← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 170

Sashe 112

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta mike tsaye tana wani rangaji kamar zata fadi, hankalinsa sai ya dauku akan karta je hawan stairs ta fadi kasa, dan haka ya bi bayanta be matsake ta daf ba, sai dai damuwa da yayi da karta fadi ta kai kasa ya saka shi tsayawa a space din idan zata fadin ma zai iya tareta, haka ya bita har sai da ta shiga dakinta ya tsaya bakin kofa tana fadawa kan bed ya kashe wutar dakin ya janyo mata kofar a hankali. Dakinsa ya nufa he can't tell why yake damuwa da ita, at first yana tsoron kar Ameer ya bata mata rayuwa ne, yanzu kuma ya gane ba tsoro ba ne kawai har da tausayinta yana yi, na rashin wani gata sai su, bata da family sai su, da ace Ummi zata koreta a yanzu a bata da wani gurin zuwa sai da ta shiga wani hali.
Sai 11pm ya saka tufafin bachinsa sannan ya kashe first switch na dakin, ya kashe bedside lamp yana kokarin kwanta daga zaune da yake sai ya ji kamar akwai mutum a gefensa, ya kai hannunsa ya taba sai ya ji ya taba jikin mutum amman akwai gashi da sanyi sanyi a jiki, da sauri ya kai hannu ya kunna bedside lamp din ya juya be ga kowa ba, ya kai hannu ya taba gurin ya ji babu komai, for the second time ya kashe wutar ya kai hannunsa ya lalaba ko zai sake jin wani abu amman be ji ba. Gaba daya ya kunna wutar dakin ya tashi zaune da kyau yana kallon gadon, be taba jin wani abu makamancin wannan ba gidan gaba daya balle kuma a dakinsa. Ya duba hannunsa ya jimke hannun ya bude yana mamakin me yaji haka? Ya sauko da kafafuwansa kasa ya zauna bakin gadon kamin ya tashi ya nufi bandakinsa alwala yayi ya fito ya sake zama a inda ya zauna dazun ya sake kashe first switch na dakin ya dauki wayarsa dake gefen gadon ya bude qur'ane application dake ciki ya karanta Suratul milk, bayan ya gama yayi addu'ah ya kwanta ba tare da tsoron komai ba. Haka nan kawai bachi yaki daukarsa, jikinsa kuma yaki yi masa dadi daga kwanciyar da yayi, a dole sai da ya tashi ya jigina da kan gadonsa ya dauki wayarsa dan rage dare, sai gashi ya shiga Whatsapp yana duba sakowannin da be shirya amsa sako ko daya ba, ya fito ya leka Instagram ba shi da wani abun yi a gurin dan haka ya fito ya sake komawa Whatsapp, sai dai wannan karon status din mutane yake kallo, kamin ya shiga camera dake status nasa, daman he update a status on whatsapp once in awhile, kara ma Insta ya kan dora hotonsa time to time musamman a lokacin da suke yawan zama tare da abokansa. Yana shiga camera hoton Waira ne first abun da ya fara cin karo da shi domin shi ne last picture da ya sauka a wayar, he can't tell what take him so long zoom the picture yayi ta kallon kamar wani da be taba ganinta ba

*** *** ***

Can cikin bachinta mai nauyi ta ji ana kokarin saka mata hannu a cikin rigar dake jikinta. Yanayin sai yayi mata kamar mafarki take dan haka ta kara gyara kwanciyarta tana sake jiki ba tare da ta sani ba. Hakan be wadatar ba har sai da ta ji ana tashinta daga bachin tare da kiran sunanta da muryar da ta haddace tun farkon zuwanta gidan.

“Waira... Waira... Waira...”

Ta amsa cikin magagin bachi sannan ta bude idon daker, arba da ta yi da fuskar Maleek ya saka ta tashi zaune da sauri tare da buge masa hannunsa dake cikin riga yana kokarin kai wa ga kirjinta.

“Ya Maleek”

Ta fada tana matsawa baya da sauri sai ya haura saman gado da wata kalar fuska shi ba dariya yake ba, kuma ba murmushi ba, ba kuka ba da damuwa ba, haka ma fa far'ar ba ba kuma kishiyarsa bakinciki ba. Still hannunsa yake son kaiwa ya taba kirjinta abun da ba taba mata ba, bata san haramci hakan ko halacci ba, sai dai tana jin abu na wani yanayi na dabam saboda abu ne da bata saba da shi ba, wani be taba kwatanta yi mata haka ba. Sai ta kara matsawa baya taba bata fuska kamar zata yi kuka gashi tsoron take yace ta masa ba daidai ba, if not she will talk ta fada masa bata so. Ganin damuwa a fuskarta har idonta ya fara tara kwalla ya saka ya rika hannunta ya sumbanci hannu ya shafa goshinta zuwa saman kanta sannan ya sauka saman gadon ya fice daga dakin, mamakin abun da yayi mata ya hanata bachi har karfe 4am na asuba, sai 4:30 ta sake komawa bachi, bata farka ba sai da Ummi ta shigo ta tasheta, sannan ta tashi ta yi shirin makaranta ta sauko tana sanye da uniform dinta tana rike da jakarta ta makaranta. Idonta na kan Maleek dake shan ruwan sanyi tun da farar safiya har ta sauko ta isa dinning.

“You didn't greet him”

Waira ta daga kai tana masa wani irin kallo da ita kadai ta san manufarsa ta gaisheshi. Kamar kar ya amsa mata sai kuma zuciyarsa da baki suka ki bashi hadin kai har sai da ya amsa din. Ummi ta aje mata komai na karyawa sannan ta aje mata lunch box dinta a gefen kujerar dake fuskantar wadda Maleek yake zauna.

“Baki gaishe da Namra ba”

Ummi ta fada, sai a lokacin ta lura da wata Namra a gurin, domin tuni tunaninta ya tafi akan abun da ya faru a tsakar daren jiya.

“Ina kwana Yaya Namra”

“Lafiya Kalau”

Ta amsa sannan ta dauki kofin tea ta ta bar dinning din domin ta gama bata karin, a nan Waira tace waye tv na ba Maleek, kallonsa take kamar zafa fada cikin idonsa, duk dagowar da zai yi da wani motsi yana kan idonta ta ma kasa taba komai a abin karyawarwa da Ummi ta aje mata, tun be kula da kallon ba har jikinsa ya bashi cewar kallonsa take, dan haka ya dago idonta da nashi suka yi tarayya da juna, a madadin ta dauke idonsa sai ta cigaba da kallonsa. Zuciyarsa ce ta fara raya masa kallon da take masa ba na Allah da Annabi ba ne, dan haka ya sake kallonta.

“What?”

Ya tambaya da wata murya can ciki, sai ta dauke idonta domin bata da amsar bashi. Kadan ta sha tea ta mike tsaye tana duba agogo dakin dake nuna 7:30am.

“Ummi zamu wuce makaranta, Ameer be tashi ba?”

Maleek ya hade tea dake bakinsa da karfi, yana jin kamar an daka masa wani mashi a zuciya, why ma ya zauna yana karyawa at this early morning abun da ba halinsa, mikewa yayi tsaye yaja kujera baya ya fice daga dinning din.

“Be farka ba, ni kuma na kyale shi yayi bachinsa ne saboda shi ne first bachinsa a gidan nan, kuma idan ma ya farka this time around me zai yi? Ai kara yayi ta bachinsa, idan ya farka zamu tafi tare anjima na duba matar nan da ta yi accident, shiyasa na hada komai tun a yanzu kuma ina son kamin ya farka na gama shirya masa komai na karyawa even though ban san favorite dinsa ba”

Ummi ta fada tana dire flask din ruwan zafi daya banbanta da sauran Flask din da suke gurin. “Zan tafi na san school bus ta iso a yanzu”

Ummi ta zagayo bangare da Waira take tsaye ta sumbanci goshinta.

“Allah ya miki albarka a dawo lafiya, ki dauki lunch box dinki, na ga baki ci komai ba ma”

“Okay”

Ta amsa sannan ta dauko lunch box din, kiss din da Ummi ta yi mata yana tuna mata da irin kiss din da Maleek yayi mata a daren jiya. Ummi kuma ta yi tsaye tana kallon Waira fuskarta da murmushi har ta fice, ta juya zata koma kitchen sai ta ji jiri ya kwasheta, ko wane gaba na jikinta ya fara rasa kamar ana dukan kashinta, da sauri ta dafa dinning din ta zauna a hankali har sai da abun ya sake ta sannan ta mike tsaye cike da karfin hali ta nufi kitchen din domin karasa abubuwan da take son shiryawa Ameer.

****** ******** ******* *******

Ummi bata samu zuwa duba matar da Ameer ya fada mata tana asibiti da safe ba, sakamakon kiran da Mummy ta yi masa ta sanar masa ta yi aika musu da breakfast, shi kuma ya sanar da Ummi a lokacin da ya sauko kasa domin yin breakfast. Ganin Mahmood a dinning make him feel uncomfortable, but ga mamakinsa sai Mahmood ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya tashi daga dinning din yana fadin.

“Bari na baka guri ka karya kamin ka saba da mu”

Ameer dai be ce masa uffan ba, ya cigaba da kallon kalolin breakfast din da Ummi ta shirya masa tare da taimakon Hanne.

“Ban san favorite dinka ba, shiyasa na girka wadannan ina fatar za su maka dadi”
Chapter 112 · 0% Book details