← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 170

Sashe 36

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Bata son skirt amman an saka mata wando, Yaya ta yi kyau ko?”

Ya daga ma Maimoon kai, sai Waira ta girgiza masa kai, a tunaninta wani abun Maimoon take nufin ayi mata ya amsa mata da kai, kamin ta riko hannunsa tana nuna masa bathroom din.

“Miye?”

Ya wuce gaba ta bi bayansa suka shiga bathroom din sai ta duka ta saka hannu ta dauko tufafinta, wannan ta dauko rigarsa ta mika masa, sai ya karba ya aje yana murmushi nata tufafin kuma ta rumgume abunta. Dayan hannunsa ya saka ya dafa kafadarta ya matsar da ita gurin madubin dake bathroom din ya duka ya dan daga ta kalli kanta a madubi, da sauri ta rufe idonta, domin basa amfani da madubi a garinsu, da ruwa suke amfani su ga fuskarsu, ko kuma yi tsafi su ga fuskarsu, ba yau ne karo na farko da ta taba wanka ba, tana wanka amman sau daya a shekara kuma a duk lokacin da ta yi wanka taba duba kanta a ruwa ko kuma Eid yayi mata tsafi ta ga fuskarta, sai dai a yau yadda ta ganta kyar a jikin madubin ta san an mata wanka da ya amsa sunan wanka ta wanku iya wankuwa, jikinta har yanzu ciwo yake na murzar fatar jikinta da Hajiya Hajara ta yi da soso. Ya sauke ta kasa sannan ya fito bathroom din tare da ita suka fice daga dakin gaba ďaya. Yadda aka shigo da ita tana kallon ko'ina haka take kallo a lokacin da ya fito da ita falon kamar zata zubar da ido. Kujera ya nuna mata ta zauna sai ta ki zaman har sai da ya nuna mata kayan marmarin dake a plate gabanta, sai ta sake shi ta aje kayanta a gefe daya ta saka hannu ta dauka, abun ka da mai jin yunwa sai ta fara ci da sauri ita kanta bata tantance kalar yunwar da take ji ba har sai da suka fara sauka a cikin hanjinta. Zaunawa yayi a saman kujera yana kallon yadda take daukar fruits din tana ci, bata ko tsayawa ta tauna da kyau sai ta hade.

“Wannan ce bakuwar ta mu”

Cewar wani Magidancin mutum dake zaune akan wheelchair fuskarsa sak ta Dr Shuraim.

“Ita ce Doctor”

Hajiya Hajara ta amsa masa tana bayansa tana turo keken, da sauri Waira ta cire hannu a fruit din ta rike kafarsa tana yi ma mahaifin Dr Shuraim kallon tsoro da mamakin yadda kamarsu ta bace kamar an tsaga kara.

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

Wadanda ba su account za su iya turo mtn card ta 08036126660

19

Bata jin kalma ɗaya daga cikin maganar da suke, sai ta san akanta ake maganar domin yanayin kallon da suke mata ya nuna haka, ita duk abun da ake bata yarda ta saki hannun Dr Shuraim ba, bata yarda da kowa ba sai shi bata jin sakewa da kowa sai shi kadai, domin shi ya fahimci kalar abun da take iya ci gashi baya cutar da ita, idan ma yayi mata allura to tana a sume ne bata sani ba, ba kamar mutanen da take ganin sun rike ta da karfi sun mata allura ba, ga kuma wadanda suka mata wanka.
Duk yadda suka yi kokarin sakata ta yi alwala sai ta ki daman can bata son taba ruwa balle kuma bata saba yi ba, bata taba sanin idan za'ayi ibada tsabtace jiki ba, musulunci ba addininta ba ne, saboda haka bata san komai akan addinin ba, sai ma ya zame mata wani bakon lamari ganin suna alwala sannan suka shimfida carpet suna abun da ba zata iya kiransa da ibada ba, domin bata ganin abun da suke bautawa, ba kamar su da abun bautarsu suke ganinshi ido da ido ba, ko suna amfani da aljannun ne, shi ne abun da ya fara zuwa mata a rai, domin ta san yadda aljannu suke iya sarrafa komai ciki har da sakawa ayi musu kalar bautar da suke so, ba abun da ya bata mamaki kamar yadda suka saka manyan tufafi suka rufe jikinsu, Dr Shuraim da mahaifinsa suna a gaba, Hajiya Hajira da yarta Maimoon kuma suna baya.
  Dr Shuraim ne yaja sallah suna sallame yayi addu'ar sallah sannan ya juyo ya kalli inda take ya sakar mata murmushi har ta yi kamar zata mayar masa sai dai ganin Maimoon na kallonta ya saka ta rufe idon nata gaba daya ta daina kallon kowa. Jin motsin mutun ya saka ta bude idonta daman so take ta ga idan ya gana ibadar, da sauri ta nufeshi ta kama hannunsa ta rike tana nuna masa dayan hannunta dake mata zogi.

“Akwai allurar da ya kamata ayi miki da yamman nan amman babu ta anan, dole sai naje pharmacy na siyo”

“Daman an taba barin mutum babu magani a irin wannan ciwon haka? Kamata yayi kamin ka ba su takardar transfer ka haɗa musu da ta magani ai”

Cewar Mahafinsa.

“Hankalina ya tashi ne shiyasa ban tsaya na yi abun da ya dace ba, domin har yanzu gani nake kamar cutar da yarinyar nan za su yi”

Yana maganar Waira na kallonsa bata ko kibta ido gaba daya hankalinta ya tafi gareshi kamar tana jin abun da yake fada, wani irin sakewa da natsuwa take ji idan tana kusa da shi, kamar sun fito ciki daya haka take jinsa. Ya nuna mata gurin zama.

“Zauna a nan can zan je na dauko magani”

Ta girgiza masa kai ko bata jin yarensa ai tana fahimtar zama yake son ta yi, ita kuma bata jin zata iya haka ita kadai har sai idan tare za su zauna. Babu juyin duniyar nan da be yi ba akan ta zauna ya tafi ya siyo mata magani amman ta ki, da ya zaunar da ita sai ta tashi tana riƙe masa hannu.

“Ashe kuwa idan zs a tafi da ita akwai aiki”

Amsawa Hajiya Hajara.

“Nima shi nake gani, saboda bata yarda da kowa sai ni, na ji suna zancen ayi mata allurar bachi, amman na faɗa musu cewar zai iya cutar da ita saboda ba ciwo take ba, balle ace tana kwana ba bachi”

Sai tausayinta ya kara kamasu, musamman ma Mahaifinsa, sai da yayi da gaske sannan ya ɓanɓare hannunta daga rikon da ta yi masa ya mikewa Maimoon ta rike masa ita da karfi, ya fita da sauri domin kokarin kwace kanta take a hannun Maimoon tana kallonsa alamar so take ta bishi. Tana ganin ya fice sai kwala uban ihu da ya saka a dole Maimoon ta sake ta ba shiri sai ta koma gefen kujera ta rakube tana ta kuka, tun tana kukan da ruwan hawaye sai ga jini na fito mata a idon amaimakon hawaye, babu wanda ya kula a cikinsu, saboda Hajiya Hajara ta ja mijinta gefe ta inda zai kalli TV da kyau, Maimoon kuma tana kitchen tana mulka tuwon shimkafa da tun kamin magariba ta gama miyarsa. Hannu biyu Waira ta saka ta taba jinin dake zubo mata ta kalla, take hankalinta yayi mugun tashi domin bata hawayen jini Eid ne yake hawayen jini idan yayi kuka, kukansa kuma yana nufi abubuwa da yawa abu ne mawuyaci yayi kuka idan kuma yayi to ta ɓace masa ne. Tsafi aka jefata da shi ko kuma Eid ne a cikin wata matsalar wata kila kuma Eid din ne a kusa, ta leka falon tana kallon ko'ina kamin ta dawo ta sake boyewa daga nan kukanta ya tsaya. Tana ta sauren abun da zai sameta.

“Ina take?”

Shi ne abun da Dr Shuraim ya fara tambaya a lokacin da ya shigo falon, Mahaifiyarsa ta fada masa inda take boye. Gurin ya nufa ya lekata har ta zabura sai ta tuna tafiya yayi ya barta sai ta koma ta zauna ta hade fuska ta juya masa baya, shi kam ba ta fushin da take yake ba jinin da ya gani a fuskarta da hannunta ne ya daga masa hankali. Ya aje ledar maganin dake hannunsa da sauri ya kama hannunta yana dubawa.

“Ina kika samu jini?”

Ta kalli hannayen nata, sai ya juya da sauri ya kalli iyayensa.

“Ta jima kanta ciwo ne?”

“Miy faru?”

“Jini ne a fuskarta da hannu”

“Subhanallahi jini”

Hajiya ta karaso tana dubawa.

“Tun da ka fita bata fito daga gurin nan ba, in da ba ta jiwa kanta ciwo ba, to babu wanda ya taba ta, sai dai ko idan ciwon dake hannunta ne”

“No duba da kyau ki gani, babu jini a hannunta ko kadan”

Ya nuna mata hannun, kamin ya shiga yi ma Waira na kurame, yana nuna jinin yana tambayarta da hannu a ina jinin ya fito. Sai ta nuna masa idonta a nan ya maida hankali gurin idon sai ya lura har yanzu akwai sauran jini a ciki dubawa yake sosai ko zai ga inda ta ji ciwo a idon har jini yake fito mata.

“Yarinyar nan abar tsoroce Shuraim ka yi saurin hannata musu ita kar ta mutu a hannunmu, tun da nake a rayuwata ban taba jin mai kukan jini ba amman yau Allah ya nuna min, anya mutum ce kuwa? Idan kuma mutum ce to sun riga sun bada jininta mutuwa zata yi”

Cikin yanayi dake nuna be jidadin maganar Hajiyarsa ba ya juyo ya kalleta.

“Haba Hajiya, yanzu da ace tana ji ai sai ki saka ta shiga tashin hankali, ba a saurin yake hukuci ga abun da baka sani ba”

“To sannu Malam, ga zahiri kana gani zaka ce kar a yanke hukunci ku ji min wani ikon Allah, Doctor ka ga wani abu? Kukan jini yarinyar nan take”

Mahaifin Shuraim ya turo wheelchair dinsa da kansa irin ya karaso gurin da mamakinsa yana kallonta ganin ido yayi mata yawa ya saka ta boye fuskarta.

“Bata son kallo, bari na mata allurar sai na kaita dakin Maimoon ta kwanta”
Chapter 36 · 0% Book details