kalli Ameer sai da ya karfafa mata guiwa ta hanyar daga mata kai, sannan ta sauka a hankali yana gefenta har suka isa dinning, kujera ce first abun da ya fara ja mata a zatonsa zata zauna a inda yaja, sai ya ga ta nufi kujerar da babu kowa kuma bata kusa da kowa ta zauna, tana sanda kai kasa alamar bata son kallon mutane. Ameer ya zauna a kujerar da ya ja, Namra ce ta fara mikewa tsaye sai Abiey ya kalleta ya ce.
“Baki gaishe da Yayanki ba?”
Ta kalli Abiey with shock, sai dai ba zata iya musawa mahaifinta ba, ko kuwa daga ita sai shi ne balle kuma a gaban yan'uwanta, saboda haka ta kalli Ameer ta ce.
“Good Morning”
Ya amsa mata kai, mamakin na gaf da kashe shi ganin Abiey ya dauko wata hanya da be san me yake nufi da haka ba.
“Kuma duk sai na fada za ku yi magana da shi? Wannan ya zama na karshe da zai shigo ba ku masa magana ba, musamman da safe irin nan, kai ma kuma karka jira sai sun maka zaka iya fara musu magana”
Ameer ya amsa da kai yana kallon Ummi dake kallonaa with so much joy.
“Good Morning”
Maleek da Mahmood suka gada baki gurin furtawa bayan sun gama kallon junansu da mamaki, su ma dai da kai ya amsa musu. Abiey ya mike tsaye da murmushi a fuskarsa ya ce.
“Good, idan ka gama ina son magana da kai Son”
Maleek ya mike tsaye daman tun shigowar Ameer da Waira a dinning din yake jin kamar yana kan ƙaya. Abiey ya juyo ya kalleshi
“I guess you're not the only Son here, i'm taking to Ameer, shi nake nufin idan ya gama ya same ni a ciki akwai maganar da zan yi da shi not you”
“O.... O.... Okay...”
Maleek ya fada har sau biyu a ukun ne ya samu hada kalmomin, hakan kuma be saka shi fasa barin dinning din ba, suka fice tare da Mahmood suna kuskus, Namra kuma ta nufi stairs. Sai da Abiey ya fice daga sashen sannan Ameer ya kalli Ummi da mamaki ya ce.
“Me yasa Abiey yake min haka this time? Is he up to something?”
Ummi yaja kujerarta baya ta mike tsaye ta nufi inda yake zaune ta shafa kansa ta sumbanci saman kanta ta kwanto da shi jikinta.
“No ko kadan, addu'ar da na dade ina yi ce Allah ya karba min a yanzu, farinciki da na dade ina son samu a tare da duka yayana ne Allah ya kawo min cikin sauki”
Sannan ta kalli Waira ta ce.
“Waira ni ban tsane ki ba, karki kalleni a baibai, kawai ina kokarin ganin na shirya tsakanin yayana ne”
“Anjima nake son na tafi”
Waira ta fada, Ummi bata ce mata komai ba ta saki Ameer ta nufi hanyar dakinta. Ameer ya mike tsaye yayi serving dinta sannan ya zuba na kasa.
“Abiey yace be yarda ki tafi ke kadai ba, sai dai a rakaki kuma sai an sanar da jami'an tsaro ina ganin ya kamata ki hakuri har zuwa gobe saboda ayi komai cikin kwanciyar hankali, kuma Maleek da zai raka ki zai samu lokaci ya shirya kamin time din”
“Bana son kowa ya raka ni, a garin ba a karba baki, kuma za a iya cutar da wasu saboda ni, ko kuma ma laifina ya yafe su”
“No ba zan iya bari ki tafi ke kadai ba Waira, ko da kuwa kashe wanda zaku tafi tare za'ayi, i know baki sona a kusa da ke, shiyasa da Abiey ya ce na rakaki na zabi Maleek ya rakaki, saboda kin fi sonsa kuma hankalinki zai fi kwanciya idan yana tare da ke sama da ni”
Kamar tace masa kai ma ba tsanarka na yi ba, kawai da zancen aurena da kai ne bane so, sai kuma ta samu kanta da jin nauyin kasa furta haka. After sun gama breakfast din Ameer ya nufi dakin mahaifiyarsa wato Ummi, first tambayar da yayi mata is.
“Kin san abun da yasa Abiey yake son magana da ni?”
Sai ta girgiza masa kai.
“Ban sani ba, be fada min zai yi wata magana da kai ba ban san komai akan abun da zai tambayeka ba”
Ya juya ya fice daga dakin yana tunanin kondai Abiey zai roki wata alfarma a gurinsa ne akan Waira shiyasa yake masa magana kamar daman can babu wata kiyaya ko tsanar juna a tsakaninsu. Be san bangaren Abiey ba, dan haka yayi ta bude dakunan da suke corridor kamin ya isa babban falon dake cike da sanyin ac. Abiey yana hakimce saman kujera sanye da jallabiyar da ya saka tun safe sai wayar dake hannunsa yana duba yanar gizo.
“Bismillah Ameer shigo ciki”
Ameer ya cire talkamin kafarsa for the first time saboda zai shiga gurin wani. Ya isa cikin falon sai ya zauna a kujerar dake nesa da wanda Abiey yake zaune, zuciyarsa na raya masa abubuwa kala kala akan kiran da Abiey yayi masa, ko da yake hausawa sun ce karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata. Shiru ne yayi ta wanzuwa a cikin falon na tsawon lokaci kamin Abiey ya dago ya kalleshi ya ce.
“Da gaske baka ra'ayin raka Waira garinsu?”
Yayi jimmmm kamar mai nazari sannan ya daga kai.
“Yeah akwai abubuwa da zan yi masu muhimmanci a nan, kuma zata fi jindadin tafiya da Maleek din dai”
“Okay, na yi magana da Imam na sanar masa komai tace zuwa 11pm na zo tare da yarinyar zai musuluntar da ita, kuma ya gabatar da ita a gurin mata yan'uwanta da za su nuna mata yadda zata yi addinin, su fada mata wasu abubuwan da suka kamata”
“Hakan yayi kyau”
“Abu na biyu ina son mu tattauna da kai ne akan ciwon mahaifiyarka, likitanta ya fada min tana bukatar a kwantar da ita a asibiti for now, ni kuma na san halinta bata son zaman asibiti maybe ma yana daga cikin dalilin da ya saka nmta boye mana ciwon tun farko, i know bata bukatar tashin hankali a yanzu shiyasa bana son takura mata cewar dole sai ta tafi asibiti, amman na san tana sonka kuma tana jin maganarka zaka iya lallaba mana ita ta yarda ta kwanta asibitin hakan ba yana nufin rasa rayuwarta ba, no saboda a samu damar bata kulawar da ta kamata, and ina tunanin ko da zata kwnata ba zata wuce sati a nan ba saboda ina tunanin fitar da ita waje, ko ba komai a can sun fi mu kayan aiki da kula da marasa lafiya yadda ya kamata amman me ka gani? Ban yi maganar da kowa ba, kawai na fi son na fara jin ra'ayinka ne”
Ameer ya dan yi shiru yana mamaki ace yau shi ne Abiey yake tambayarsa shawara akan Ummi, be tambayi yayansa ba.
“Zamu iya fitar da ita India ko Egypt suna da asibiti mai kyau da kwararun likitoci da suke kula da wannan bangaren kuma na ga ana yawan kai masu irin ciwonta kasashen, akwai kuma London can ma suna da asibiti mai kyau”
Abiey yayi murmushi yana jinjina kai.
“Good ni ma tunanina zuwa can zai fi, amman dai na yi shiru na ji irin shawarar da zaka yanke ne, zan yi magana da Maleek da kuma likitan sai mu ga inda ya kamata”
“Okay”
Ameer ya mike tsaye.
“Ameer, please feel free to talk to a duk lokacin da kake bukatar wani abu, ko da kuwa shawara ce, kuma ga yan'uwanka nan please ka manta da komai ka zauna lafiya da su ko dan saboda mahaifiyarka, ka dauke ni a matsayin uba, na san kana kallona a matsayin wani makiyinka no ba haka ba ne, akwai wadandansu dabi'u da bana so a cikin halayyarka, kuma ina ganin kamar ka dauko hanyar sauyawa, ina fatar hakan zai daure Allah ya kara hada kanku, su ma na yi magana da su, kuma zan sake yi sai na hadaku gaba daya na yi muku nasiha, and idan za a fita da ita waje tare za mu da kai, ko da sauran ba su samu damar zuwa ba”
“In Shaa Allah”
Ameer ya fada sannan ya juya ya fice daga falon.