← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 170

Sashe 25

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanta yayi jikin motar yayi relaxing yana tunanin mahaifinsa, wannan kadai ya isa ya fahimci cewar mahaifinsa yayi masa gata, domin be san duk wannan wahalar ba, idan zai yi tafiya kamin time din tafiyar yayi an shirya masa komai, sannan jirgi yake hawa ba mota ba, sai idan zai isa Airport ko kuma daga Airport zuwa gida ne kawai yake hawan mota sai kuma yawon cikin gari, motar ma sai wanda ta amsa sunan motar da ba kowa ya isa ya hau ba, ya kwanta a gado mai kyau gida mai kyau tufafi baya saka mai karamin kudi, kudin Naija ma idan ba ganin dama ba ba zai rike ba sai Dollars kuma babu mai ce masa dan me? Wani lokacin ma a private jet ma za a kai shi inda yake so na mahaifinsa , tun da yake a rayuwarsa be taba hawa motar haya zuwa wani gurin ba sai a yau. Sai a yanzu yake jin be kamata ya bijirewa umarnin mahaifinsa ba, mi zai saka yayi haka? Why? Gashi makiyinsa ya samu yadda yake so bayan raba shi da abokansa, ya busar da iskar bakinsa ya dago kadan yana kallon hanya sosai yake son yin bachi amman ya kasa saboda babu ac a motar kuma iskar dake shigowa ta gilashin motar yayi masa yawa, abu ne da be saba da saba da shi ba. Haka dai ya daure har suka isa kano. GRA suka shiga direban be sauke shi ko'ina ba sai cikin gidan Hajiya Jamila. Yana fitowa motar ya ciro kudin aljihunsa gaba daya ya mikawa direban.

“Ka kara da wannan”

A firgice direban ya fito daga cikin motar gaba daya ya zagayo inda Ameer yake tsaye ya fadi kasa ya rike kafafuwansa yana masa godiya har da hawayensa, shi kansa Ameer ba zai fadi ko nawa ne kudin ba, balle kuma wanda aka bawa kyautar domin babu wanda ya kirga a cikinsu, sai dai ganin yan 1k da yawa ya san kudi ne mai yawa.

“Ba wani kudi ba ne fa”

Ameer ya fada domin ba ga wani abun godiya da mutumen zai masa ba, akan abun da be taka kara ba balle har ya karya.

“A gurinka ba komai ba ne ranka ya dade, amman ni a gurina kudi ne mai yawa, da tsoro na kawo ka Kano ashe ban sani ba rabo ke kirana, motar nan ba tawa ba ce amman ka ga abun da Allah yayi min”

Ameer ya dan ji wani irin for the first time domin yau ne karo na farko da yayi sadaka, not just sadaka wannan ne karo na farko da yayi ma wani abun kirki kuma har aka masa godiya, this is the first time da ya kyautataw wani. Tabe baki kawai yayi ya nufi cikin gidan da harabarsa ma ta ishe talaka da wani bakauye kallo domin kana ganin gidan ka san Ameer ya isa har ya wuce, a tunanin direban gidansu Ameer ne, shi kuma ya zabi zuwa Kano ne saboda ba zai iya jure tafiya a Abuja a motar haya da babu ac ba, kudin dake aljihunsa ma ya bashi kyautar su ne saboda baya jin zai sake taba kudi mai datti again, daman ya matsu su fita aljihunsa sai yake jin kamar tsukarsa suke.

This is the second reason da yake son zuwa gurin Hajiya Jamila kullum kofar falonta a bude take not like gidansu da sai danna ko ka yi knocking za a bude maka, talkaminsa ne abun da ya fara cirewa sannan ya shiga falon. Hajiya Jamila dake zaune kam carpet rike da carbi ta dago ta idonta dake sanye da gilashi ta kalleshi, a take annashuwa da farinciki suka wanke zuciyarta har suka kasa boyuwa sai da suka bayyana a fuskarta.

“Ameer... Dana....”

Ta fada tare da aje carbin ta mike tsaye ta cire gilashin ta bude masa hannayensa tana masa alama ya karaso gareta, sai ya tsaya yana kallonta.

“Akwai datti a jikina sosai i can't hug you like that, idan na fada miki wahalar da na sha sai kin yi wahala”

Ita da kanta ta karasa inda yake tsaye ta rumgumeshi.

“Ban taba jin kyamarka ba ďana, ba zan taba kyamarka ko kuwa datti duniyar nan zai tabbata a jikinka ne”

Maganar take hawaye na sauko mata, shi kansa ya san Hajiya Jamila tana matukar kaunarsa, kamar yadda yake kaunarta sosai a ransa domin mahaifinsa ya fada masa ita ce second macen da nononta ya kai cikin cikinsa bayan mahaifiyarsa.

“I miss you so much Ammyna and i Love You”

“I love you more Son”

Shi ma rumgume ta yayi sannan suka nufi kujera suka zauna tana rike hannunsa, wani irin kaunarsa take kamar ta bude zuciyarta ta saka shi ta rufe ta hana kowa iko da shi sai ita kadai.

“Ina ka je Ameer?”

“Daddy ya kira ni?”

“Ya kira ni, kuma hankalina ya tashi sosai, Ameer ashe ni ba mahaifiyarka ba ce idan Mr Bashir ya koreka ba zaka iya guduwa ka zo gurina ba? Ka daga min hankali sosai ina ta fargabar abun da ya same ka, duk inda na san zaka iya zuwa na bincika amman ban san samu ka ba, Wayoyinka duk a kashe”

“Ance Daddy be da lafiya da gaske ne?”

Ta daga masa kai.

“Kuma Saboda kai ne Ameer, ni yanzu na yanke shawara tun da har matsala kuke samu zaka zauna a gurina shi kuma sai ya zauna a can tare da matarsa da yayansa, daman ni bana ni da kowa sai kai, kai kadai nake da Ameer Allah be bani kowa ba sai kai kadai”

Jikinta har rawa yake tana taba fuskarsa, akwai wani irin rauni da tarin damuwa a gurin macen da girma ya kamata kuma bata ganin sanyin idaniyarta ba, bata da wani ďa na cikinta sai dan ya sha nononta kamin girma.

“Ina da duk wani abu na jindadin rayuwa da zan baka Ameer, kuma zan jidadi idan ya zabi zama a nan, ko ba komai mahaifinka zai samu space kuma za su daina fada da juna”

“Ammyna kin san ina sonki, amman ba zan iya zama a Kano ba, rayuwata gaba daya a Abuja nake yinta musamman a yanzu da ya kamata na dauki fansa, mun saba na kan zo na dubaki ke ma kuma kina zuwa dubani idan kika yi marmarina”

“Haka ne”

Ta fada ba dan ranta na so ba, sai dan ya zame mata dole ta so abun da yaron da take kallo a matsayin ďanta yake so, tana da ƴaƴan yan'uwa da take riko maza da mata amman bata son kowa kamar yadda take son Ameer saboda ya sha nononta shi ne kadai ďan da ta shayar a matsayin nata ta rumgume shi a hannunta ta yi masa duk wata hidima da uwa take yi ma ďanta.
Ya mike tsaye tare da cire rigar jikinsa

“Ina yan matan gidan nan?”

“Basa nan kasan an koma makaranta duk suna makaranta, bari na shirya maka abun da zaka ci kamin ka yi wanka”

“I hope my room is clean”

“Kullum dakinka a gyare yake Ameer, kullum ina sakawa a gyara shi a saka turare saboda ina saka ran zuwanka a ko da yaushe kamar yadda kake yi ba tare da ka fada min ba”

Yayi murmushi sannan ya nufi hanyar fita falon domin dakinsa ba a cikin part dinsa yake ba, gidan kuma ba bakonsa ba ne.

MALEEK POV.

“No ba sai kin zuba min ba, zan karya tare da yarana”

Abiey ya dakatar da Ummi a kokarinta na zuba masa ruwan zafin da suke ta kamshi. Dagowa ta yi ta kalleshi doguwar riga ce a jikinsa har yanzu babu annuri a fuskarsa, dawowar da yayi ma bayan kauracewa gidan ta yi tambayarsa dalilin haka sai ya fada mata ba komai aikine ya biyo da haka, yanzu kuma yana kokarin kauracewa abincinta.

“Fushi ne har yanzu ranka ya dade?”

“Ke fa kika fada min cewar mu ba yara ba ne a yanzu, to mi zai saka mu yi ta abu kamar yara?”

Yaja kujerar daya saba zama ya zauna, daman ya saba ya kan yi breakfast tare da yaransa irin weekend haka ita kuma ta yi da yan matansa, saboda Maleek da baya kaunar zama kusa da mace ko jin muryarta ko da kuwa mahaifiyarsa ce balle kuma kanenesa sai dole, idan har ana son aga sakewarsa sai idan an bar shi ya kebe da maza yan'uwanshi ko kuma mahaifinsa da kanensa, wannan ya saka Abiey ya ware musu gurin karyawa ko yin lunch saboda Maleek. Ta bude baki zata yi magana Mahmood ya shigo falon sai ta yi saurin hade kalamin ta dauke hannayenta daga teburin ta nufi kofar fita, hakan yayi daidai da shigowar Maleek matsawa yayi gefe domin ya bata hanya ta fita, secondly kuma baya son jikinsa ya taba nata. Tsayawa ta yi kallonsa shi kuma ya sauke kai kasa.

“Ina kwana?”

Bata amsa masa ba sai ta tambaye shi abun da ya fi tsaya mata a rai.

“An gano inda Abokin ka yake Maleek?”

“I don't think so”

In a very law voice ta yi masa maganar, amman hakan be hana Abiey jiyo abun da take tambayar ďansa ba, domin hankalinsa gaba daya yana kansu.

“Ina matukar kaunar yayana, hakan ya saka nake kaunar farincikinsu, ko kadan bana son abun da zai daga hankalinsu ko ya saka su a damuwa”
Chapter 25 · 0% Book details