← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 170

Sashe 134

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ka bata tambayar lafiyarsa? Ka taba cewa Ina Ameer? Me Ameer yake so miye baya so? Me dace mu yi akan Ameer?”

“Yanzu dai ki bar abun da ya wuce ya wuce, tashi muje mu kwanta, kuma likita ya min waya satin nan za ki kwanta asibiti for some months or weeks ya danganta da yadda jikinki ya karbi maganin, idan kin samu lafiya kamin lokacin da ake tsammanin zamu iya dawowa gida ma”

“Lokacin ziyartar asibiti ya wuce kenan, sai dai kwana”

“Hakan kuma ba yana nufin ba zaki warke ba, ko kuma ki dawo gida, kawai mu yi addu'a saukin ya zo a kusa babu cutar da bata da magani ai”

Ya sauko da kafafuwanta kasa ya rikata sai ta mike tsaye ya kwanta jikinta, shi kuma ya daga kansa sama saboda ya hana hawayensa zubowa, yana matukar tausayin matarsa da kaunarta fiye da tunanin duk wani mai tunanina. Da taimakonsa ta fito dakin ta sauko kasa yana rike da ita har suka isa bangarensa, ya kwantar da abar kaunarsa akan gadonsa ya lullube ta sannan ya shiga bandaki yayi alwala ya gabatar da shafa'i da wutiri yayi ma matarsa da yayansa addu'a sannan ya kwanta bayanta ya rumgume abarsa. Washe gari Abiey be bari Ummi ta fito daga bangarensa ba, shi ya shiga bangarenta ya tasa yaransa a gaba daga Maleek har Namra da Mahmood Waira ce kawai aka bari a daki, su kuma suka dunguma zuwa kitchen ko Hanne be yarda ta saka masa hannu a cikin a breakfast din da suke shiryawa ba, kawai so yake yau ya burge matarsa, rabon da ya shiga kitchen irin haka tare da yaransa ko Ummi tun yana da sauran kurciya, kamin ayukan da iyali su fara girma su sauya masa rayuwa.
Hadin girkin ya saka kowanensu nishadi, Namra ta saka wayarta tana musu hotuna da video, kamin ta saka su hawaye tunawa da ta yi da yar'uwarta, tana fadar ina ma ace Nimra tana raye, kusan kowa sai da yayi hawaye har Abiey.
Suna fara jera abinci a dinning Ummi ta iso bangaren, bata a cikin yanayi mai dadi amman hakan ba hana ta murmushi da farinciki ganin iyalanta a haka ba. Abiey da kansa ya ja mata kujera ta zauna. Yana zolayarta wai idan bata bashi rate na 100 ba za su samu matsala.

“Abiey to ai bakai kadai ka yi girkin ba”

“Then n OK da yayana na yi”

Ya amsa yana cire gilashin idonsa. Nimra ta koma gefen Ummi taja kujera ta zauna.

“Toh ni ina bangaren Ummi, saboda na saka hannu girkin yayi dadi”

Ummi ta kalleta tana murmushi.

“Aa daman ni mijina ya iya abinci, tun kamin a haife ku yake min girki”

Sai duk suka sa dariya jin Ummi ta shigarwa mijinta kai tsaye.

AMEER POV.

“Hakan ma abun farinciki ne a gurina, zan gabatar da maganar nan a gurin Daddy sai mu yi abun da ya kamata”

Ya juya ya bude motarsa ya shiga ya barta a gurin tsaye tana bin motarsa da kallo har ya fice.
Har ya isa gida da hannu daya yake driving dayan hannunsa na dafe a kirjinsa, gaba daya ya rasa abun da ke masa dadi ga zuciyarsa sai zafi take. Ya faka a daidai lokacin da motar Daddy ta faka harabar gidan, shi ya bude ya fito Daddy kuma direba ya bude masa ya fito, tsabar hankalinsa da tunaninaa ba a jikinsa suke ba sam be lura da Daddy ba sai kokarin shigewa ciki yake har sai Daddy ya kira sunansa.

“Ameer”

Sai ya juyo kamar a rude ya kalli saitin inda ake kiran sunan nasa. Ganin Daddy ya saka shi hanzarin isa gurin motar, wani abun da be saba ba sai ya bawa Daddy hannu su gaisa, kamar wanda ya tarardar wani abun kunyarsa ba Daddy ba. Kallon tsanaki Daddy yayi masa yana karantar damuwar dake tare da shi, hakan kuma be hana shi mika masa hannu su gaisa ba.

“Ameer me yake damunka? Yau kuma ni kake bawa hannu mu gaisa?”

Ameer ya kalli Daddy sai kuma ya sauke kansa kasa, be san ta inda zai fara fadawa Daddy damuwarsa ba bayan ya gujewa bukatarsa kuma ya kara masa da yin karya. Daddy ya kai hannu ya dafa shi.

“Ameer ďana ban taba ganinka a irin wannan yanayin ba, fada min mw ya faru? Wani abu ya same ka ne ko Ummi? Ko wani ya fada maka wata magana marar dadi ne? Waya jefaka a wannan yanayin? Tell ko miye zan magance maka shi”

Ameer ya hade yawu ya girgiza kai ya soma magana kamar zai yi kuka.

“Ba zaka iya ba Daddy, wani abu ne da kudi baya siya, kyau ilmin martaba ko isa basa siya, kima mutumci da daraja basa siya”

Daga saman kafardarsa Daddy ya gangaro zuwa kasa ya rika hannunsa.

“Zo mu shiga ciki”

Ameer ya jera tare da Daddy suka shiga cikin gidan, sai da suka isa a inda za su zauna sannan Daddy ya sake hannun Ameer ya zauna a kujerar da ya saba zama.

“Ina iya fahimtar halin da kake ciki Ameer, na san damuwarka na san farincikinka, sai dai wannan karon ka shiga a wata kalar damuwa da ta wuce misali, a yanayin yadda ka jera min abubuwan da na za su iya siyen damuwarka su kawo maka farinciki ba sai na fahimci so ne am I right?”

Ya daga kai ba tare da ya kalli Daddy ba.

“Ya sani yi maka karya Daddy, ya maida ni mahaukaci, ya jefa ni a halin da ban taba mafarkin shiga ba, sanin cewar kai ba mahaifina ba ne, sanin abun da Ummi ta yi, gorin da za ayi min da duk wani abun da zan rasa ko na ji, ba kai yadda nake ji a yanzu da na rasa Waira ba”

“How comes ka rasata? Wane irin sake ka yi har ka rasata? Garin ya?”

“Bata sona Daddy, ta fada min kuma na ga haka a idonta, na karanta a kalamanta wani take so dabam ba ni ba”

Daddy ya tashi daga inda yake zaune ya dawo kusa da Ameer ya zauna ya dafa kafadarsa.

“Ameer kana da kyau da asali da kudi da muruba da kwarjini da farin jini da haiba da cikar zati da siffar da ko wace mace zata so ka, ko da kuwa kai baka furta mata ba ita zata so haka, balle kuma ace har ka furta mata ko da kuwa yar zinarice, kasan abun da na dade ina jira arayuwata? Ganin Ranar da zaka zama mai hankali da sanin ya kamata, ranar aurenka”

“Daddy Yarinyar nan ta wuce duk yadda kake tunani, ita bata duba dayan ababen nan da ka lissafa, kuma ta banban da sauran mata, ina ji Kamar babu wata mace da ta kaita kyau da iya mu'alama, Daddy ta dauke hankalina a komai komai ta yi burge ni take i lie to you Saboda ita amman ban a daura mana au...”

Daddy yayi murmushi yana girgiza masa kai.

“Ba sai ka fada ba, na fahimci karya kake tun a ranar da ka fada min haka, kawai dai na saka maka ido ne, shiyasa ban ce maka komai ba, kuma a yanzu na kara tabbatarwa kana son yarinyar nan sosai”

“Amman ita bata so na Daddy”

“Karamar yarinyar ce fa, ina tunanin kamar Safiyya ma zata girma ta, to miye abun mamaki idan tace bata son namiji kamar kai, ita ai bata san so ba, kuma irin sun fi dadin zama domin kai zaka koya mata sonka da kaunarka hankali kwance”

“How Daddy how? Ita bata fahimta tana so na amman na so na aure ba, kuma barin garin zata yi ta fada min, yanzu ma zuwan da na yi na zo ne saboda tace tana son ta musulumta ta hannunna domin ni na koya mata addinin musulumci har ta fahimceshi”

“Wow ka yi abu mai kyau, wannan ma ai first step ne na jefa kaunarka a zuciyarta, baka bukatar fada da wani dan ka burge mace, baka bukatar mace ta tare maka fada dan kasan tana sonka, Saboda ita mace ba a iya mata, zaka iya abun burgewa kuma ita ta ji be mata ba, wata kila ma shi ne silar batawarku, idan tana sonka tana sonka ne ko da kuwa kai kafi kowa zama rago a cikin garinku, idan kuma bata sonka bata sonka ko da ka fi kowa zama gwarzo a garin. Sai dai ta wani bangaren kana bukatar ka yi Gwarjanta saboda ka nunawa duniya kai gwarzo ne, kuma zaka iya a kowane fanni, karka da bata sonka ko tana sonka. Kai da ka maida hankali gurin bi da ita a yadda take so, ka cigaba da dagewa gurin koya mata addinin. Zan yi magana da Imam na Masjid din mu, sai ya fada mana yadda ya kamata mu yi zuwa gobe zamu gabatar da komai”

Ameer ya mike tsaye

“Okay Daddy”

Har ya fara takawa Daddy ya kirashi.

“Ameer”

Sai ya juyo ya kalli Daddy.

“Kai yanzu mai bukata ne a gurin Allah, bachin dare, ba naka ba ne, aikata sabo da duk wani abun da addinin ya haramta ba na mutumen dake nema a gurin Allah ba ne, ka hana kanka bachi ka yi ta fadawa Allah bukatarka ka kai kukanka a gareshi ka fada masa damuwarka, kuma ban ce ka roki Allah ya baka yarinyar ba, aa ka roki Allah ya baka ita idan ita din alheri ce a gareka ka karkarto da hankalinta izuwa gareka, idan kuma babu alheri a zamanku ya yaye maka damuwarta ya musanya maka da wanda ta fita, kuma ya saka maka natsuwar rashinta da kwanciyar hankali, saboda ta fadi bata sonka ko ta nuna karka ya karya maka guiwa, ita mace kamar hawainiya ce mai canja kala, ka ga tsufan Mommy nan ta ku? Da ace ba ni nake aurenta ba zaka iya zuwa da kalamai da hayyala da dake so a gurin namiji kuma ka kwace min ita ta manta da ni idonta ya rufe ta ce sai karamin yaro irinka, saboda haka karka dauki soyayyar mace a banza tun da har ta nuna tana sonka son aurene kawai bata maka, zata fara maka na haihuwa ma soon”
Chapter 134 · 0% Book details