Sashe 123
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Abiey ya tambaya yana kallon yanayinta, shi kansa ya san ya karya mata guiwa, ya yanke zaren duk wata magana da take dauke da ita, cikin wani yanayi mai kama da rudani ta dube shi ta ce.
“Yaushe Maleek ya fada maka haka?”
“Gaskiya, an kwana biyu amman dai jiya ya nuna min yana son ki sani, shiyasa na fada miki”
“Meyasa baka fada min tun a jiya ba sai yau?”
“Ban samu zama ba, kuma kin ga yau na ga kina cikin farinciki kamar zaki fi jindadi”
Ta mike tsaye tana fara takawa, farincikin da Abiey yake tsammanin gani a fuskarta ya gagara bayyana, damuwa da firgici suka cika mata ruhi, da ace ba mace daya suke so ba, tabbas zata fi kowa farinciki, domin abun da take nema ne ya samu, musamman ma a gurin Maleek da bata taba ganin haka daga gareshi ba. Ta juyo ta dawo ta zauna tana ta kallon wani bangare na dakin.
Wa za'a bawa barwa? Wa za'a hanawa? Dukansu yayanta ne kuma dukansu tana bukatar farincikinsu, ba ma kamar Maleek ashe wata rana zai ji yana son wata a ransa har ya fada? A yanzu ta gane dalilinsa na sakin agogon da yayi a dazun da ta fada masa, sai a yanzu ta gane dan shirin da Maleek yake da Waira na soyayya ne, tabbas zuwan Waira ya canja rayuwar Maleek completely, kuma a yanzu ta tabbatar ya riga Ameer fara son Waira. Samun kanta ta yi da murmushi da kuma hawaye a lokaci daya, tausayinta da kaunarsa suka cika mata zuciya.
“Allah sarki Maleek”
Abiey yayi murmushi.
“Ni na dade da fahimtar haka, kawai dai na barshi ne saboda na san idan ta yi wari zamu ji”
“Amman....”
Sai kuma ta yi shiru ta mike tsaye.
“Ameer ya zo min da makamanciyar wannan maganar”
Mikewa tsaye Abiey yayi ya rike matarsa ganin kamar kafafuwanta ba za su dauketa ba.
“Me ya fada miki?”
“Shi ma makamancin abun da Maleek ya fada maka ne, amman abun da ban gane ba me yasa da Maleek ya ji be fada min komai ba? Kuma be taba nuna min ba? Sai ma takurawa Waira da yake ta wani babin?”
“Amman ke baki alamun yana sonta ba? Ni da nake namiji ma na lura da haka balle ke da kike tare da shi kullum? Ko irin yadda yake kokarin taka mata burgi idan tana hulda da wani ba ki lura da hakan ba? Kishi na cikin kauna, ke ma kuma kin san haka sai dai idan kin manta, kuma rayuwarsa ta sauya a yanzu”
Ummi ta kalli Abiey maganar da yayi mata a yanzu tana kara shiga cikin kanta, ta fahimtar da ita abubuwan da ta manta, da kuma wadanda ta gani bata fahimta ba. Ta san rayuwarsa ta canja zuwan Waira ita kanta ta fadi haka, zuwan Waira ya saka danta ya samu lafiya, a sanadiyar Waira ta fahimci danta na da samuwa har aka masa rokon Allah aka masa saukar qur'ane kuma aka yi masa dawafi a makka duk sa saboda ya samu sauki kuma ya samu.
“Maleek ya dade yana son Waira, sai dai shi ma be san sonta yake a lokacin ba, sai daga bayan nan, wannan dalilin ya saka na zurfafa a binciken danginta, ”
“Amman me yasa be fada min ba sai a yanzu da Ameer ya fada a fili? Bayan kuma ta dade a gidan nan?”
“Ban sani ba, wata kila sun fada a lokaci daya ne, amman suna hankali da natsuwa irin ta Maleek mai tunani bana ganin zai yi hakan a yanzu da Ameer ya nuna yana son Waira, kuma ai Maleek ya fi shakuwa da ita, abun ya zama wani ace suna son mace daya”
Ummi ta kwanta jikin Abiey hawaye na sauko mata, farinciki ya jure mata ya zama bakinciki, domin ba zata raba Waira biyu ta ba wa kowa rabi ba, haka kuma ba zata iya bawa Ameer ta hanawa Maleek da be taba jin soyayyar kowa a zuciyarsa ba sai wannan karon. Ba kuma zata bawa Maleek ta hanawa ďanta Ameer da take ji da shi a yanzu ba, take tsananin kaunarsa bayan ta gama bayyana masa farincikinta da jindadin fada mata yana son Waira har ma ta fada masa zata shige masa gaba a komai, kuma shiri take bukata da shi a yanzu, so take ta bashi farincikin da bata samu damar tsayawa ta bashi a lokacin da yake karami.
“Maleek yana yawan cewa Ameer lalata Waira, saboda yana sonta ne ko kuma dai ya fadi haka a yanzu ne saboda kar Ameer ya aureta?”
“Ya kike magana kamar baki san waye Maleek ba, ai shi ni ya gado bashi da wannan zuciyar ko kadan, ina zaton dai Ameer ya fahimci haka ne shiyasa yake kokarin ganin ya shiga tsakaninsa da Waira, kuma be kama ace suna jayayya akan abu daya ba, musamman Ameer da shi ne babba, wannan shi ya zo daga baya bayan ya gama cewa be san yarinyar ba, ba san inda ta fito ba, da ban rike ta na mata gata ba, wata kila da be ganta ya ce yana so ba a yanzu, hausawa sun ce so so ne amman son kai ya fi, kuma da arziki a gidan wasu kara gidanku”
“Ranka ya dade dukansu yayana ne, zan fi kowa farinciki idan dukansu suka samu abun da suke so, amman a yanzu ban san wa zan dauka ba, farincikin ya zame min bakin hadari da na kasa hango haske a ciki”
“Maleek ya Ameer kaunarta, kuma shi ya kamata ya aurenta zai fi sanin darajarta fiye da Ameer, wata kila shi kyauta ne kawai ya dauke shi, ina gudun kar maganar Maleek ta tabbata ya aureta na dan lokaci daga baya ya nemi rabuwa da ita, kin ga ya lalata mata rayuwa kawai, kuma Maleek ba zai jidadin kin bawa dan'uwansa shi kin hana shi ba, ni kaina ba zan lamunci haka ba, kin fi kowa sanin yadda nake goyon bayan yaya a komai”
Ta lumshe ido tana jin wani kalar abu marar dadi na neman karya mata zuciya.
“Amman zamu iya bata dama ta zabi wanda take so, duk kuwa da na san be zama lallai ta san wanda take so din ba”
“Aa haka be kamata ya kasance a tsakanin yan'uwa ba, da ma da wani ne a waje amman ba yan'uwa da suke jini daya ba, me yasa abubuwa suke zuwa min a haka ne? Abubuwa suna zuwa min da yadda shawo kansu zai zama mai wahala a gareni, kullum zuciyata a cikin kunci take”
Ba tare da ta bude ido ba take fadar haka, sai dai haka be hana hawaye samun hanyar fita daga idonta ba.
“Babu wani abun kunci a nan, kawai mu yi addu'a kuma mu ja hankalin kowa a cikinsu, zan yi magana da Maleek na ga idan har zai zan iya canja nasa ra'ayi, na san abu ne mai wahala amman zan gwada, idan na yi nasara kin ga an huta, sai ya barwa Ameer”
Ummi ta bude idonta ta saki Abiey ta nufi hanyar fita tana jin zuciyarta kamar zata fashe. Maleek be cancanci a gabatar masa da wata a matsayin ya so ta ba, domin be taba nuna son wata ba, sai a yanzu, neman canja masa ra'ayi kuma zai iya sakawa ya dawo da rayuwarsa ta baya, ko kuma ya kara rashin fahimtar dake tsakaninsa da Ameer, wata kila kuma yayi ma Ummi guguwar fahimta zai ga abun kamar ta nuna fifiko akan Ameer ne sama da shi. Ba kuma zata iya tunkarar Ameer ta canja masa ra'ayi ba, yadda yake da wahalar tankwaruwa ma ta san abu ne mai wahala ya amince, kuma zai sake kallonta a wata muguwar uwa wadda ta kasa bashi farinciki a baya, kuma ta kasa sama masa shi a yanzu.
Wai miyasa tuntuni bata kula da alakar dake tsakanin Maleek da Waira ba, da a yanzu haka duk bata kasance ba, da yanzu ta san yadda zata bullowa lamarin, zuwan Ameer ya dauke hankalinta daga komai har bata ganin wata alaka sai ta Ameer da Waira, shi kuma ya cancanci farinciki daga gurinta a yanzu, ta dayan bangaren kuma ta san Abiey fada kawai yake amman ba zai bar vangaren dansa ya zabi Ameer ba, wadda suke yi ma kallon makiyinsu saboda abun da ya faru da Nimra, ga kuma salsalar rashin jituwa dake tsakanin Deen da Abiey, Deen din ya tafi amman Abiey ya kasa jefar da wannan gabar da kiyayyar wata kila shi ya saka har yanzu bw taba tambayar lafiyar Ameer ko kuma zuwa duba shi a bangarenta, tun da Ameer ya sako kafa a gidan Abiey be taba maganarsa ba idan ma ta yi magana ba zai ce uffan ba har aci a sude.
“Wayyo Allah....”
Ta fada tana jinginawa da corridor ta sulale kasa tana kuka marar sauti, gaba daya abun ya rikice mata, ta rasa na dauka ta rasa na zubarwa haka ma ta rasa yadda zata bullowa lamarin.
WAIRA POV.