← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 170

Sashe 50

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahmood ya girgiza kai.

“Haba Ummi wane irin aljana kuma? Yadda Maleek ya tsani mata har wata aljana ta samu damar aurensa?”

“Maybe ita ta saka mishi tsanar matan ai, wani mafarki na yi da ya ba ni tsoro...”

Jerawa suka yi suna tafiya tana labarta masa yadda ta yi mafarkin.

“Mafarki ba gaskiya ba ne, kawai dai dan kin saka abun a ranki ne ya saka kike yi mafarki, Ummi damuwata yanzu ciwonki ne yaushe zaki ga likitan? Kuma wane likitan ne yake dubaki, ba a wasa da ciwon nan”

“Sai na gama da matsalar Waira”

“And Ummi miye reason dinki na boye wannan sirrin ciwo ne fa”

“Bana son na tashi hankalin Babanku, kuma bana son hankalin Nimra da Namra ya tashi har da kai, dan dai Maleek na san ko ya rasa ni ba zai yi bakinciki ba”

Ta karasa a lokacin da Mahmood ya kai hannu ya tura kofar dakin da Waira take ciki.

“Maleek yana sonki Ummi, kawai dai wannan ciwon ne na kyamar mata ya saka shi nesantarki amman abun na masa ciwo, ya fada min haka kuma yace baya iya ayyana rayuwarsa idan babu ke, addu'a kawai ya kamata mu yi masa komai zai wuce”

“Kuma dole mu tashi masa tsaye, domin mafarkin nan da na yi jikina na bani kamar gaskiya ne in ba haka ba miyasa na ga Waira a mafarki har tana fadar wai kasheta za'ayi ban san ko suwa za su kashe ta ba”

Ummi ta zauna bakin gadon tana kallon fuskar Waira dake bachi.

“Akwai abun da yarinyar nan ta gani dazun tun da har gashi ta nuna”

Mahmood yayi shiru saboda baya son musawa Ummi. Ba shi kadai ba Abiey ma da ta labarta masa mafarkin a waya ta fada masa abun da ya faru be yarda ba.

“Mafarki ba gaskiya ba ne, kowa da yadda Allah yake halittarsa ku mata komai sai ku rika cewa aljannu ne, mun bincika abun nan a likitance an fada mana cewar halittace da Allah yake halittarsa kowa da irinsa”

Ta sauke ajiyar zuciya daman ta san ba lallai ne ya yarda ba.

“Hiayatee ki kwantar da hankalinki dan Allah komai zai wuce”

“Haka zamu saka masa ido ba tare da komai ba? Kullum sai dai ka ce min komai zai wuce when?”

Ta fashe masa da kuka kasancewar dakin babu kowa sai ita kadai da Waira dake bachi har lokacin, Mahmood tuni ya fice daga asibitin zuwa gurin aikinsa.

“Bari ki dawo sai mu zauna mu yi maganar abun da ya kamata, zamu saka ayi addu'a kuma muma zamu dage da yi har da sadaka idan ta kama har gurin dakin Allah sai aje ayi masa addu'a shikenan?”

“Eh amman da kullum baka yarda da zancena sai ka rika cewa komai zai wuce”

Daga can cikin wayar yayi dariyar manya, wadanda ke nishadi da matansu ya san halin sahibarsa tun kurciya na dawainiya da ita har zuwa yanzu da girma ya kama.

“Haba Madam yanzu ai na zubar da makaman yaki na ce za'ayi duk abun da kike so, kina asibitin har yanzu?”

“Eh ina son na tafi gida yanzu sai Hanne ta zo ta zauna da ita”

“Ya jikin nata? Likita ya fadi wani abu?”

“Sun duba komai a game da jinin idonta ba su ba mu sakamakon ba har yanzu, amman cizon dake hannunta sun ce da sauri tana da kyau jini, kuma likitan da ya duba da farko ya iya aiki shiyasa abun ya zo da sauki, sai dai yace duk da haka za su bata gado ta zauna har sai ta samu sauki gaba daya”

“Toh Allah ya biyaki, ita kuma ya bayyana mana iyayenta kuma ya shirya mana na mu yayan, ya nuna mana aurensu da yayansu a tare”

“Ameen... Abiey Ameen... Allah ya amsa....”

Ta amsa tana jin wani iri a zuciyarta, gani take kamar ba zata ga lokacin ba.

“Amman dan Allah ki saka ido akan yaran nan, bana son a samu wata matsala kuma ke ma ki kula min da kanki yawam tunani da damuwa ki ciresu kin fi kowa sanin yadda nake son farincikinki”

“Allah ya ba ni iko”

“Ameen, to sai na dawo?”

“A dawo lafiya Habibi”

“Allah ya sa”

Ya aje wayar, ita ma ta sauke wayar idonta na cika da kwalla, number Maleek ta lalubo ta danna kira ta saka hands-free. Ringing ďaya ya daga kamar yana jiran kiranta.

“Hello Ummi...”

Ya fada muryarsa har rawa take, sai da ta rumtse ido ta bude sanin uwa bata fushi da ďanta ta amsa masa.

“Na'am”

“I'm sorry ki yi hakuri da abun da ya faru bana nufin bata miki rai, ban san mi ya zo kaina ba kawai na samu kaina da bacin rai ne marar misaltuwa”

“Ba komai kana gida?”

“Aa na fita”

Ta yi shiru tana saurarensa sannan ta ce.

“Maleek ina son na tambaye ka, akwai mafarkin da kake ko kana ganin wani abun?”

Ta san it's not the right place ta yi masa tambayar, sai dai bata da zabin da ya wuce haka saboda baya zama da ita idan kuma ya dawo gida ba zai amsa mata tambayar ba.

“Ban fahimta ba”

“Baka mafarkin komai?”

“Ina mafarki kamar yadda kowa yake idan ya kwanta”

“Okay idan ka dawo za ku yi magana da Abiey”

“Okay amman kin hakura Ummi?”

“Ya zan yi Maleek uwa ai bata fushi da ƴaƴana na yi hakuri tun kana karami har ka girma, mi zai haka na ki hakuri akan abun da ka yi min? Ni dai ina son ka dage da azkar na safe da yamma, kuma idan zaka kwanta ma ka yi addu'a sannan ka roki Allah ya yaye maka wannan abun saboda yana damuna, bana son na mutu ban ga ka warke daga wannan damuwar ba Maleek, ciwon zai min yawa, idan zaka kwanta ka rika alwala kuma ka yi addu'a, sannan ka tsare karatun Qur'ane fiye da yadda kake yi, sannan ka rika daurewa ko da baka so kana zauna cikin kanenka da ni dan Allah duk abun da kake ji ka daure ka yaye abun a ranka idan ka ji abun ya taso maka ka nemi tsarin Allah”

“In Shaa Allah Ummi”

“Ka yi alkawari?”

“Na yi, ni ma abun yana damuna fiye da yadda yake damunki”

“Allah ya maka albarka, ya yaye maka ko minene?”

“Ameen na gode”

Ya amsa yana jin sanyi a ransa, ita ma sanyin ta ji domin daukar lokaci tana hira da ďanta Maleek ko da a waya ne zata iya kirgashi. Dawood ya dafa kafadarshi.

“This too shall pass Maleek In Shaa Allah, mu kan mu abun yana damun mu balle kuma mahaifiyarka da kai kanka dole ku damu, sai ka dage da addu'a nima kuma zan taya ka In Shaa Allah”

Maleek ya gyada masa kai, ya sauka daga kan motar da yake zaune ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya nufi wata almajira ya saka mata a robar baranta sannan ya dawo gurin motar suka yi sallama da Dawood....

*AFTER ONE YEAR.....*
*BAYAN SHEKARA ƊAYA....*

_Ku yi guessed abubuwa da da yawa🥰🙌_

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

26

Tsaye take ta jingina da karfen dake gabanta tana kallon harabar gidan, Mahmood na tsaye kusa da ita shi ma nasa hannayen suna jingine kamar nata. Daga ita har shi Maleek dake wasa da kallo suke kallo, farar singlet ce jikinsa sai short jean, da dukan kuzarinsa yake buga ball ya hada gumi sosai kamar mai yi tare da wasu team.
Kusan lokaci daya suka kalli Gate din gidan da aka bude manyan motor alfarma ta kunno kai harabar gidan.
     Maleek ya tsayar da ball din da yake yana kallon motar data faka gabansa fuskarsa da murmushi. Wani kyakkyawan bakin saurayi ne ya fito gaban motar dayan kuma ya fito a gurin zaman driver, Maleek ya nufi wanda ya fito a driver seat da sauri ya mika masa hannu suka gaisa, Mahmood dake tsaye kusa da Waira kuma ya zagaya ta dayan side din ya koma dakin, ya sauka kasa gaba daya. Ummi dake falon tana gyara dankwalinta ta kalleshi tana murmushi.

“Sun iso ne?”

“Eah”

Da sauri ta bi bayansa fitowar Ummi falon ta yi daidai da fitowar Dr Zainab a motar dake bayan ta su yayanta. Ummi ta nufe ta da sauri Dr Zainab ma ta nufo Ummi da saurinta abun ka da an dade ba a hadu ba, sai suka rumgume juna cikin farinciki.

“Sannu da zuwa Aunty Zainab”

Ummi ta fada idonta na cika da hawaye rabon data saka ta a ido yau shekara biyu kenan da watani, domin Abuja ba gurin zuwan Dr Zainab ba ne tun bayan da suka bar kasar.

“Zahra... Ya kike ya gida ya rayuwa bayan rabuwa”

Dr Zainab ta dago Ummi daga jikinta tana kallonta tare da aika mata tambayoyi a jere.

“Lafiya Kalau Aunty Zainab mun yi marmarinki sosai ku shigo ciki mana”

Ta riko hannunta suka nufi cikin gidan tana share hawayen dake zubo mata, rayuwar baya take tuna ita da Dr duka sun manyanta a yanzu, sai dai ita da sauki ba kamar Dr Zainab da tsufan ya bayyana karar a fuskarta ba. Kusan gaba daya suka shigo falon, Ummi da Sister in-law dinta agaba, Mahmood da Maleek na binsu sai yayan Dr biyu yan mata dake binsu kamin mazan su shigo daga karshe. Kamshin turaren wutar da Ummi ta kamsashe falonta da shi ya fara yi musu maraba, suka zauna a falon Ummi ta kira Hanne ta zo ta dauke kayansu da ďaya daga cikin yaran dake aiki gidan Rilwanu yake shigowa da su falon.

“Mommy Sannu”

Maleek ya gaisheta da sunan da yake kiranta kamar yadda yayanta ma suke fada, fuskarsa da murmushi kadan yana dan shafa kansa, ya ji yadda suka tararda shi yayi haje haje da gumi kamar wani mai aikin sharar gida.

“Maleek ya aiki? Kai ma Babanka ya koya maka zaman gida da son kwallo ko? Ko kai zaka gado Abiey ne”

“Come on Mommy na girma yanzu, idan za a fara ai da kananan shekaru ake farawa, ni yanzu aikin da nake na kai shi ina?”
Chapter 50 · 0% Book details