← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 170

Sashe 6

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gefen wasu manyan itatuwa ya faka motarsa, nesa da wata motar yan mata guda biyu dake zaune gefen motarsu sun shimfida carpet suna ciye ciyen kayan kwalan da maskulashe. Fitowa yayi rike da da sarewarsa a hannu ya hau bayan motarsa yana ta kallon titi da babu motoci sai jefi jefi, har lokacin zuciyarsa tafasa take tana wani tiriri, be taba jin kaskanci da wulakanci ba irin na yau da Maleek ya tofa masa miyau a fuska, Ameer yana ganin babu wanda ya isa yayi masa wulakanci ko ya tozarta shi sai dai shi yayi ma wasu, amman a yau Maleek ya masa kuma a gaban friends dinsu.

“Tun da ka fara sai ka karasashi Maleek sai ka kai kasa da guiwoyin ka kana ba ni hakuri Maleek”

Har wani tauna hakora yake yana furzar da numfashi da karfi kamar shi yayi masa laifi. Ya dade yana kallon sarewar dake hannunsa sannan ya kaita bakinsa ya fara busawar irin busar da babu wanda ya iyata a isa saninsa sai shi da wanda ya koya masa, yana jindadin busar sarewa ko wace kala ce balle kuma wannan da take ta musamman a gurinsa, tana saukar masa da nishadi a duk lokacin da yake yinta, lumshe ido yayi yana busar cike da karewa. Fararen yan matan dake zaune gefen motarsu suna motsa baki suka fara kallon junansu da mamaki, kamin su mike tsaye suna lekonsa.

“Wow.... Nimra kin ji wannan?”

Dayar ta fada tana kallon dayar dake kokarin rufe kanta, sai duk suka yi murmushi suna jin yadda busar ki tsara iska tana shiga kunnuwansu kamar ana musu susar kunne. Wanda aka kira da Safna ce ta fara daga kafa ta taka zuwa gurin motarsa tana lekensa, kamshin turaren da ya ji ya banbanta da na shi ne ya sanar masar akwai wani bakuwar hallita a kusa da shi, a take ya daina busar ya bude idonsa a hankali, wani karamin yaki ya murza da idonsa da zuciyarsa dake mugun bugawa da karfi kamin ya samu nasarar kawar da idonsa a cikin kwayar idonta.

“Ya aka yi?”

“Busa muka ji kana yi mai dadi”

Ta fada tana kallonta with smile on her face, shi ma murmushi yayi kamar ba shi ba, ya dan daga kafada sannan na sauko saman motar, ba tare da ya sake cewa komai ba ya bude motarsa ya shiga ya bar ta a gurin tsaye.

WAIRA POV.

Al'adarta ce yin rawa ko babu kida hakan ya saka ta sauko tsaunin da ta hau tana taka rawar kamar yar makada. Eid ya karaso gurin ya mika mata hannunsa ta rika ta karasa saukowa.

“Abinci zan ci yanzu”

Ta fada da yarensu, ya gyada mata kai.

“Mu je gida mu ci”

“Lambu zan je”

Ta sake hannunsa ta nufi hanyar da zata sadata da lambun da gudu tana gudu tana tsalle har ta isa, bata bi ta kan yayan itatuwan da suke take akan itacecen ba ta fara daukar wadanda suka fado kasa tana ci, wani ma tsuntsaye sun ci shi amman bata damu ba take ci haka nan, ba tare da ta wanke ba sai dai wanda ta tauna da ji da kasa sai da zubar.

“Da kin wanke dai Waira”

Ta juyo da sauri domin ta firgita bata san da mutum bayanta ba, ganin Eid ya saka ta lake kafada daya ta fara yin baya baya.

“Atud shie”

Be ma'ana ba zata wanke ba, shi ma dai ya san fada kawai yayi domin bata da kyama ko kadan, kuma bata da tsabta ita da kasanza kamar twins ne, da za a bashi neman wani abu da Waira ta wanke shi kamin ta ci am ba shi babban aiki, komai kazanta guri zata iya kwana kuma ta tashi ba tare da ta wanke jiki ba, wannan ya saka dakinta yake cike da beraye da jajayen zakaru da wani lokacin ma a tare take cin abinci da su, basa tsoronta har rufa take dasu idan zata kwanta, berayen kam ta sha saka su a aljihunta ko a rigarta tana yawo da su. Tun abun yana damun Eid yana mata magana har ya gaji ya fara saka mata ido, domin ba zai iya canjata daga yadda take ba, haka kuma ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma yawan yi mata magana yana saka su yin fada.

Sai da ta ci yayan itatuwan ta koshi sannan ta samu guri a bakin magudanar ruwan dake lambun da zauna tana kallon yadda ruwan suke tafiya, Eid ya tsaya kusa da ita yana kallon ruwan shi ma, kamin ya shafa kanta.

“Zan tafi gurin Sarki, sai na dawo”

Ta daga masa kai ba tare da ta kalleshi ba har ya bar gurin, kwantawa ta yi tana kallon saman da gira gizai ba su gama wawayewa ba.

ABIEY's HOUSE.

Ta aje dankunne data cire a kunnenta saman mirror sannan ta juyo tana gyara rigar bachinta, Abiey dake kokarin rufe kofar bathroom ya kalli matarsa, da fuskarta ke bayyana damuwarta karara.

“Lafiya?”

Zaunawa ta yi gefen gado, sai ya zo kusa da ita ya zauna, a kan kananan kitson dake kanta ya fara sauke ido sannan ya kalli fuskarta.

“Bana son gani damuwa a tare da ke, Zahra ko abu be taka kara ya karya ba sai ki dauke shi ki saka a rai, yanzu kuma me aka yi?”

“A gurin ka wata kila ba wani abu ne ba, amman ni na san abun da nake ji, kullum cikin jarabawa nake Abiey, kamin na same ka na sha wahala na fuskanci bakinciki na yi kuka kala kala, bayan na aureka na dauka damuwata ta wuce na dauka zan dauwawa a farinciki ne, sai dai daga lokacin da Maleek ya fara girma ya tsane ni sai na gane damuwa ba zata kyale farinciki ya zauna shi kadai ba, ina ganin kamar kiyayyata ce ta saka Maleek ya tsani mata gaba daya”

“To me kika masa da zai tsane ki? Wannan wace irin magana ce? Kin tana ganin ďa ya sani uwarsa?”

Ta juyo ta kalleshi hawaye na zirya a fuskarta.

“Wata kila saboda abun da na aikata ne, hakki ba zai bar ni ba Abiey, na ha'inci wasu kuma na cutar da kaina”

Ta fashe da kuka mai karfi, ajiyar zuciya Abiey ya sauke ya dafa kafadarta yana girgiza ta.

“Ki cire wannan a ranki, babu wanda kika ha'inta, Maleek ma zai daina komai yana da lokaci ai, dan Allah ki daina kukan nan”

“Babu abin da ke da ke da bakinciki kamar ďan ka yana cikin damuwa ka fuskanci ka tambaye amman ya kasa fada maka, Abiey ni fa uwa ce ni kadai na san zafin da zuciyata take min”

Ta fada tana nuna kanta, mikewa yayi tsaye ya fito daga bangarensa ya shiga bangaren matarsa, sai ya samu Mahmud zaune tare da kanwarsa yar'uwarsa Namra.

“Daddy”

Nimra dake kofar kitchen rike da cup ta fada tana kallonsa, sai duk suka juya suka kalleshi domin ba su san da shigowarsa falon ba, gaishe shi suka yi, ya amsa da murmushi a fuskarsa.

“Ina Maleek?”

“Yana ďakinsa, Daddy ai kasan idan mu nan falo ba zai zauna ba”

Be ce musu komai ba ya nufi upstairs, cikin natsuwa ya tura kofar dakin dansa ya shiga sai ya same shi zaune yana karatun kur'ane gaba daya ya cika dakin da muryarsa mai dadin sauraro. Abiey ya karasa ya zauna akan kujerar dake kusa da inda ďansa yake zaune saman carpet, Maleek na ganin haka ya rufe qur'ane bayan ya kai ayar karshe.

“Abiey...”

“Maleek karatu ake yi?”

Yayi murmushi ba tare da yace komai ba.

“Hakan yana da kyau ai, Allah ya kara basira, Umminku ta fada min kana da damuwa, sai kuma na zo na tararda kai rike da abun da ke kawar da damuwar, kusa da mai kawarda damuwar, sai dai duk da haka ba zan ki mu tattauna matsalar ba”

Maleek ya sake fadada fuskarsa da murmushi mai kyau ya gyara zamansa.

“Abiey gashi kai ma ka fadi, damuwa ai ta wuce saboda hada ta da mai iko da ita, kuma daman ba wani abun ba ne, fada ne kawai muka yi da wani friend dina shiyasa na dawo gida rai a bace, ita kuma sai ta dauka ko wata babbar matsala ce”

“Ka tabbatar ba matsala ce ba?”

“Babu wata matsala Abiey, kawai akan yayi min maganar mata ne ni kuma rai na ya bace na yi masa abun da be dace ba, wanda na ji ba dadi bayan yi masa haka, amman abun ya wuce”

“Sai da na raya wannan a raina na san ba zai wuce akan wannan issues ba, amman a rika kiyayewa be kamata kana samun matsala da abokinka ba, su ma kuma ka fahimtar da su rayuwarka so that's kowa ya ya daina taba kowa”

“In Shaa Allah”

Abiey ya shafa kan ďansa sannan ya mike tsaye.

“Allah ya muku albarka”

“Ameen”

Ya amsa yana kara jin kaunar mahaifinsa.

___________________

Wace kalar ramuwa kuke tunanin Ameer zai yi?
Su Waira manya, team kazamai ku zo ku dauki yar'uwarku 🤣😂

*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

_Na Khadeeja Candy_

4️⃣
Chapter 6 · 0% Book details