← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 170

Sashe 72

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin shiru bata amsa ba kuma bata ce komai ba ya saka ya yanke kiran, ya cira kafa ya taka zuwa gurin motarsa ya shiga har ya murza key sai kuma ya fito koma ciki, sai dai wannan karon ba cikin yafa kai tsaye ba sai da ya tambaya ina kitchen din gurin yake aka fada masa sannan ya shiga kai tsaye ya doahi kitchen din wadanda suka san fuskarsa suna ta gaishe shi, be amsa musu ba domin ba gaisuwar ce ta kawo shi ba.

“Ina kuke aje kayan da kuke aiki?”

Ya tambayi wani namiji wanda daya ne daga cikin masu dafa a abinci a gurin, sai ya nuna masa hanyar da ake zube kayan da aka wanke, Ameer ya nufi gurin yana dubawa sai da idonsa suka sauka akan wukaken dake aje a gafe daya na aiki, ya isa gurin ya zari daya ya juyo sai duk suka ja baya da suna kallon juna irin kallon na gulma wasu na ala ala idan ba a cikinsu zai dabawa wani ba.

“Ranka ya dade wukar nan ta aikinmu ce”

Ameer ya juyo ya watsa masa harara sannan ya fice, kamar zai tashi sama haka ya isa gurin motarsa dake kunne yana ta sauri, ya bude ya shiga yayi reverse ya fice daga gurin. Left side ya fara bi yana tafiya yana duba gefen hanyar, ganin babu abun da yake nema bata isa barin unguwar ba domin hanya ce mai tsawo kuma guri ne da ba a cika zirga zirga da motoci, wannan dalilin ne ya saka mutane ke son restaurant din ne, unguwa ce dake nesa da mutane kuma guri ne da babu hayaniya da ganin mutane barkatai, wani ma har ya shiga yayi abun da zai yi ya fito ba za a san ya shigo ba, saboda yanayin gurin da kuma unguwar. Ya juya kan motar ya dawo right side yana gudu sai yana kallon gefen titin addu'a kawai yake a ransa Allah yasa ya ganta, kuma ya san zai ganta matukar ba wani gurin ta shiga ba, ko kuma wani ya rage mata hanya.

Humairah na tafiya gefen titi wata motar aka rage gudun motar ta dawo daidai ita ta tsaya, tsoro ta dan ji domin bata san waye cikin motar ba, tsayawa ta yi tana kallon bakin gilashin da aka sauke, ga mamakin Ameer ne matukin motar, da kai yayi mata alama da ta shigo ciki sai taja tsaki ta dauke kai ta cigaba da tafiyarta, tuka motar yake a hankalin yana binta ganin kamar bata fahimci abun da yake nufi ba ya saka shi mika hannu ya bude mata front seat. Sai ta tsaya kamar zata shiga sai da ta ga shi ma ya tsaya sannan ya kama murfin motar ta rufe da karfi har sai da yayi kara kamar zai cire, ta cigaba da tafiyarta ya sake binta ya bude mata gambun motar.

“Get in”

“Ba zan shiga ba, har ka isa me kake nufi da na shiga an fada maka ni yar iska ce? Ko kuma ni an fada maka ban san ciwon kaina ba? Ko an fada maka tsoronka nake? Ba zan shiga ba, aiki ne daga yau na zan sake yi ba, balle har ka wulakanta ni”

Jan motar yayi ya matsa gaba ya faka yana jiran ta karaso, ita kuma ta ayyana a ranta cewar ba zata shiga motar ba ko da kuwa hankata zai yi. Sai dai abun da bata sani ba ya shirya mata, tana isowa gurin ya bude motarsa ya fito ya zagayo gefen da take.

“Wai Ameer me ka dauki mutane ne? Bayinka? Ka rika juya su yadda kake so kana cilasta kowa yin abun da ka ga dama? Ni abun kunya ne a gareni a gan ni a motarka, domin ni ma zai ayi min daukar yar bariki...kuma... ”

Bata karasa ba ya dago wukar dake boye a hannunsa ya nunata saitin wuyanta.

“Ke idan kika fara zuba baki san ki tsaya ba, idonki yayi tsauri baki tsoron kowa”

“Ina tsoron wuka Ameer dan Allah karka kashe ni”

“Shiga mota or will cut your throat”

“Toh”

Jikinta na rawa ta bude motar tana ta kallon titin ko zata samu wanda zai taimake ta, motoci biyu da suka wice ba su damu da kula da abun da le gafen titi ba balle har a kawo mata dauki, haka ta shiga motar ya rufe sannan ya zagaya, wani bangare na zuciyarta na raya mata cewar ta fita ta gudu kamin ya shiga sai dai ina tsoro irin na masu bakin tsiwa ya hana ta aikata komai har ya shiga motar ya fara tuki fa hannu daya, dayan hannunsa kuma yana rike da zumgurariyar wukar ta yankan nama.

“Dan Allah karka cutar da ni Ameer? Me na maka?”

“Baki san abun da kika yi ba?”

“Toh ka yi hakuri ba zan sake ba, yaushe kuma ka koma yin dabanci ba a san yayan masu arziki da wannan dabi'ar ba”

“Yau na fara, kuma kina yin wasa zan yanka wuyanki ko na fada cikinki kin ga dai ba za ayi min komai ba ko? Idan na kashe ki an kashe banza dan haka ki bini a hankali”

“Toh... Yanzu gida zaka kai ni?”

“Saboda gani direban ki ba”

“Amman Wallahi tallahi na rantse da Allah ni ban taba iskanci ba, dan Allah karka lalata min rayuwa Ameer”

“Ni na taba iskancin, negative mind daman shi ne a ranki, you should be praised kin shiga motata ma ni me zan yi a jikinki?”

“To miyasa zaka dauke ni a motar kana ta tafiya me zaka yi min? Dan Allah karka yi tsafi da ni toh”

“Dodona baya son irin jininki”

Cikin dabara ta kai hannu ta murda gambun motar da zimmar ta bude sai ta ji shi a rufe.

“Na shiga uku na lalace”

Ta fara kuka, hankalinta ya tashi sosai domin bata san manufar Ameer na yi mata haka ba, kai ta zai yi wani gurin ya aje ko ya hukuntata akan abun da ta yi ko kuma wani abun zai mata.

“Ni zan iya baka hakuri a bainar jama'a idan dan abun da na yi maka ne, zai saka ka hukunta ni, dan Allah dan darajar iyayenka ka yi hakuri”

Kallonta kawai yayi ya dauke kai, yadda ta makure a cikin motar ta zama marainiyar gaske duk sanyin ac motar ita gumi take ga idonta ya zurma kamar zuru. Faka motarsa yayi gefe ya bude ya fita rike da wukar da kuma wayarsa da key motar da Daddy ke kira. Yana piciking kiran Daddy ya tambaye shi.

“Kana ina Ameer”

Ya juya kalli inda yake.

“Wani guri Daddy?”

“An fada min ka shiga har gurin da ake dafa abinci ka dauki wuka, me zaka yi da ita?”

“Wani zare na yanke a jikin tayar motata”

“Ameer ba ka min karya karka fara, ni nasan ko me zai faru ba zaka yanke zare a jikin motarka ba”

Yayi dariya.

“Daddy maganar gaskiya wata yarinya na yi ma barazana da ita”

“Subhanallahi barazana da makami Ameer? Kar zuciya ta dauke ka ka aikata kuskure, ka zo ka same ni gida yanzu nan, sai mu ji idan akwai matakin dauka kamata a adauka akan yarinyar kuma na ji abun da ta yi maka”

“Ba wata babbar matsala ba ce Daddy karka damu”

“Na ce ka zo mu tattauna, kuma karka tana yar mutane Ameer dan Allah”

“Okay Daddy gani nan zuwa”

Ya sauke wayar ya nufi motar ya cire key ya shiga ya zauna, tun da suka kama hanya suna tafiya bata ce masa uffan ba sai share hawaye take gabanta na zillo tana ta tunanin inda zai kaita zuciyarta sai sake sake take mata. Tafiya mai nisa suka yi sannan ya shigo umguwar manyan mutane ya fama gaban wani katon gida da gate din gidan ma ya isa bakauye kallo. Wani karamin littafi ya dauko ya fara rubutu, yana yi tana leko har ya gama ya nade takardar ya mika mata sannan ya bude gurin daya aje wayar Nimra ya dauko ya mika mata.

“Shiga gidan nan ki kai wannan wayar tare da takardar nan, amman idan kin shiga ki ce ke kawar Nimra ce kin zo ganinta, sai idan kun kebe zaki bata”

“Wallahi ba wata Nimra yanke min kai za'ayi wannan katon gidan na yan mafiya ne”

“Kwarai kin san mahaifina kudin tsafi yake da su”

Ta lake kafada tana kuka.

“Ni ba zan shiga ba, Allah ya fika”

“Ke look babu abun da za'ayi da katon kan nan naki, yarinyar da kika rika zagina kwanakin baya saboda ita, to gidansu nan, so nake ki shiga ciki ki kai mata wayar nan da wannan takardar, daga nan sai ki duba lafiyarta daman na ga kin damu da ita ai”

“Idan aka kashe ni hakkina yana kanka”

“Idan baki shiga ba, zan saka wukar nan na yanka ki, ko kuma na dauke ki na kaiwa abokaina su yi miki wulakanci son raina, dan haka ki zabi ďaya”

“Ameer me yasa kake mugu ne? Kana ta daukar hakkin mutane da basu maka komai ba”

“Toh bari na zabar miki a cikin ukun”

“Zan tafi, ka bude min motar”

“Idan na bude miki motar kuma ki gudu, na biki da wukar nan ko kuma na aika har gidanku a daukoki ai kin san dai na san gidanku ko?”

Ta daga kai, ta zabi shiga ne saboda shi ne mai sauki a cikin hukuncin abubuwan uku da ya shar'anta mata ta zaba, ta san ko da masu fille kai ne zata musu addu'a, idan kuma abun da ya fada ne a ciki idan ta aikata ga huta. Ta karbi wayar da takardar ta saka a jakarta sannan ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito.

“Kina yin wani abu kin san sauran”

“Me yasa kai ba zaka shiga da kanka ka bata ba, idan har da gaske gurinta ka zo”

“Ki kwankwasa kofa a bude miki”
Chapter 72 · 0% Book details