← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 170

Sashe 12

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Karya fa na yi na ce yayana ya aiko ni gurin Manager shiyasa aka bar ni na shigo, dan Allah ka taimaka ka fada min”

Ya tsaya sai kuma ya sake juyowa ya kalleta.

“Ba ma bukatar irinku”

Ta kalli tufafinta zuwa kasanta.

“To na gode”

Ta sauko ta wuce ta fice daga gurin cikin yanayi na rashin jindadin, bata san waye shi ba, sai dai da alama yana da babban mukami shiyasa har yake korarta, samun kansa yayi tsaye yana kallonta har ta sauka daga gurin gaba daya sannan ya fito, a gurin da ya saba aje motarsa ya nufa ya bude motar ya shiga ya dora rigarsa a kan kujerar sannan yayi reverse ya fice daga kamfanin da irin tukin da ya fi kwarewa akai.
   A harabar entrance din falon ya faka motarsa sannan ya fito ya doshi kofar, a ka'idarsa baya taba door Bell din wai be san iya mutanen da suka tsaba ba zai iya tabawa ya kwashi cuta, wannan ya saka yafi jindadin yayi knocked ko ba komai knocked kan banbanta shi da sauran mutane a san da cewar shi ne zai shigo so that ayi saurin bude masa. Sai da ya tsaya ya cire talkaminsa ya saka na shiga falon sannan ya shiga, as usual ko'ina na falon kamshin turaren wuta yake bayan air freshener da aka saka da kuma turaren goge tile. Karamar kofar da suka saba budewa su shiga ta sada su da bangaren Mahaifinsa ya bude ya shiga dan karamin corridor dake cike da kayan kawa, karamin falon ya shiga sai ya samu Daddy a tsaye Momy na daura masa a gogo a hannu.

“Lafiya Daddy?”

Da hannu Daddy yayi masa alama da ya zauna, sannan shi ma ya zauna Momy ma ta zauna cikin yanayin damuwa.

“Ameer ka yi fada da wani?”

Ameer ya kalli mahaifinsa kamin ya kalli Momy dake maganar.

“Kamar ya?”

“Police aka turo su tafi da kai”

Dariya yayi ya dan yamutsa fuska.

“Ni kuma? Ni police za su tafi da ni?”

Sai a wannan karon Daddy yayi magana.

“Calm down na yi magana da CP bana son ka je gurin nan but it seems like dole sai ka je da alama yaron da ka taba shi ma dan masu gari ne”

“Me suke zargina da shi?”

“Wai cin mutumci da barazana akan rasa rayuwar wani, da wa ka yi fada Ameer? Na sha gargadinka akan abun da kake tun kana yi abu yana wucewa yanzu ya kai har a turo police a gidana da sunan ana son a tafi da ďana? Na so na kashe case din ba tare da kaje ba amman CP ya nuna min abun ba zai yiyu ba Ameer ina tsoron ka dauko rigimar da zata fi karfina na kasa cireka daga wata matsalar”

“Waye yayi karata ne Daddy? Shi nake son sani”

“Akwai yaron da ka saka yayi wani aiki a gurin da kuke shakatawa?”

Ameer na jin haka sai yayi murmushi abun da ya bawa mahaifinsa mamaki.

“Yeah akwai wanda na saka ya bawa wani abokin mu abu”

“Kamar ya? Ka yi min bayanin komai so that na san yadda zan bullowa lamarin”

Daddy ya bukata.

“Ya taba ni ne Daddy, kuma zan koya masa hankali nan gaba kadan”

“Me ka yi masa a yanzu?”

Ameer ya kalli mahaifinsa.

“Ba su fada maka ba?”

“Wata kila laifin yana da girma shiyasa CP be fada min ba yace min sai na zo”

Babu kunya babu tsoron Allah Ameer ya fadawa mahaifinsa abun da ya aikata da kuma wanda yake da kudirin aikatawa a gaba. Daddy ya mike tsaye yana kallon đansa cike da tsoro.

“Ameer yaushe ka lalace har haka? Ka kullawa abokinka Sherri saboda kawai ya watsa maka yawu a fuska? Bayan kai ka fara takalarsa?”

Ameer ya daga kai yana kallon mahaifinsa.

“Daddy sai ka rika daga hankalinka akan abun da be kai ya kawo ba”

“Ameer kana da hankali kuwa?Miye be kai ya kawo ba? Kokarin bata sunan abokinka ko kuma kallon tsabar idona ka fada min saboda ka tambayi friends dinka yarinyar ka ta zo ya hada ka da abokinka? Ko kuma abun da ka aikatawa abokinka?”

Momy ma kallon Daddyn take  tashin hankalin da ta gani a fuskarsa ya daga mata hankali sosai, ta dade ta sanin cewar Ameer yana gwada aron hannu sai dai ba damar ta fadawa mahaifinsa gudun kar ta hada su ko kuma yayi zaton tana yi ma ďansa sheri ne. Daddy ya nuna kansa.

“Kwarin idonka ya kai ka kalleni ka fada min cewar kana da budurwa sheke aya? Dukanin arzikin da na baka na nufin ka lalace ba, amman kullum sai ka saka ni ciwon zuciya, a kullum ina nuna maka abun da kake be dace ba amman ka kasa fahimtar hakan, tun kana dauko kanana har ka fara dauko mana magana”

Ameer ya mike tsaye yana kokarin danne bacin ransa.

“Daddy wannan abun da na aikata har ya kai ka fada min magana marar dadi kamar wannan? Simple abu? Ashe wani ba zai iya taba ni na gudu bayanka na buya ba”

“Zaka iya only idan kana sa gaskiya, bana son zalinci bana son cin mutunci da rainin wayo, ka wuce mu tafi gurin CP yanzu nan, kuma karka kuskura amsa cewar ka aikata laifin nan”

Daddy ya fada yana nuna shi da yatsa, domin ya san karamin halinsa ya amsa laifin a gaban kowa a kokarinsa na nunawa duniya cewar shi baya tsoron kowa ko kuma babu mai iya hukunta shi. Ameer ya kalli Daddy kamar yace wani abu sai kuma ya juya ya fice daga falon rai a bace. Motar da ya shigo ya sake shiga yayi mata key Daddy na jin karar tashin motar ya san ďansa ba zai bi umarninsa na zuwa inda ya bukata, wani kulikulin bakinciki ne ya taso masa har sai da ya fadi kan kujera zaune.

“Ba mu yi ma iyayenmu haka ba, kullum muna gudun bacin ransu, tarin dukiya da yawan gata be saka mun lalace ba”

Momy ta matso kusa da shi tana kokarin kwantar masa da hankali.

“Zamani ne ya zo, wasu abubuwan da baka tana ji ko gani ko zato ba za su faru, wani abun jarabawa ce dole sai ka yi hakuri zaka iya ci, dan Allah karka saka komai a ranka, shi ma na san anjima kadan zai sauka ya gane kuskurensa”

Daddy ya lumshe ido ba tare da yace komai ba.

“Yanzu ka samu kashe wannan wutar, da alama shi ma yaron da ya tsokano dan manya ne shiyasa har CP ya aiko maka da police har cikin gida, idan ba haka ba ba zaka san ma an kashe case din ba”

Ya amsa mata kai yana jin yadda zuciyarsa take masa mugun ciwon, irin ciwon da ta saba yi masa tun kamin ya samu Ameer.

A gurin da ya koyawa kansa zama ya nufa, ya isa gurin a lokacin da wata zuciyar ta jika da jiransa, gaban motar Nimra ya faka motarsa sannan ya fito motar ya nufo inda Nimra take jingine da motarta fuskarta ba yabo ba fallasa ba kamar yadda ya saba yi ganinta da far'a ba.
Tsaye yayi ya kasa ce mata komai, he need someone to talk to amman ba ya jin zai iya fara yi mata magana sai dai ita ta yi masa.

“Tun safe nake a nan”

Ta fada tana kallon harabar cikin wani yanayi da ya fi kama da na damuwa. A gogon hannunsa ya kalla 12pm da mintuna ya gani, ya saka hannayen nasa aljihu yana wani shan kamshi.

“Why?”

Ta kalleshi a karon farko.

“Daman na saba zama a nan, saboda guri ne da babu hayani sosai, kuma babu mutane da motoci idan kuka kake son yi zaka yi kuka babu mai ce maka domin me? Idan kuma nishadi zaka yi duk zaka iya yi a nan, na saba na kan zo wani lokacin da kawatau zauna a nan mu ci wani abu ko mu yi hira, kamar yadda ka tararda muna ci abincin a farkon zuwanka gurin nan”

Ya daga kai yana karewa gurin kallo.

“Mi ke damunki?”

“Ban sani ba, tsoron rasa mahaifiyata ne ko kuma damuwar da ďan'uwana ya shiga ne? Na matukar son family na, musamman mahaifiyarmu ko kadan bana son na ganta a cikin damuwa, damuwarta tana haifar min da tashin hankali, wani lokacin sai na rika jin kamar zan iya rasata idan na rasata ya zan rayu? Ummi tana yawam shiga damuwar da bata fadawa kowa, tashin hankalin da na gani a cikin idonta a jiya saboda yaya da kuma halin da yayana ya shiga ya saka na tashi ina jin wani yanayi na dabam”

A karon farko ya jingina jikin motarta ba tare da tunanin kar tufafinsa su kwashi datti ba kamar yadda ya saba jin tana cikin damuwa ya saka ta sa damuwar nisantar ruhinsa.

“Akwai ta inda zan iya taimakawa?”

Murmushi ta yi.

“No... Karka damu komai ya wuce a yanzu, fada min ya kare da abokinka?”

“Kamar baki cikin yanayin da ya kamata mu yi wannan hirar, but na yi nasara kuma ina daf da sake yin wata nasarar, but yau din ma an sake mata min saboda shi”

“Waya bata maka rai?”

“Daddy na”

“Karka damu da sannu zamu ga bayansa da yardar Allah, duk makiyin da ya saka mu gaba sai mun ga bayansa”

Ya daga mata gira

“Yeah...”

Tare da yin murmushi mai sauti kamar ba shi ba, ita ma ta yi murmushin tare da busar da numfashi.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

_Na Khadeeja Candy_

BARKA DA SALLAH
Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu, Ameen.

7️⃣

MALEEK POV.

Maleek ya hade carpet din da yayi sallah da shi ya mike tsaye ya juyo ya kalli Mahaifiyarsa dake cikin shirinta na fita.

“Ummi da zaki taimaka ki fita a maganar nan, tsakanina da friends dina ne?”

“Friends...?”

Ummi ta tambaya tana matsowa kusa da shi da wani irin mugun kallo.
Chapter 12 · 0% Book details