← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 170

Sashe 73

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya koma cikin motarsa ya zauna yana kallonta tana kallonsa, yana ganin ta matsa jikin gate din ya danna mata horn ta koma. Cikin tsoro ta kai hannu ta kwankwasa kofar gidan dake rufe sai da ta yi haka sau uku sannan aka bude kofar ganin mutumen daya fito yana sanye da uniform din police ya saka ta dan ji sanyi a ranta, ta juya ta kalli motar Ameer yayi reverse da ita zat tafi ya barta a gurin.

“Na zo gurin Nimara ne”

Ta fadi sunan a birkice tsabar tsoro da rashin rike sunan da ta yi.

“Ke wacece?”

“Kawarta ce”

Police din ya kalleta kasa da sama, shi dai be san yaran gidan na da kawayen da basa da motoci ba, yanayin mu'alamarsu ya saka ba kasafai suke zuwa gidan kawaye ko kawaye su zo nemansu ba, idan ma sun zo suka zo da manyan motoci ne, sai dai Humarai a kasa ta zo duk kuwa da ya hango motar da ke kokarin juyawa wacce yake kyautata zaton a ciki aka kawota.

“Kun yi da ita zaki zo?”

“Eh ga ma wayarta a hannuna tace na zo mata da shi”

Ta saka hannu a jaka ta dauko wayar tana nuna masa.

“Toh jira a nan ina zuwa, wa a ce mata?”

“Ka ce... Ka ce... Ka ce.. Aisha Humaira ce Ameer”

“Aisha Humaira Ameer?”

Ya maimaita sunan sai ta daga masa shi.

“Yeah”

“Okay shigo sai ki jira nan”

Ya matsa jikin kofar ya samu shiga sai ya rufe gate din ita kuma ta tsaya kusa da inda ya nuna mata jikinta na rawa gabanta na faduwa. Kamin yau idan wani ya zo yace yana son ganin masu gidan kai tsaye masu gadin suke ba shi damar ya shiga domin haka Ummi tace musu, sai dai Umarnin da Abiey ya bada na cewar kar a sake Nimra ta fita gidan ya aaka suka tsaurara tsoro gudun kar wani abun ya faru a dora laifin a kansu.

*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

38

MALEEK POV.

Yana shiga dakinsa ya shiga closet dinsa ya aje jakar ya fito ya sauko downstairs ya zauna a dayan side din da kujeru suke, sosai ya maida hankalinsa gurin plasma dake kunne yana kallon film da MBC 2 suke hakawa. Sai da suka tafi talla tukuna hankalinsa ya kai gurin wayarsa dake kan ďayan set din kujerun tana ringing da hanzari ya isa gurin ya dauki wayar tare da amsa kiran da ya biyo bayan miss calls din dake bayyana a saman kiran.

“Maleek kana ina?”

“Ina cikin gida, bana kusa da wayar ne”

“Ka same ni bangarena zamu gaisa da mijin Namra, na kusa karasowa”

“Okay”

“Kuma ban ce ka zo min da kananan kaya ba”

Yayi murmushi kawai ya sauke wayar yana kallon kansa domin kananan kayan ne a jikinsa. Haurawa yayi sama ya canja tufafin jikinsa zuwa shadda ash color ya fesa turare ya saka kular Zanna bukar yar ubansu, ya canja talkamin kafarsa ya saka wandanda za su dace da shaddar jikinsa be damu da duba madubi ba domin ba yin kyau ko akasin haka ne a gabansa ba burinsa yayi shigar mutunci kamar yadda mahaifinsa ya bukata, be fice dakin ba sai da ya murza wani karamin turare a hannunta ya shafe hannunsa zuwa wuyansa, ya dauki wayarsa ya saka aljihu sannan ya sauko stairs din yana wani irin kamshi na tashin hankali kamar shi ne angon. Kofar fita falon ya nufa tana tafiya kamar mai tausayin kasa.  Entrance din bangaren Ummi ya tsaya yana kallon gate din gidansu, a hankali ya juyo yana kallon motar Shuraim sai ba motar yake kallo kai tsaye ba, kyakkyawar halittar Allah mai matukar burgewa da daukar hankali yake kallo, Waira ce tsaye jikin motar can side din da ace bata mike tsaye ba ba zai iya sanin tana gurin ba, ita ma bata mike tsaye dan sanin cewar shi ne tsaye a gurin ba, sai dan kamshin turaren da ya kaiwa hancinta hari ta kasa jurewa har ta leko a zatonta zata ga Sulem dinta ne sai ta yi arba da abokin fadanta.

Yayi kyau, kyau da ake kira da kyau irin kyaun dake fitar da asalin kyau da siffar kyau a jikin namijin, da haramun ne ka yi masa kallo daya ka dauke ido. Hular kansa ta zauna das kamar sai da aka sauna kalar zaren da girman aka zaka masa domin shi kadai kawai. Shaddar ta haska fatarsa ta kara masa kwarjini da cikar izza irin ta jinin sarauta, daga ita har shi sun dauki lokaci suna kallo junansu, ko wane na tantance kyaun dayan jinsinsa. Waira ce ta fara sulalewa kasa ta zauna tana rike da zomonta, a lokacin da idonshi suka daina ganin kyakkyawar fuskarta sai hayyacinsa ya dawo jikinsa ya dauke kai ya sake maidawa gurin gate din yana hade yawun bakinsa da suka tsinke...
Me kike yi a nan wa kike jira, duk baya bukatar amsarsu, yadda aka yi ta fito daga cikin falon ta zauna a gurin ne abun tambaya a gurinsa, jira ko me take yi a gurin ya san amsarsu, ko da ya tambaye ba zai wuce tace masa tana jiran Sulem ba, domin a gurin motarsu ta tsaya. Yana kokarin zuba hannayensa aljihu ta sake lekowa irin leken da be yi kama da gulma take ba, ta gefen ido yake kallonta rabin idonsa na kan gate din da aka buden ragowar kuma suna kan Waira dake kallonsa, tana ganin motar Abiey ta kunno kai cikin gidan sai ta mike tsaye gaba daya ta bar jikin motar ta nufo hanyar shiga falon inda Maleek yake tsaye. Tana doso inda yake tsaye gabansa ya tsanata faduwa na rashin dalili kuma ya kasa kallonta har ta iso gurin ta ratsa gefensa ta wuce. Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya samu sukuni a zuciyarsa, tun da yake a rayuwarsa be tana jin abun da yaji a yau ba. After Abiey ya faka a compound din gidan ya sauko ya isa gurin motar yana masa sannu da zuwa.

“Maa Shaa Allah, haba ko kai fa yanzu da ban maka magana ba da kananan kayan zaka saka ka fito a matsayinka na yayan Namra”

Murmushi yayi as respond ya karbi jakar dake hannun driver mahaifinsa suka jera a tafe kamar ba uba da ďa ba, kamin su karasa apartment din Abiey yayi masa tambaya uku ya kasa bashi amsar ko daya.

“Ai tun kamin ya zo a matsayinka na dan'uwanta kuma namiji, wanda nake sa ran ko bana raye ko kuma nan gaba kadan zaka iya gudanar da komai ya kamata ace ka mata tambayoyi akansa”

“Abiey ka san ba wani sakewa nake da su sosai ba, so ban cika son shiga rayuwarsu ba”

“Amman ai na ga alakarka da su yanzu ba kamar da ba, ka samu lafiya inji Umminku kasan ita ce kullum take ganin baka da lafiya”

Abiey ya fada yana dariya. Maleek kuma ya kai hannu ya bude babbar kofar falon Abiey ya fara shiga sannan Maleek ya biyo baya. Falon farko babu kowa a ciki hakan ya bawa Abiey da ďansa Maleek damar shiga kofar dake cikin falon wacce zata sada su da corridor dakin Abiey ba sai sun bi ta cikin karamin falon da Namra ta sauki surikinsu ba. Abiey ya fara shiga dakinsa kai tsaye ya zauna tare da Maleek yana fadin.

“Kira Namra ka fada mata ta sanar da bakonta zamu shigo mu gaisa da shi yanzu nan”

“Abiey ba zaka huta ba?”

“Hutun me? Aiki na bari na zo nan fa kuma muna gama gaisawa zan koma”

Maleek ya ciro wayarsa dake aljihu a maimakon ya kira sai ya aika mata da sako. Abiey kuma ya kira Ummi Dr Zainab ta amsa wayar.

“Ka dawo”

“Eh ina dakina tare da Maleek”

“Toh bari idan kun gaisa da shi sai mu fito muma mu gaisa da shi”

“alright”

Ya aje wayar, after like 20 minutes Namra ta shigo dakin ta zube kasa ta gaishe da Abiey kanta a kasa tana mai jin kunyarsa abun da bata saba ba.

“Abiey na fada masa”

Mahaifinta yayi dariyar farinciki yana zolayarta daman ya saba wasa da yayansa ba maza ba matan ba balle kuma Ummi da take matarsa.

“Toh Gimbiya Namra bari mu tafi mu gaisa da Yarima”

Ta rufe ido tana dariya. Shi ma dariyar yake Maleek kam kallonsu kawai yake kamin ya mike tsaye tare da mahaifinsa suka fice daga ďakin. Shuraim na jin an taba kofar falon sai suka kara daidaita natsuwarsu domin Namra ta sanar musu mahaifinta zai shigo ya gaisa da su, kusan a tare Shuraim da abokinsa suka mika tsaye suna amsa sallamar Abiey. Maleek ne ya riga karasa inda suke ya mika musu hannu suka gaisa sannan ya zauna a kusa da inda suka zauna. Shuraim ya mikawa Abiey hannu biyu ya gaisa da shi as well as abokinsa.

“Bismillah”

Abiey ya fada yana nuna masa kujera, tsantsar ladabi da girmama na gaba ya hana Shuraim zama a saman kujera saboda Abiey ya zauna saman kujera yana ganin be dace shi ma ace yana kan kujera ba.

“Sannunku da zuwa”

Sai suka amsa da yauwa suka zauna a kasan Shuraim kansa na kasa kamar wani mace, Abiey kam kamar ya samu tv haka ya rika kallon saurayin mai shirin zama surukinsa.

“Namra ta fada mana zaka zo, saboda mun bata damar zabar wanda take so, mun yi maganganu da ita, sai dai ina tunanin yana da kyau mu kai ma ka gabatar mana da kanka, kuma ka yi hakuri da tambayoyin da zan maka”

“Ba komai Abbah, daman shiyasa na zo ai, saboda mu san juna kuma na yi bayanin kaina, idan na koma sai na sanar da iyayena su same ku da maganar ko a yanzu ma sun san da maganar sun dade da sanin Namra sai dai a yanzu ne magana mai karfi zata shigo”

Abiey ya tsuke ido yana kallon Shuraim tare da murza tsayansa daya da hannunsa kamar mai kokarin tuna wani abu.
Chapter 73 · 0% Book details