← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 170

Sashe 31

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta rumgume kanta tana kara matsawa baya. Be sake ce mata komai ba sai ya dauki abincin ya matsar mata da shi hannu ta saka ta buge abincin ya zube kasa ta dauki Apple din kadai ta rike.

“Waya bata Apple”

Ya tambaya yana kallon Nurses din dake bayansa, suma kallon mamaki suke masa domin sun san shi ya bata apple din da kansa.

“Dazun kai ka bata da kanka”

With confused ya kalli wacce tayi maganar, baya son musu surutu ma bangarensa ba ne balle kuma musu, hakan ya saka be damu ya musa musu ba, all what he thought is wani likitan ne ya bata suka yi zaton shi ne. Matsawa yayi kusa da ita sai ta matsa baya kamar zata shige jikin ginin tana masa kallon tsoro, hannunsa ya kai ya rika kanta yana kokarin duba idonta dake kama da nashi tsabar farin idon, sai dai nata gwaiduwar ciki blue ce tsabanin tashi da take baka wulik, kallo daya zaka mata ka fahimcin kyaunta ya banbanta da na sauran mata sa'aninta duk kuwa da kasancewar dattin dake jikinta. Tana da masifar kyau ga kirjinta a cike daidai har ya fi na sa'arta domin rigar saƙin dake jikinta ta fata tana fito da ainahin zatin kyaunta ne. Be ankaro ba ta dantsara masa cizo a hannu da mugun karfi, abun ka da wanda ya dade be ci nama ba hausawa suka ce masa maye wai idan yayi cizo ba a warkewa da wuri, idan kuma yayi magana sai ta kama Mutun lol, tana dota hakoranta a hannunsa kamar reza haka hakoran suka yaga rigar hannunsa suka shiga har cikin naman hannunsa sai wani zafi yaji kamar an yanke shi da wuka a take jini ya fito sai dai ba mai yawa ba, cikin zafin nama ya fisge hannunsa yana zaro ido

“Easy Girl...”

Da sauri Police din da suka zo daukar report dinta suka jo kanta da gudu suka riketa dayan ya juyarda hannunta da karfi zan lankwasa sai Likitan yayi saurin dakatar da shi ganin yana kokarin yi mata illa kamar ya samu katon namiji.

“Nonono she's just a girl karka ji mata mana”

“Ai kara ayi mata haka, what is akwai dafi a bakinta fa? Ba mu san waye ita ba”

Ya fada yana kara matseta.

“Saketa dan Allah ta tsorata ne tana zaton zan mata wani abun ne”

Ya saketa kamar yadda Dr Shuraim ya bukata, sai ta rumgume hannayen nata m har da mai ciwon.

Dr Shuraim ya fice gurin rike da hannunsa har lokacin ciwo yake ji a  iz  sosai, kamin ya karasa Office dinsu na Likito ya cire safar hannun ya jafa a gurin da aka tana da domin zuba shara, bathroom 2(8 ya fara shiga ya wanke hannunsa sannan ya fito ya dauki audiga ya saka a gurin ya goge, sannan ya cire labcoat din dake jikinsa ya aje ya ciro wayarsa dake ringing ganin mai kiran ya saka shi murmushi.

“Hey Baby Girl”

“Ruhul Kal ya kake ya aiki?”

“Ina lafiya fatar ke ma haka kike?”

“Nima haka, ya Katsina”

“Katsina na nan sai zafin kamar za a kama da wuta”

“Mu kuwa ruwa ake mana yanzu, wani guri na samu na fake ma”

“Daman ku yan Abuja kun fi kowa zama yan gayu, fatar dai ruwan be taba min ke ba”

“Ya jika ni kadan”

“Da ace zan ga ruwan an kuwa da na masa duka”

Ta kyalkyale da dariya, shi kuma yayi murmushin da ya bayyana fararen hakoransa da suka haska bakar fatar jikinsa mai kyau da sheki.

“Take care of yourself zan kiraki idan na bar gurin aiki”

“Toh I love you”

“I love more and more and more Baby girl”

Ya sauke wayar, sannan ya fice daga gurin, dakin da ake aje majiyanta ya sake komawa sai ya samu har lokacin suna nan tsaye akan yarinyar yanzu ma har an samu karin wasu mutane dake kallonta a cikin masu jinya.

“Wannan ai zaku tsoratata ne, please kowa ya koma gurinsa”

Kowa ya wuce ban da police din da suke zon tirsasa ta tayi magana.

“Ba zata iya magana a yanzu ba, a yadda na fahimta ko tayi magana ba zai amfanar ku komai ba, domin ba ta jin yarenku inda ba ta yi hakan da gangan ba, kai kana duba jikinta da yanayin tufafinta kasan ba ta jin yarenmu”

“Amman Doctor zai dauke ta lokaci kamin ta warke?”

“Eh ya danganta da kalar majicin daya cije ta, zata iya sati ko sama da haka a ka'ida dai ana son ta samu kulawa mai kyau na wata daya idan abun yana da karfi wata shida shi ne zata warke gaba daya”

“Okay mun gode, dan sandanmu daya zai tsaya tare da ita saboda bada tsaro da kuma kula da ita, ni kuma zan je na sanar da halin da take ciki”

Da kai ya amsa masa, sannan ya mika masa hannun suka gaisa su biyu suka fice dayan ma da aka bari domin bata tsaro fita yayi saboda ganin Likitan ya zauna a saman gadon da take zaune. Kallonta Dr Shuraim yake yana son fahimtar wasu abubuwa a tattare da ita.

“Baby Girl...”

Ya kirata da irin sunan da yake kiran Babensa, domin be san sunanta balle ya kirata da shi.
Ya leka kasan fuskarta sai ta boye kanta.

“Akwai bukatar ki tsabtace jikinki ki ci abinci a baki magani”

Kamar wacce ta san abun da yake fada sai ta lake kafada daga boyen da take ta fashe da kuka. Da kamar mamaki ya ke kallonta.

“Kina jin yarena?”

Nan ma ta lake kafadar.

“Wane yare kike ji?”

Nan ma ta sake yin abun da ta yi dazu, sai ya fahimci bata son yayi mata magana ne.

“Okay Baby Girl zan barki ki huta”

Ya mike tsaye sai ta dago kanta ta kai apple din hannunta a baki ta fara ci, still tana kuka kamar wata shagwababbiya. Shi dai be sake ce mata komai ba ya fice.

AMEER POV.

Fitar Ameer da kamar minti biyar da fitar Ameer Daddy ya kira Momy sai a lokacin yake fada mata abun da ya faru, da kuma response din Ameer akan cewar shi be san da labarin yarinyar ba.

“Wata kila da gaske ne, kasan Ameer baya tsoron amsa laifi idan ya aikata kamar yadda ya amsa maka cewar ya karbi motar”

Ajiyar zuciya ya sauke mai dauke da damuwa.

“Ina fatar haka, sai dai ina jin kamar ba yarda da shi ba, kwana biyun nan abun da Ameer yake ya fi karfin na baya”

“Jarabawa ce, dole hakuri zamu yi muna masa addu'a har Allah ya shiryar da shi, kuma ni ina ganin kamar ayi masa aure a zai saka ya natsu”

“Tun da nake da Ameer be taba min zancen soyayyar ba, gaba daya mata basa gabansa shiyasa na sha mamaki lokacin da yake fadar akwai wata yarinyar shi har suka samu matsala da abokinsa”

“Kai mahaifine ai, zaka iya zaunar da shi ka nuna masa inda kuskurensa yake, idan ya manta karatun sai ka tusa masa, yaran yanzu sai da haka, kuma duk wata lalace da kake ganin Ameer yayi laifinka ne, sam baka yarda ayi masa magana idan yayi kuskure”

“Akwai yara da yawa da suka tashi a cikin gatan irin na Ameer, amman basa yin abun da yake yi, zai fi kyau mu dora abun a babin kaddara Allah ya hukunta kawai”

“Toh Allah ya shirya mana, amman gaskiya a maida hankali gurin yi masa aure kasan aure yana natsar da Mutum kuma idan an tashi kar a nema masa yar Babban Mutun domin ba ko wace mace ce zata iya zama da shi ba, sai dai a nema masa mai hakuri wanda zata iya bin halinsa”

“Idan kuma yana da wanda yake so fa?”

“Shikenan ta kwana gidan sauki, sai a aura masa daman ai ya kai munzalin auren kuma Allah ya hore komai”

“Nima kuma shekaru suna ja, ina da burin ganin haka kamin ta Allah ta kasance”

Furucin da Daddy yayi sam be yi mata dadi ba, hakan ya saka bata sake cewa komai ababin maganar ba.

“Zan aje waya, saboda ina shirya abincin rana”

Yayi murmushi ya sauke wayar, sannan ya sake kiran CP, duk wani abun da za ayi a kashe maganar Daddy yayi domin baya son damuwa a yanzu kamar yadda likitansa ya tabbatar masa.

Jikin Motar Momy ya jingina thinking of din yarinyar ta mutu yadda zai bata ma Maleek da kanwarsa suna, a yanzu din ma tunanin yadda zai yi amfani da wannan damar ya taba martabar gidansu Maleek yake, he just wants to take revenge shi dai zuciyarsa suna masa take Maleek yayi masa Zagon Kasa, ya bude motar ya shiga yayi mata key jin kamar yana marmarin gurin da suka saba zama da abokansa ya saka shi nufar wani gurin shakatarwar na dabam, domin baya son ya sake shiga safgarsu tun bayan wulakancin da suka masa na zabar Maleek su barshi.

MALEEK POV.

Babu wanda yace Uffan a cikinsu bayan Abiey ya gama labarta cewar Ameer yace shi be san yarinyar ba be san inda ta fito ba kuma ba shi da alaka da ita.

“Amman karyar yake yi yana son ya kulla mana wani abun ne kawai”

Namra ta fada cikin jin haushi domin ji take kamar ace yana gabanta ta kwada masa mari. Ummi ta kalleta a hankali jin yadda take magana da zafin rai sai dai bata ce komai ba ta mai da kanta kasa tana jin zuciyarta ba dadi. Maleek ya saka hanayensa aljihu

“Wata kila kuma gaskiya ya fada, domin na san waye Ameer baya shakar ya amsa laifi komai girmansa matukar ya aikata zai ce shi yayi, idan har be amsa ba to be aikata din ba ne”

Namra ta girgiza kai.

“To waya aikata? Waye zai yi hakan bayan shi? Ko da ma ace wani ne yayi ai shi ne sila, kai da Ummi kamar kuna son kare Ameer din nan makiyin mu ne fa”

Maleek ya nunata da yatsa.
Chapter 31 · 0% Book details