← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 170

Sashe 38

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tausayi take ba shi sosai, ya san zata san wahalar rayuwa a inda zata je, idan ma ta rayu kenan idan kuma ta mutu fa? Kamar yadda mahaifiyarsa tace? Ko kuma yadda yake zargin tsafi za'ayi da ita? Tafiya yayi mai nisa har sai da fita unguwar, gidansa incomplete building ne, be gama ba balle yace ua tafi can ya kwana ba kuma zai iya kwana a hotel ba, gashi baya jin zai iya kaita gurin police din a yanzu idan wani yayi kokarin keta haddinta fa? Yadda take da masifar kyaun nan zata iya jan hankalin wani ya ji yana sha'awar yin alfasha da ita. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya dauki hanyar gidan nasa da yake ginawa gimbiyarsa dake Abuja, da kansa ya fita ta bude gate din ya shiga da motar sannan ya dawo ya rufe gate din, fita yayi ya zagaya side din da take ya kwantar da kujerar ya dagota ta dora masa ya share mata hawayen, babu haske a gidan a dole ya bar hasken motarsa a kunne ya kunna na wayarsa. Ita dai kallon gurin kawai take ya dauko carpet ya shimfida a gafenta ya zauna kasa ya jingina jikinsa kusa da kujerar da take zaune saboda ta samu natsuwa. Be daga daga gurin ba har sai da aka yi sallah Isha'i be sha wahala samun ruwa da bula ba saboda akwai rijiya a gidan, kuma akwai butocin da masu aiki suke amfani da su su yi sallah ko kama ruwa a duk lokacin da aikin ya kawo su, da kansa ya bude rijiyar ya debo ruwa ya zuba a bukatar yana juyowa sai ya ganta tsaye bayanshi, murmushi kawai yayi ya zauna bakin rijiyar yayi alwala ta sake biyoshi har inda ya aje carpet din dake ta zauna a kasa tana kallonsa har ya gama Sallah. Rikata yayi ya maida ita cikin motar ya rufe, sannan ya zagaya side dinsa ya shiga ya zauna ya rufe bayan ya kwantar da kujerarsa. Juyowa ta yi tana kallonsa sai ya sakar mata murmushi, be ce mata uffan ba ita ma ba ta iya magana da yarensa balle ta fada masa abubuwa da yawa dake son bawa wani labari. Sai karfe tara Hajiya Hajara ta kira wayarsa da gangan yaki daga wayar har sai da ta yanke sannan ya saka ta plane mode, ita dai kam ban da aikin kallonsa babu abun da take har bachi ya dauketa daman a gajiye take kamar wanda ta yi yakin duniya. Bachi tai sosai sai dai ta yi shi a takure saboda ba gado ba ne kuma ba tabarma ba, a cikin mota ne duk yadda ta so ta wala ba zata samu haka ba, bata farka ba sai da ya tashe ta da kanshi, sai ta bude idon a hankali ta kalleshi sannan ta tashi zaune. Fitowa yayi da kafafuwanta ya rike hannunta ya kaita inda zata yi fitsari ya aje mata buta, yana juyowa sai ita ma ta juyo bata saba sarki idan ta yi fitsari ba balle ta gane cewar fitsari yake nufin ta yi. A kokarinsa na fahimtar da ita ya saka hannunsa a daga rigarta ya dukar da ita, sai ta fahimci manufarsa, mikewa ta yi tsaye sai ta juyo ta kalleshi, ganin hakan ya saka ya juya baya sanin idan yayi nisa zata iya cewa ba zata yi fitsari ba. Tashi ta yi ta zo gabansa ta tsaya tana dage sai ta saka hannunta daya ta rufe masa ido daya, a take rufe idon gaba daya yana murmushi, ta daga hannunsa ta kai gurin kunnensa, sai ya saka hannu biyu ya rufe kunnensa.
Dawowa ta yi ta yi fitsari a inda ya nuna mata Hankali kwance, bata jin kunyar aga cikinta ko wani bangare na jikinta, sai gabanta da kirjinta, daman a gurinsu kirjin mace da kasanta ne a abun kunya a gurinsu, shiyasa gurin kawai suke damuwa su rufe, a gurin namiji kuma kasan ne kawai abun kunya, wannan na daga cikin dalilin da ya saka mazan garin basa damuwa da saka riga ko tufafin da zai sitirta jikinsu. Bata yi tsaye ba ta mike tsaye ta ja wandonta sannan ta dawo gabansa ta tsaya, shi ya ji cewar ta gama ya bude ido, juyawa yayi ya dauko butar ya mika nata yana mata alamar yadda zata gage cewar ta wanke fuskarta da baki, sai ta girgiza kai daman wanke baki ko fuska idan an tashi da safe ba al'adarta ba ce, yana daga daga cikin abun da ta tsana. Juyin duniya yayi Waira ta ki yarda ta wanke bakin nan nata daga duniyar kazanta, shi kan mamaki kawai yake daman haka take fama da kazanta ko kuma koya mata aka yi. Mota ya saka ta sai ta sake zaunawa irin zaman da ta saba idan ta shiga mota ta zauna a kasa, ta rufe ido bata dago ba har ya isa gurin masu siyar da fruit kasancewar da safe be samu wasu abubuwan ba, sai lemu da abaya ya siya mata, ya sake shiga motar yana sauke ajiyar zuciya. Sai a lokacin ta bude ido saboda ta ji kamshin abaya. Zobensa na azubarfa ya cire ya mika hannu ya dauko rigarsa ta yaga ya saka zoben yayi mata sarka da shi ya saka mata a wuya, sannan ya dauki diary sa da biro yayi rubutu akai ya mika mata, ta karba ta rike. Ya ja motar suka nufi CID office, fita yayi ya zagaya gefenta ya fito da ita ta dauko maganinta da kayanta ya mika mata kayan maganin da ledar kayan marmarin daya siyo mata kuma sai ya rike ya rufe motar yaja hannunta sai taja ta tsaya tana kallon gurin, a gurin ya barta ya shiga ciki yayi musu bayani sannan ya bukaci mai uniform din gida ya zo ya rikata kuma kar a shiga da ita gurin saboda zata tsorata sosai. Haka kuwa aka yi dayan ya cire uniform dinsa ya saka kayan gida bayan Dpo ya ba shi umarni saboda kawo ta da Dr sai da yayi musu karyar cewar Tiyata zai shiga kuma yana tsoron kar azo daukarta ba shi kusa. Dr Shuraim ya mika masa maganin sannan yayi masa bayanin abubuwan da take ci, sannan ya mika mata ledar fruits din ya nuna kanshi yana gabatar mata da sunanshi.

“Sunana Shuraim, sai wata rana”

A nan ta saka hannunta mai ciwo a kirji ta nuna kanta.

“Waira....”

“Waira....”

Ya maimaita sai yayi murmushi ya mike tsaye yana nata waving, zuciyarsa na masa babu dadi, ji yake kamar kar ya rabu da ita, kuka ne kawai be yi ba amman sai da idonsa suka cika da kwalla, he thought za ta yi ihu tace zai ta biyo shi, sai ga tsabanin haka ta tsaya a inda ya barta tana kallonsa babu kuka babu hawaye sai dai ta ki dauke ido akansa har sai da ya shiga motarsa sannan ya saki ledar fruit din dake hannunta. Tana jin kewarsa ta fahimci fada ake masa tun jiya hakan ya saka bata takura cewar dole sai ta bishi ba, tunanin zai tafi ya barta ya saka ta manta da tsoron mota take, tana kallonsa har ya fice daga harabar.

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

20

A gurin ta risina tana kuka dafe da fuska, coworkers dinta suka rika bata hakuri dayar ta rikata ta kaita restroom ta wanke mata fuskarta.

“Wai miya hada ku?”

Bakin ciki da masifa irin na Humaira sai ya yana ta fada mata komai, da zarar ta bude baki ta yi magana sai ta fashe da kuka, ta girgiza kai, ta san ita talaka ce mai nema a karkashin wasu saboda ta taimaki iyalinta, amman hakan ba zai saka ta dauki wulakanci ko kaskanci a gurin kowa ba, bata taba wulakanta wani ba, hakan ya saka idan aka wulakanta ta abun yake mata ciwo.

“Da gaske shi dan mai gurin nan ne?”

Shi ne kawai abun da ta iya tambaya, tana dafe zuciyarta saboda bakinciki dake taso mata.

“Bana jin haka, ni ban ma taba ganinsa ba sai yau”

Ta lumshe idonta hawaye na sauko mata kamar ba gobe, fitowa ta yi daga gurin ta dauki katon hijab dinta ta saka, ta dauki yar karamar jakarta da take sako tarkace a ciki.

“Humairah ba zaki tafi da abincin ba?”

Ta juyo ta kalli kawarta Muneera, tun da ta kama aiki gurin bata da kawa irin Muneera sun shaku sosai kusan duk wani abu daya shige mata duhu ita take nema shawara ta warware mata. A ka'ida idan za su tafi gida suna raba abincin daya rage a gurin ne, mai gurin ya fada musu idan har an raga abincin to su raba tsakaninsu kowa ya tafi da shi gida, saboda ba a dumamane abincin da safe idan kuma aka bar shi nan zai lalace ne kawai. Duk wadanda suka yi duty dare ana kaisu gida ne da motar gurin, saboda fadin garin Abuja wasu a kusa suke ba, Mr Bashir yana musu haka ne a kokarinsa na kyautatawa kowa a zaman da suke a gurin, ana canjin duty idan wadannan sun yi da safe na sati sai a canja wasu su yi na yamma ko dare ko rana, kana ana canja su daga wannan gurin zuwa wani dabam.

Kai ta girgiza mata alamar ba zata tafi da shi ba, saboda bakincikin abun da aka yi mata a yau ya rufe mata ido bata iya ganin komai, daman can haka take ba kasai take jan mutun fada ba, amman ko harararta ka yi ba zata kyale ba. Muneera ta matso kusa da ita ta rumgume ta ganin har lokacin hawaye take.

“Wai miya faru ne Humairah me kika masa?”

“Akwai wata hanya ta kai kara”

Ta tambaya so take ta kai kararsa idan har da gaske dan mai kamfanin ne ya kamata mahaifinsa ya san abun da ďansa ya aikata mata. Arzikin ďaya bata kone ba amman har yanzu fuskarta zogin zafin tea take da kuma marin da ba a taba yi mata ba.

“Idan ma akwai ai ba za a masa komai ba, dan mai gurin ne fa?”

“Da gaske dan mai gurin nan ne?”
Chapter 38 · 0% Book details