← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 170

Sashe 42

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Dukan abun da kake zargin na aikata saboda na cutar da kai ban aikata ba Ameer Allah shi ne shaidata, Maleek ma ba shi da wani buri ko kudiri na cutar da kai, sai dai kuskuren fahimta da kuka samu, kuma ni ban san ka bar motar a can ba balle har na saka a aikata maka abun da kake zargina da shi, mi zai saka na saka wata a motar dan kawai na cutar da kai, miye ribata idan na yi haka? Ka fada min garin da ka tafi? Balle na aika wani yayi maka haka? Ka aminta da ni Ameer, ina cikin damuwar abubuwan da suka faru, mahaifina baya magana da ni saboda abun da na aikata na baka mota da kudi da wayata da na yi, har aka samu wata yarinya a motar ka”

Yana yi yana tsayawa har ya gama karantawa, yanayin yadda ta turo masa sakon zube a lokaci daya ya tabbatar masa da cewar ya fara yin nasarar karya lagonta, duk kuwa ba be san abun da take shirya masa a boye ba. Har yanzu be ji ya yarda da ita cewar ba da hadin bakin yayanta ta bashi motar ba.

“Sarewar kuma ban duba motar ba, balle na san abun da yake ciki saboda yau aka kawo motar tare da yarinyar a gidanmu, amman bayan komai ya lafa zan duba motar na dauko maka sarewar idan tana ciki, kuma ba zamu hadu a inda muka saba haduwa ba sai dai a gurin da muka taba zuwa da kai wajen Abuja, shi ma kuma idan har na samu sarewar domin ban san iya abun da zai faru idan mahaifina ko Maleek ya gan ni tare da kai ba”

“Really”

Ya fada bayan ya gama karanta sakon na biyu, sannan ya jefar da wayar saman gado ya cire rigarsa yana tunanin wata kila kuma ita ce take shirya masa wani zagon kasa kamin ya gama saka tasa gadar saren.....

DR SHURAIM POV.

“Wato ana yi ma mutun kallon mai hankali sai ka tarar babu hankali a tare da shi, ko kuma tunani zan ce?”

Hajiya Hajara ta fada tana masa kallon bacin rai.

“Yanzu ina yarinyar take?”

Cewar Mahaifinsa. Shuraim ya kalli mahaifiyarsa domin damuwarta ce ta fi daga masa hankali ya san mahaifinsa mai fahimta ne zai iya fahimtarsa amman Hajiya kam sai yayi da gaske.

“Ita yarinyar tana hannun Police na kai musu ita, ni kuma ina lafiya”

“Ina kwana? Kuma na kira wayarka baka daga ba daga baya kuma ka kashe wayar”

“Hajiya yarinyar bata yarda ta bar ni ba, a dole a can muka kwana ni da ita CID din, sai da safen nan da suka kama hanya sannan ta hakura, kuma kin san mace ce be kamata na barta ta kwana a can ba saboda mace ce, kuma na san idan idan na fada miki ba zaki bari na kwana a can ba ko dan yanayin jinin dake zuba a idonta ya kamata ace na tsaya a gurin gudun kar sai na dawo wani abun ya faru su ce ni na cutar da ita, shiyasa ban amsa kiranki”

“Aifa duk yadda zaka yi ka kare kanka ka sani, ku kullum ana nuna muku yadda za ku tsira sai son jefa kai a halaka kuke”

Fada ta yi masa sosai a washen garin ranar da ya koma gida, sa'arsa daya mahaifinsa ya masa uzuri har ma ya tare masa fada a gurin mahaifiyata. Sai da ta gama masa fadan tsab sannan ya fita daga falon ya shiga domin bangarensa yana wajen falon ne, ya shiga dakinsa cikin rashin jindadin rayuwa da Waira, har lokacin ya kasa natsuwa da inda za aje da ita, tunawa da yadda ta tsaya tana kallonsa ba ta yi kuka ba ya kara tausayinta a cikin ransa.

“Allah sarki Allah yasa tsare ki Waira Waira”

Ya maimaita sunan a karo na farko bayan idonta, ya kalli inda ta cije shi a hannu har ya fasa yana murmushi zuciyarsa sam bata masa dadi, ya san abu ne mai wahala kamin ya manta da lamarinta ba nan kusa ba.

“I hope zaki samu gurin da zaki aminta da kowa, Allah ya hana masu niyar cutar da ke su cutar da ke”

Kamar marar lafiya haka ya wuni a ranar saboda rabuwa da Waira, wata kila da sun dade a tare da ba zai ma iya sabuwa da ita ba saboda shakuwa. Musamman da ya je asibitin suna da zancenta wasu kuma na tambayar abun da ya faru bayan barin asibiti.

©Khadeeja Candy
   ©®Copyright
        2023

*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

22

Ummi ta yi saurin shiga tsakiyar su tana kallon Maleek dake huci abun da ba halinsa ba.

“Bata san komai akanka ba, ba ta yi hakan da ganganci ba, bakuwa ce miyasa baka yi wannan tunanin ba?”

Ya dauke kai ba tare da yace komai ba ya shige dakinsa, gaba daya manta yayi abun da ya kawo shi dakin har sai da ya zauna na tsawon lokaci sannan ya mike tsaye, sai ya ji kansa na mugun sarawa irin jikinsa jikinsa yayi weak sosai a take zazzabi ya karyo masa, daker yayi alwala a dole dakin yayi sallah Magariba yana gamawa ko addu'a be tsaya yi ba ya hau gado ya kwanta ya lulluba saboda sanyin da yake ji. Ummi ta kama hannun Waira ta koma da ita cikin dakin tana fada da Nimra wacce ta biyota a guje.

“Ummi na shigo na samu bata kan gadon, i just want to check on her ashe ta boya bayan curtains sai da na daga na ganta ina mata magana na rika ta sai ta fisge ta fito a guje”

“Gashi ai kin tsoratata, kuma kin ja mata ta sha mari ji yadda bakinta yake jini”

Bandaki Ummi ta shiga da ita ta kunna tap ta tara cup ta tara ruwa ta kai mata a baki, kamar wata tsumma haka Waira ta zama hawaye kawai ke zubo mata, duk inda aka yi da ita sai ta bi, ta kuskure baki kamar yadda Ummi ta nuna mata sai ta zubar da ruwan tare da jini, haka tai ta yi har sai da jinin ya fita sannan Ummi ta tafi dakinta ta dauko brush ta saka man goge baki ta mika mata.

“Zaki iya wanke bakin ko kadan ne? Saboda akwai ciwo a bakin”

“Ummi zafi zata ji fa, saboda brush ne kara dai a kyaleta sai gobe ko jibi sai ta wanke”

“Okay”

Ta hada mata ruwan wanka da kanta sannan ta juyo zata fito sai Waira ta biyo bayanta har lokacin hawaye take, yanzu kam ba kuka rashin marin da Maleek ya mata take ba, kukan barin garinsu da rayuwarta take, yanzu kam ta gane ta yi kuskure mai girma, ta baro mutanen da ta sani kuma take iya rayuwa a cikinsu ta dawo a inda bata san kowa ba, kuma kowa be santa yarensu da addininsu ba daya ba, abincinsu ma ba daya ba.

“Wanka zaki yi”

Ummi ta nuna mata ruwa, sai ta juya ta kalli ruwan ta juyo ta kalli Ummi ta fashe da kuka, a nan hankali Ummi yayi matukar tashin tausayinta ya kara kamata domin ta san bata jin yarenta kamar yadda police din suka fada tun kan a kawo ta, gashi ta samu mari daga Maleek ga kuma rashin sabo da su da bata yi ba, domin farkowa kenan ta ganta a dakin akan gado sai sanyin ac, hakan ya saka ta tashi ta boya a bayan lalulen dakin har sai da Nimra ta shigo ta ganta, a kokarinta na gujewa Nimra ne ta fito dakin a guje saboda barin kofar dakin a bude da Nimra ta yi.

“Wani abu na miki ciwo ne?”

Ummi ta taba hannunta sannan ta taba shafin fuskarta a inda Maleek ya mareta gurin har ya kumburo yayi mata ja kasancewar fara irin farin nan da ko sauro ya cijeta sai jikinta ya bayyana.

“Yi hakuri, hakan ba zata sake faruwa ba na miki alkawari”

Ita dai kallon Ummi kawai take ba dan tana jin yarenta ba, ita ma Ummin tana kokarin fahimtar da ita abun da take fada ta hanyar amfani da hannu, sannan ta saka duka hannayen ta goge mata hawayen.

“Ki yi wanka sai a kawo miki abinci”
Chapter 42 · 0% Book details