← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 170

Sashe 132

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta amsa tana kallon cike da kulawa. Maleek dake tsaye jikin Mirror ya kalleshi sannan ya mike tsaye daidai da zimmar ficewa daga dakin, saboda shigowar da Ameer yayi.

“Maleek...”

Ya tsaya cak sakamakon kiransa da Ameer yayi, ya juyo ya kalli Ameer din dake kallon kasa cikin wani yanayi mai wuyar fassara.

“I know bana so na ko son wani abu nawa, na san ba zaka taba son abun da nake so ba, kuma ba zaka so na samu farinciki ba”

Ameer ya dago ya kalli Maleek.

“But Waira is different ita rayuwa ta ce, ina sonta irin son da kalamai sun yi kadan su bayyana alkali yayi kadan ya rubutu, ka bata a gurin kowa ka saka kowa ya tsane ne amman ban da Waira, kokarin bata alakarmu da nuna mata ni ba mutumen kirki ba ne, dan Allah ka bari, idan baka son zama a gidan nan zan iya tafiya na bar gidan, zan iya kaucewa duk wata hanya da zaka gan ni, amman please ka bar alaka ta da Waira, na san kana min kallon mutumen banza ko kuma makiyinka saboda abubuwa da suka faru, amman Waira da gaske nake, kai kasan idan ina son abu bana bashi baya, kuma idan na sakawa abu gaba ba zan saurara ba na maka magana ne saboda ina son abu ya samu ta masalaha. Kana da Abiey a raye, ka rayu da Ummi tun tashinka har yanzu baka rasa komai ba, so please ka bar min wannan ni na na samu farinciki, domin a yanzu farincikina yana tare da Waira...”

Yana gama fadar haka ya mike tsaye ya fice daga dakin ba tare da ya ce da Ummi komai ba. Ummi ta bishi da kallo kamin ta kalli Maleek dake tsaye.

“Me ka yi? Yaushe zaku fara son junanku Maleek? Akan me zaku raba hankalinku kirkiri kiyayya saboda Mace? Ba kasan zaka iya rasa Waira ka samu wata ba, amman ba zaka rasa dan'uwa ka sake samun wani ba, kar soyayya ko kiyayya ta rufe maka ido ka nemi cin amanar dan'uwanka, na san kana son Waira amman kokarin bata dan'uwanka a gurinta ba abu ne mai kyau ba”

Yana son yayi magana zuciyarsa na raya masa ko da ya bude baki yayi magana Ummi ba zata fahimce shi ba. Saboda haka yayi shiru ya kuma tsaya a gurin ya kasa tafiya.

“Baka tashi nuna kana sonta ba, sai a lokacin da shi ma ya ce yana sonta? Kuma ba za ku iya bari ta zaba a tsakanin kai da ita ba, sai ka soke dan'uwanka a gurinta”

“Ni ban soke shi a gurinta ba, ba zan hana ya sota ba, ba kuma za hana ita ma ta so shi ba, amman ba zan bari ya fitar da ita a gidan nan ba, bayan duk abun da yayi mata a baya”

“Yayi mata ko kuma yayi ma Nimra? Ina zaton saboda haka ne kake rike da shi a ranka, idan har wani zai rike wani da laifi ba za a zauna lafiya ba, kai ka manta irin abubuwan da ka yi min kuma ka yi ma kanenka, ka manta yadda kake nuna min kiyayya, ba dama na yi magana da kai ko na zauna a kusa da kai?”

Yayi shiru yana jin wani iri

“Da ace ban yafe maka na manta ba, kana tunanin zan zauna da kai kamar haka? Kowa yana laifi Maleek kamar yadda ni ma na yi, amman aka daga kafa, domin Allah ma yana yafe mana idan muka yi kuskure”

Ya sauke kansa kasa tare da ajiyar zuciya sannan ya yi walking out slowly kamar mai abun kunya. Yana janyo kofar dakin ya rufe Waira ta iso gurin tana rike da hannayenta idonta yayi ja sosai alamar ta yi kuka, suna hada ya sauke idonsa daga barin kallonta ya sauka kasa, binsa ta yi da kallo har sai da ya kusa sauka sannan ta kira sunansa.

“Ya Maleek”

Ya tsaya sai dai be juyo ba, ta kawa ta yi ta sauka kasa ta tsaya gabansa.

“Zaka kai ni gida Please”

Ya kasa ce mata komai kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta.

“Ina son na tafi gida ne, zan gane hanya yanzu”

Be ce mata komai ba ya dauke kai ya sauka kasa ta bishi da kallo kamar ta san zai waigo ya kalleta, kallonta sosai irin na tausayi tunaninsa na bashi cewar saboda shi ne zata bar gidan. Yana kokarin juyawa ya cigaba da tafiyarsa idonta ya fara zubar da ruwan jini, ba tare da ta sani ba, da sauri ta hauro yana kallonta.

“Idonki Waira jini”

Ta kai hannu ta taba hawayen da suka zubo mata ta duba sai ta ga jini.

“Wani abun zai faru, wani abu marar dadi”

“Kamar ya?”

“A duk lokacin da na ga hawayen jini a idona to wani abu ne zai faru, wanda ba zai min dadi ba”

Ya kalli kofar dakin Ummi sai kuma ya kalli downstairs, baya son Ameer ko Ummi su ganshi tare da Waira, Ummi zata yi zaton yana fada mata abun da ya faru ne, Ameer kuma zai yi irin wannan zaton.

“Waira zaki shigo dakina mu yi magana”

“Ina son na yi magana da Ummi ina son na fada mata cewar zan tafi gida”

“Akan haka zamu magana please come”

Ya wuce gaba sai ta bishi a baya, rike mata kofar dakin yayi har sai ta shigo ciki sannan ya rufe yana kallon saman gadonsa da take kallo.

“Ya Maleek kana da aure?”

Ya girgiza kai.

“Ban taba tunanin yin aure ba, balle na yi me yasa kike tambaya? Idan ina da aure ai da kin sani tun farkon zuwanki gidan nan”

“Ni ma abun ya ba ni mamaki, domin ban taba ganinta a downstairs tare da mu ba, amman ina ganinta idan na shigo dakinka, kuma ka fada min addininku ya rahamta taba jikin macen da bata tashi ba, amman ni ko wane dare kana zuwa min kana taba ni ko kuma kana zaton ban fahimta ba ne?”

Ya juya ya kalli gadon ya kalli Waira

“Wace mace dai tukuna?”

Sai a lokacin ta kalleshi, tun da take maganar matar dake kwance saman gadon kawai take kallo.

“Gata can”

Ta nuna saman gadon har lokacin jini zuba yake a idonta. Maleek ya juya cike da tsoro ya sake kallon gadon shi kam be ga komai akai ba, amman ita har lokacin saman gadonta take nunawa.

“A lokacin da na taba suma ma ita na gani, gata can zata fita, ta windows”

Ya kalli Windows din dake rufe ya kalli gadon ya sake kallon Waira.

“You're scared me please, idonki na jini and now kina fada min wata a gadona zata ta windows you're acting weird”

Ta sauke kanta kasa.

“Ni na san na ga mace, kuma ina ganinta a duk lokacin da zan shigo dakin nan”

“And kin ce ina taba ki when?”

“Kullum tun a wani dare da ka rakani dakina, ka fita sai ka sake dawowa ka taba ni, daga lokacin kusan kullum sai ka yi min haka”

“Nooo ba ni ba ne, maybe dai mafarki kika yi”

“Ban yi mafarki ba, na ga hakan a zahiri ba bachi ba, idan ma ina bachi tashina kake yi har sai ka gama tukuna nake iya bachi, wannan ya saka bana kwantawa wani lokacin har sai ka gama”

Ganin ta gaske take fada ya saka shi mamaki, sai dai mamaki irin na wanda ke lafiya wata lalurar rashin lafiyar kwakwalwa ta same shi, domin a yanzu be kallon Waira a matsayin mai hankali.

“Ba ni ba ne, ni ban taba yi ma kowa haka ba, kwalkwalwarki ke nuna miki haka, can you tell me why kike zubar da jini a idonki?”

Ta sake kai hannu ta taba jinin.

“Hakan na nufin faruwar wani abu, a gareni ko ga wani masoyina wani abu da zai min ciwo”

“Kamar ya?”

“Ya Maleek ni ina da banbanci da kai, ina ya ji abubuwa da yawa da zaka iya ji ba, zan iya ganin abubuwa da yawa da ba zaka iya gani ba, wata kila shiyasa nake ganin mace a duk lokacin da na shigo dakin nan alhalin kai mai dakin baka ganinta”

“Haka ne, wata kila shiyasa kike ganin wani mai kama da ni yana shiga dakinki yana taba ki, saboda ya bata ni a idonki, maybe fuska ya saka mai kalar tawa ko kuma”

“Ko kuma kai din ne...”

“Kin ce kina iya gane abubuwa me yasa baki gane waye shi ba?”

“Saboda ban taba rumgumarsa ba, sai na rumgume mutum ne nake iya ganewa”

“Toh ki gwada yau mana, kina tsafi ne Waira”

Ta girgiza kai a daidai lokacin da hawayen jinin ya daina zubo mata. Ba tare da tace masa komai ba ta juya.

“Dole ne sai kin tafi? Indai saboda ni ne ki zauna mana, ba zan sake yin wani abu da zai saka Ummi ta yi fushi da ke ba”

“Ba saboda kai zan tafi ba, zan tafi ne saboda lokacin tafiyar yayi, wata kila lokacin mutuwar ne yayi, daman na fada muku, wata rana za amin sako, ashe ba sako za a min ba ni zan tafi da kaina”

Ta bashi amsa ba tare da ta juyo ba sannan ta bude kofar dakin ta fita, ido hudu suka yi ita da Ameer, ya fito dakinta ita kuma ta fito dakin Maleek. Ya kalleta sama da kasa zuciyarsa na suya kamar yayi mata magana sai kuma ya dauke kai ya karaso inda take ya wuce ya sauka kasa. Ita kuma ta bishi da kallo sannan ta sake nufar kofar dakin Ummi ta murda kofar ta tura ta shiga. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon Ummi dake zaune gaban madubi tana hawaye, ta cikin madubin take kallon Ummi, Ummi ma take kallonta kamin ta kai hannu ta dauki tissue ta goge hawayen idonta ta juyo ta kalli Waira saboda jinin da ta hango a fuskarta da saman rigarta.

“Me ya same ki? Me ya faru? Ina kika samu jini?”

Waira ta kalli rigarta sannan ta kalli Ummi.

“Ummi me yasa kike kuka?”

“Fara fada min dalilin jinin da na gani a jikinki, kina tsorata ni a yanzu Waira”
Chapter 132 · 0% Book details