← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 170

Sashe 17

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Saboda me? Shiyasa ka hana na shiga? Yaron ya fi karfin a hukunta shi ne? Taya mutum zai nemi kashe min yaro kuma kace kun sulhunta Ba sulhu nake so ba, hukunta shi nake son ayi idan ya saba yi ana kyaleshi to yanzu ya kai karshe”

Abiey be ce mata komai ba, ya wuce dakinta sai duk suka bishi da kallon mamaki, har sai da ya shige kofar da zata sada shi da bangarensa. Sannan Ummi ta juyo tana kallon Maleek.

“Waye yaron nan ne? Ya fi karfin kowa a garin nan ne? Waye Ubansa?”

Nimra ta dafata tana kokarin kwantar mata da hankali.

“Ummi, Abiey fa ya fiki son yaya tun da kika ga ya bar maganar nan abun ya fi karfinsa ne please calm down”

“Yaron ba a san inda yake ba Ummi, DSS din da aka tura su kama shi sun ce ba su same shi a gidan ba, kuma step mother dinsa ta zo tana kuka ta yi ta ba mu hakuri, ta ce yanzu haka mahaifinsa ya koreshi ya karbe komai nasa saboda abun da ya aikata, kuma mahaifinsa yana can ya fadi ba lafiya”

Mahmood ne ya bata amsa, daman can bata sa ran samun wannan dogon bayanin daga bakin Maleek ba.

“Karya ne sun shirya hakan ne saboda su kare dansu”

Namra ta fada, a daidai lokacin da wani tunanin na dabam ya zowa yar'uwarta Nimra.

“Waye Ubansa?”

Ummi ta tambaya tana jin kamar ba zata iya kyale maganar nan hakan nan ta tafi ba. Maleek ya fara tafiya ya nufi kofar fita daga falon domin ya tsawalla dan tsayin da yayi a falon da kanennensa da kuma mahaifiyarsa.

“Sunan Yaron Ameer dan gidan Alhaji Bashir something Mr Bashir shi ma dan Kano ne”

Da wani irin karfi Ummi ta zabura sakamakon bugawar da zuciyarta ta yi cikin rashin shiri, sai ta ja numfashi da karfi. Nimra ta nufi Mahmood tana fadin.

“Ka san shi Mahmood? Kana da hotonsa?”

“Na san shi, lemme see”

Ya ciro wayarsa ya shiga Instagram yayi searching Account dinsa, a nan yayi ta haduwa da fake account da sunan nasa, sai dai be damu da hakan ba domin abun da ya kai shi Application din neman hotonsa, hotunansa ya kama ya mikawa Nimra, ita ma faduwa gabanta yayi jikinta ya fara rawa kamar marar gaskiya.

WAIRA POV.

By the time din da Eid yake tsammanin ta yi bacci sai ya kashe wutar, ita kuma ganin wutar ta mutu ya saka ta tashi zaune ta fito daga cikin dakin, a bakin kofa ta zauna tana kallon sama, taurarin da suka yi ma samaniya ido suka fara burgeta kallonsu take sosai kamin ta fara kirgasu. Tun tana zaune har abun ya kai ga ta mike tsaye ta fito waje gaba daya yana juyawa idonta na sama kamar wanda aka cewa idan kika kalli kasa zaki mutu, bata ankara ba ta ji ta bugi mutum da sauri ta dawo da dubanta gabanta sai ta yi arba da wani saurayi da be wuce sa'ar Eid ba, dariya ta yi ta sauke kai kasa tana cewa yayi hakuri, shi ma dariyar yayi ya rike walkin dake kugunsa yana kallonta.

“Ba sai kin ba ni hakuri ba, laifina ne”

“Laifina ne dai ban kalli gabana ba sai sama”

“Ba ki yi bachi ba har yanzu me kike yi?”

“Bana komai bachin ne be zo ba, kai miyasa baka yi bachi ba”

Ta tambaya yana saka yatsanta a baki tana watsa da yawun dake cikin bakinta.

“Daman na kan dade ban yi bachi ba”

“Waira....”

Kamar daga sama suka ji muryar Eid daga ita har shi juyowa suka yi suna kallon inda sautin muryar ke fitowa, Saurayin ya kalleta.

“Matsalar kenan Eid baya barin kowa ya rabe ki, ba ya barin kowa yayi magana da ke, shi yake tafiyar da ke”

Ita dai ban da kallonsa babu abun da take domin bata fahimci komai a cikin maganarsa ba, karaso Eid yayi gurin fuska babu annuri.

“Mu je ki kwanta”

“Bana jin bachi”

Ta amsa kai tsaye sannan ta juya zata cigaba da tafiya, wani irin fisgota yayi ta dawo baya da karfi ya daka mata tsawa

“Muje ki kwanta”

A ka'idarta ba a mata fada, haka zalika ba a mata tsawa, sai kawai ta fisge hannunta ta yi tafiyarta wani gefen dabam, kallon Saurayin kawai Eid yayi ya bi bayan Waira, gurin wasu manyan duwatsu ta nufa ta zauna tana kallon wajen garin iska mai dadi na kadata.

“Kar wani ya sake miki magana ki amsa?”

Ta juyo da karfi kamar ta dake shi.

“Zan amsa ko yanxu wani yayi min magana sai na amsa, ba ruwanka da ni”

Kallonta kawai yayi be ce komai ba, ya juya ya fara tafiya, ba shi da halin hukunta wacan saurayin da ya haddasa masa ruruwar wuta a zuciyarsa, domin idan yayi masa wani abun dole za a gani idan aka yi tsafi, ya san kuma babu makawa dole ne sarki ya hukunta shi, Waira ce kadai ke da ikon ta illata wani ko ta kashe shi a kyaleta, sai dai ayi mata fada ko dan hukuncin da be taka kara ya karya ba. Jin kamar ba zai iya barinta a gurin ba ya saka ya dawo ya sake cewa ta tashi ta je ta kwanta.

“Ba zan kwanta ba, na fada maka babu ruwana da kai”

Matsawa yayi kusa da ita sosai ya dafa kafadarta, tana kokarin kai hannunta ta janye na shi hannu ta ji tafiyar wani abu mai kamar Maciji ya shiga cikinta yayi bayanta da sauri kamar mai neman gurin boya haka ta rika jin abun na mata yawo har sai da ya zagaye jikinta ko'ina sannan ta ji yayi kasan cikinta. Da wani irin karfi da bata san tana da shi ba ta tura Eid ta fara dukansa babu kakkautawa.

“Me ka saka min a jiki me ka yi min? Eid me ka yi min me ye wannan abun nake ji?”

Hannayenta ya rike ya juyar da ita ya matseta a jikinta sosai ta bayanta har sai da ta natsu sannan ya sake ta.

“Kin san ba zan cutar da ke ba ko?”

Bata taba jin tsanarsa a ranta irin yau ba, gaba daya ya gama canja mata tsarin daren yau da take jinsa da nishadi, ya jagula mata lissafi ya bata mata rai. Wani irin huci take kamar zaki tana masa wata hararar da shi kanshi ya san sai ta dauki lokaci kamin ya su shirya. A gurin ta bar shi tsaye ta dawo dakinta ta kwanta tana ta jin haushinsa a ranta, shi kuma ya kasa tafiya ya kyaleta sai ya dawo bakin kofar dakin ya zauna ba tare da ta san yana gurin ba, sai da ya tabbatar da ta yi bachi sannan ya leka dakin, da idonsa ya haska fuskarta, bakinta a cige yake ta rumgume hannayena irin na masu fadan nan. Wani abu mai kama da Ƙulba ya fito daga kafafuwanta Eid yayi tsaye yana kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ya koma ya zauna kamar mai gadinta, be bar gurin ba sai da sanyin safiyar asuba ya fara sauka. Waira kuma bata farka ba sai da rana ta hasko dakin nata da wata bolar zuba shara ta masu kudi ya fita.
Ba musulma ba ce balle alwala da sallah ya zama abu na farko da zata fara yi, ba mai tsabta bace balle wankr baki ko wanka ya zame mata dole, haka ta fara lalaben abun da zata ci, babu komai a cikin akushin dake dakin, ganin bata samu komai ba ta nufi gurin da zakarunta suke ta leka ramen bera ta dora hannunta a bakin ramen, da gudu bera uku suka hau hannunta, sai ta saka daya a cikin gashinta dayan kuma a cikin aljihun walkinta na dama, daya daya rage ta saka shi a na hagu sannan ta fita kafarta babu talkami daman can bata da su gaba daya ko ma akwai bata damuwa ta saka, wata mahaukaciyar rayuwa take da babu mai burin yin irinta.

Waje ta fito gaba daya ta murza idonta so that ko da akwai kwantsa ta fita ba tare da ta wanke ba, gurin da ta saba zuwa ta ci yayan itatuwa ta nufa kamin ta karasa ta hango mutane sun doso inda take da sauri irin na wadanda aka bawa umarni, ganin haka ya saka taja ta tsaya domin mutanen na gidan Sarki ne dakarunsa ne ba gama garin mutane ba, ko ba a fada mata ba ta san laifi ta yi domin ba kasai Sarkin zai sa a kirata ko zo masa da ita ta sunan su gaisa ba sai idan ta yi laifi.

“Fada ta yi kira, Sarki yace a zo da ke”

Bata ce musu uffan ba, ta kai ta taba hannunsa in 5 seconds ta ga abun da ya faru a fada kamar a gabanta aka yi komai.

“Ban kashe shi ba”

“Mu yan aike ne kawai”
Chapter 17 · 0% Book details