← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 170

Sashe 53

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Baki shiryawa fuskartar ko wane kalar kalubale akaina ba kika bari na fada sonki? Mi na yi ma iyayenki ne suka tsane ni? Just because of abun da ya faru tsakanin da Maleek ni fa na dade da watsar wannan abun, soyayya ba haramun bace kuma aure ba zamu yi ba wai muna soyayyar ba ne dan mu rabu, da kin san yadda Daddy yake matsa min lamba akan maganar aure da kin tausaya min”

“Ni ma ai matsa min ake yi, kawai na kasa fitowa na fada musu cewar kai bake so ne, na kuma kasa bawa kowa kofar da zai furta min so ko ya nuna min haka, saboda gudun kar a cilasta ni na fitar da wani ba kai ba, ina matukar sonka Ameer, na jefawa maza da yawa dutse saboda da kai, kamin na hadu da kai idan maza sun taya ni bana amsawa balle na siyar, bayan haduwa ta kai ma kamar ammin turaren farinjini haka maza bina da nuna soyayyar a gareni, amman na saka amsar kowa, idona be ganin kowa zai kai Ameer, bana jin muryar wani namijin na jidadi sai kai, sunan kowa baya min dadi sai kai, kullum mafarkina da burina yadda zan yi rayuwa da kai ne, na karya dokakin gidanmu, na gurbata tarbiyata saboda kai Ameer, yanzu kuma ina shirin fuskarta wani babban kalubalen saboda kai, Allah yasa wata rana karka juya min baya, karki min irin abun da wasu mazan suke yi na butulcewa matarsu, idan na rasa ka zan shiga mawuyacin hali, ina matukar sonka Ameer...”

Tana maganar hawaye na sauko mata, gaba daya sai jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta yi wani iri, a sirrance ya sauke ajiyar zuciya, ya matsar da fuskarsa kusa da tata ya tsatsa bakinta, sai ta lumshe ido hawayen na cigaba da yi mata zuba....

“Ya kamata ki tafi kar a sake kiranki, i love you”

Ta bude ido ta share hawayen tana kallonsa, sannan ta bude motarsa ta fita ta nufi tata motar ta shiga, ta murza key ta yi reverse tare da horn Mai Gadinsa ya bude mata ta fice. Ta madubin motar yana hangota har ta fice sannan ya kwantar da kujerarsa baya ya jingina ya lumshe ido yana busar da iskar bakinsa...

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
27

Hanne ta kawo ma Dr Zainab abincinta a daki, yaranta kuma suka ci nasu abinci a falo bayan sun yi sallah. Maleek ne kawai ya fito da abincinsa a waje ya zauna ya ci a balcony da ya gama kuma sai ya zauna a gurin be tashi ya cigaba da latsa wayar da yake. Sai da yamma list Ummi ta hada Waira tea ta kuma saka Hanne ta soya mata dankali, sai ta fito ta zauna a Balcony nesa da inda Maleek yake zaune tana sipping tea da Biscuit, irish din da aka soya mata ma bata taba shi ba, idonta harabar gidan kawai take kallo da motocin da aka faka, har yanzu tana mamakin yadda rayuwarsu mutanen gidan take duk girman gidan ace su kadai suke rayuwa a ciki, ga kawata ko'ina da aka yi kamar ba za a mutu ba, har gobe tana tsoron hawa mota sai dai tsoronta ya ragu ba kamar da ba. Jin an zauna kusa da ita ya saka ta juyo a hankali sai ta yi arba ďaya daga cikin bakin da suka zo dazun, murmushi yayi mata ita kuma ta maida kanta kasa ba tare da tace masa komai ba. Ya kai hannunsa ya dauki biscuit ďaya ya fara ci.

“Waya saka miki zobe a wuya?”

Ta kalli zoben.

“Sulem...”

“Sulem.... Waye kuma Sulem.... Saurayinki ne?”

Ta yi shiru, sai ya kara matsowa kusa da ita.

“Na sanki ni na tsince ki a lokacin da aka jefar da ke kin tuna”

Ta kalleshi da kyau.

“Yes karki min karya kin san dai na sanki ko? Fada min ina iyayenki suke, na sani ma domin yayanki abokina ne kuma na ga suna nemanki, amman ina son na sake sani ne”

Ba zata iya fadar wanda ya dauko a lokacin da hankalinta ya gushe ba, sai dai ta san kamin ta suma mutumen da ta gani ko kadan be yi kama da wannan ba. Hakan ya saka ta mika hannunta ta taba hannunsa be san manufar ta yi hakan ba shiyasa be hana ta taba hannun nashi ba, sai ma kallon hannun da yayi. Gardamar da suka yi da Mahmood ta gani har yayi ikirarin cewar shi ya san yadda zai yi ta fada masa inda iyayenta suke, bayan Mahmood ya labarta masa cewar har yau bata taba cewa komai akan iyayenta ba.

Be ankaro ba ya ji ya bushe da dariya sosai har tana tintsirawara, shi ma murmushi yayi yana kallon yadda dariyarta take da burgewa. Maleek ma sai da ya dago ya kalleta ya dauke kai ya cigaba da latsa wayar da yake.

“What...”

Jabir ya tambaya yana kallon kansa da mamaki domin ban san abun da take yi ma dariya ba, Waira kam plan dinsa take dariya da yadda ya sha alwashin sai ya mata wayo ta fada masa komai. Kofar falon aka bude Ummi ta leko tare da Mahmood da Nimra har da Hanne suna kallon ikon Allah.

“Jabir me ka fada mata take dariya haka?”

Ya dan karkato ya kallesu.

“Nothing bata dariya ne?”

“Tun da take a gidan nan bata taba dariya ta kyalkyata ba”

Ya juyo ya kalleta a yanzu kuma murmushi take wanda ya bayyana hakoranta. Ummi ta yi murmushi cike da jindadin ganin farincikin Waira.

“Well done Jabir daga zuwanka ka saka min ƴa dariya”

Yayi dariya shi ma ba tare da sanin abun da Waira take yi ma dariya ba, shi dai ya san tambayar kawai yayi after that be fada mata wani abun dariya ba. Ummi ta juya ta koma ciki tare da Hanne suna ta mamaki, Nimra kuma ta kashe masa ido irin na zolaya.

“Yaya dai Jabir ko dai taku ta zo daya?”

“Da wa? Ai ba zaki yarda ba”

“Saboda me? Indai ruwan zai maka wanka ai sai dai mu nama maka na dauraya”

“Hmmm -Nhmmm Nimra kenan ke zaki yarda ki barwa wata ni?”

Ta saka dariya domin ta san halinsa da barkwanci musamman idan baya son abu yanzu ne zai juye ya mayar akan wani.

“Ni na mashinshini na kai ne baka da kowa, shiyasa nake maka kamu ka samu wannan yarinyar ta taimaka maka”

Ya girgiza kai yana cije baki.

“Ko waye mashinshinin nan na ki ki fada masa you're taken kuma ina da kishi bana son wani na rabar iyalina”

Dariya ta saka gudun kar Maleek dake zaune can gefe ya gwatsaleta ya saka ta juya ta koma falon tana gyara dankalin kanta. Shi kuma ya sake juyowa ya fuskanci Waira.

“Fada min ina iyayenki suke?”

“Waira zata fada, amman ba wayo ka yi ba”

Fada masa take zata fada masa, amman ba dan yayi mata wayo ba, shi kuma sam be gane salon karin halshen nata ba, shiyasa be yi kokarin cewa komai ba har ta cinye biscuits din dake kan plate din gaba daya ta kalleshi idonta na cika da hawaye ta ce.

“Waira bata da yaya, bata da Baba, bata da Mama amman tana da Eid”

“Waye Eid?”

“Dan'uwanta ne, yana sonta, Eid yana mata komai amman yanzu be neme ta ba, Waira ba zata koma garinsu ba, idan ta koma Sarki zai kasheta”

Mamaki ya kama Jabir.

“Saboda me? Me kika aikata? Wani kika kashe”

Sai ta girgiza kai hawaye na sauko mata.

“Bata kashe kowa ba, amman Sarki yace idan Waira ta gudu ba zata iya dawowa ba, kuma wani ya mutu saboda ita, za a kasheta”

“Miyasa kika gudu? Baki da yan'uwa a can? Ke baiwa ce ko kuma me?”

Ta girgiza kai hawaye na sauko mata kamar ba gobe.

“Waira bata san kowa ba, ita kadai take zaune tana da....”

So take tace bera da zakara kuma ba zata iya fadar hakan da hausa ba, ta suna sunan da aka fada mata na zaka da bera.

“Waira tana da Hens, Waira tana da Rat, Waira Waira zata mutu kusa Sarki ba zai kyale ba, zai kasheta”

Ta girgiza hancinta na zubar da majina kamar yadda idonta ke zubar da ruwan hawaye.

“Waira bata son ta mutu, Waira tana son ta ga Eid Waira bata son ta koma, ba zata gane hanya ba”

Da gaske take fada domin tana yawan tuna mutanen garin da rayuwar da take a garin amman ko kadan ta kasa tuna sunan garin ma balle kuma ta san hanyar da zata bi ta tafi, ita dai ta san ta rayu a wata duniyar kamin ta samu kanta a nan, kusan kullum sai ta kwanta da tunanin Eid da berayen da suke rage mata kewa. Ta kalli Jabir tana kuka sosai.

“Waira bata son ta mutu, Waira tana son Eid, Eid ba zai zo ba, Sulem ba zai zo ba... Waira tana Son Sulem....”

Ya matso kusa da ita ta jingina kanta jikinsa yana jin tausayinta na kama shi. Har suka ci suka sude Maleek be dago ya kalleta ba tun bayan kallon da yayi mata da farko, sai dai kunnuwansa suna sauraren komai take fada and one by one ya fahimci ko wace kalma dake fita bakinta.

“Waira bata son makaranta, suna mata dariya idan ta yi magana, Waira bata da kawa a makaranta”
Chapter 53 · 0% Book details