← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 170

Sashe 125

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“ Tsawon rayuwata wannan ranar nake jira, ranar da zaka gabatar min da wata mace a matsayin wadda kake so, ko kuma ni na gabatar maka ka karba, ba tare da ka musa min ba, sai dai abun ya zo min da inda ban zata ba, a wani yanayi da ban yi tsammani ba, ba zan ga laifinka ba, haka ma Ameer ba shi da laifina ne da ban maida hankali na kula da abun da idonka yake a kai ba”

Sai a lokacin Maleek ya samu baki magana domin a dazu jin yayi kamar Ummi ta daure shi da tsarkoki.

“Ba komai ne laifinki ba Ummi, ki daina dorawa kanki laifi babu abun da kika yi a nan”

“Da ace na zama Jarumar uwa kamar sauran iyaye mata, da na dade da lura da haka, da komai ya zo da sauki”

Maleek ya matsa daf da ita sai ta kwanto saman jikinta.

“Mahaifinka ya fada min abun da kake ta boyewa, ban yi zaton abun zai zo da wuri haka ba, kullum addu'a da buri na ga ranar da zaka canja, i wish i could...”

Sai kuka ya ci karfinta. Wani abu ya ji na rashin dadi, irin wanda ki wane dan kwarai yake ji idan uwarsa tana kuka. Sai yayi unkurin fada mata shi ba son Waira yake ba sai kuma ya ji ya kasa, wata kila farinciki take da hakan din ma da Abiey ya fada mata, sai dai shi ya san baya son kowa a ransa. Dan haka ya rumgume yana jin wani sanyi irin na wadda uwarsa take raye da kuma kaunarta a zuciyarsa da tausayinsa. A yanzu ya tabbatar hi miss alot na rashin samun damar rabar jikin mahaifiyarsa da sanin danuwarta tun da dadewa.

“Dare yayi Ummi ya kamata ki samu wutawa”

Ta dago daga jikinsa ta kalleshi sannan ta sauke kai ta nufi hanyar stairs jiki babu kwari. Da kallo ya bita har ta haye sannan ya zauna yana tunanin maganar, a sirance ya yi murmushi ya shafa kansa, be san me yasa abun yake saka shi nishadi ba, saboda Abiey yayi amfani da shi ne ko kuma saboda za a hanawa Ameer ita ne? Abun dai is just funny to him kuma be san dalili ya mike yana murmushin da ya kusan komawa dariya ransa fes kamar an masa albishir da wani abun farinciki. Wayarsa ya ciro ya rika ta da hannu biyu ya shiga message dinsa ya turawa Abiey sako.

“Abiey ban ce ina son yarinyar nan ba fa, me yasa ka fadawa Ummi haka zata yi zaton saboda Ameer ya ce yana sonta ne”

Silly Emoji Abiey yayi masa reply da shi ba tare da yace komai ba, a nan ma Maleek murmushi yayi ya nufi kofar fita daga falon, harabar gidan ya fito gurin motoci ya tsaya yana ta kallon taurarin dake samaniya, yana jin kamar bashi da damuwa ko daya. Can kuma ya sauke kai yana tuna sallah da ya tarar Waira na yi a dazun abu ne mai kyau domin haka na nuna sha'awarta ga addinin musulumci ne. Wayarsa dake hannunsa ya taba ya shiga sashen hotuna ya kama hotonta da ya dauke ta tana bachi yayi ta kallo kamar ba gobe.

A daren Ummi kasa bachi ta yi saboda tunanin da ya zame mata biyu ta rasa ina zata bullo, wane zata dauka wanne zata aje. Sai kusan asuba ta samu runtsawa asuba na yi kuma ta farka ta yi sallah ta fito dakinta kamin ta kawo kasa ta hango mijinta dake kokarin hauro stairs din.

“Na san baki yi bachi ba yau, zaki takura kanki da tunani ne kawai na raya haka saboda ba zo kin kwanta a bangarena ba”

Kamin ta karaso inda yake har hawaye ya cika idonta.

“Ba ni da sauran karfi a yanzu Abiey, dukansu yayana ne, ban san wa zan goyawa baya ba, a zan iya zaba a tsakaninsu ba, kuma na san hakan zai haifar da matsala da karin rashin fahimta ne a tsakaninsu, a maimakon a samu mafita sai abun ya kara lalacewa”

“Ina ganin kamata yayi ki fito fili ki fadawa Ameer gaskiya nima zan sanar da Maleek”

“Ba lallai ne ya fahimta ba, Ameer yana da wuyar sha'ani, yar alakar dake tsakaninmu zata yi tsami, da ma ace zan iya tankura Maleek wata kila shi zai iya hakura, domin Ameer yana son Waira sosai fiye da tunaninka, yadda kike ganin kamar cutar da ita zai yi ba zai yi haka ba, na ga kaunarta idonsa”

“Amman kuma kika kasa ganin hakan a idon Maleek karki zama selfish mana Zahra, ni ma ina son farinciki ďana fiye da yadda kike son Ameer, ina bin komai a hankalin ne saboda Matsalar da kike ciki... Dan haka ina ganin abun da ya dace kawai a fitar da yarinyar nan waje ta yi karatu kamin mu ga abun da Allah zai yi”

Ummi bata da karfin cewa komai a yanzu, ta san Abiey ba zai fahimce ta, haka ma Ameer ba fahimtar da zai yi ba.

“Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri, bari na shiga kitchen”

Ta wuce ta nufi kitchen, yana ganin haka ya san akwai abu a kasan zuciyarta daman shi ma juyawa yayi ya fice daga falon ya koma bangarensa. Sai da ya wuce sannan Waira ta sauko daman tun dazun tana labe a saman ba dan tana ji abun da suke tattaunawa ba kuma ba dan tana son ta ji din ba, sai dan bata son Abiey ya ganta, domin zuciyarta na yawan raya mata Abiey baya sonta. Ta sauko ta shiga Kitchen sai ta Ummi ta rike fridge sai kuka take a hankali, ta saba ganin Ummi a kitchen da asubar fari irin haka, amman sai idan akwai dalili kamar tana son shirya abun karyawa da wuri saboda wani ko ita, amman a ka'ida Ummi bata shiga kitchen sai 6:30am ko 7 ma.

“Ummi...”

Ummi ta juyo ta kalli Waira da ta kira sunanta, sai ta ji kamar ace tana da wani iko da zata cewa Waira ki cire sonki a cikin zuciyar kowa.

“Are you okay, ko Abiey ya miki fada ne na ganshi ya zo”

Ummi ta share hawayenta.

“Labe kike mana?”

“Aa na zo zan shiga dakinki na dauko abun sallah ne sai na hango kin fito na zo saukowa sai na ganshi shiyasa na koma na boya na san ai baya so na”

“Abiey be tsane ki ba Waira ki daina saka wannan a zuciyarki”

Ta daga mata kai son sanin damuwar Ummi da abun da ya saka ta kuka ya saka Waira tambayar Ummi.

“Ummi can I hug you?”

Ummi ta daga mata kai, sai ta rumgume Ummi ya rufe ido, babu abun da bata gani ba, tun daga kan maganar da Ameer ya fadawa Ummi har zuwa wanda Abiey ya fadawa Ummi akan Maleek da kuma na yau da Abiey yayi magana da ita. A cikin duk abubuwan bata ga na damuwa ba, da zai saka Ummi kuka ba, domin duk cewa suke suna sonta ita kuma a gurinta haka abun ne mai kyau sai dai kalmar aure da ta yi ji a ciki shi ne abun da ya fi daga mata hankali. Ta dago daga jikin Ummi ta kalleta sai Ummi ta sakar mata murmushi.

“Mun yi magana da Abiey ne akan yana son ya fitar dake wata kasar ki yi karatu”

“A nan fa?”

“Ba wai na aminta ba ne, zan yi shawara na ga idan hakan ya dace kuma idan kina ra'ayi”

“Bana so, bana son wani gurin da ba nan karatun da nake a nan ma ya isa ai, ba kullum ina zuwa school ba, Mai Lesson ne ya daina zuwa ai amman ni ban fasa yin darasi ba”

Tana fadar haka ta saki Ummi ta fice daga kitchen tana shirin yin kuka.

AMEER POV.

“Abun is na ma rasa me zan ce”

Ameer ya hade yawu yana marairaice fuska kamar gaske.

“I know shiyasa tun farko ban fada ba, amman yanzu ina kokarin ganin na gyara abubuwan da na bata ne, dan Allah karka min mummunar fahimta ne”

“Nonono ka yi tunani mai kyau, amman aure ba abu ne da za ayi wasa da shi ba, kuma a yanzu da kake kokarin gyara abubuwa hakan yana da kyau, sai dai dole ne ka nemi afuwar yarinyar”

“Zan yi haka Daddy, na gode sosai da fahimta, me kake son mu tattauna?”

“No karka damu wata rana zamu yi magana akai ci abincinka”

Daddy ya fada da murmushi a fuskarsa, Ameer ya fara cin abincin yana jin wani iri, domin be tsaya ya saurari shakuwar Daddy ba, kuma be kamata yace masa no a duk wani abu da zai gabatar masa ba, shi dai be masa wannan karyar dan kawai ya hana shi fadar abun da zai fada ba, sai dan ya samu mafitar gabatar masa da Waira kamin shi ya gabatar masa da wata a matsayin matar aure.

“Daddy ba zan jidadi ba idan baka fada min abun da kake son mu tattauna ba, please ka fada min ko gankali zai kwanta”

“Zan fada maka amman ba yanzu”

Cewar yana murmushi sai dai zuciyarsa ta kasa yarda abun da Ameer ya fada masa a yanzu, kuma ya kasa natsuwa wata kila saboda ya ji abun ne wani irin kamar ba abun da kai zai kama ba. Ameer yayi bachi a daren mai dadi da saka nishadi, saboda tunanin Waira. Washe gari da 6:30am ya fita daga gidan zuwa gidan Ummi saboda ya samu kai Waira School da wuri, domin ya daukarwa kansa nauyin kaita makaranta kullum kuma ya daukota. Bakwai da yan mintuna ya iso gidan ya shigo falon yana ta zuba kamshi. Sai dai yana shigowa ya tararda Mahmood da Maleek da Namra a dinning sai ya saka jin babu dadi, kara ma Mahmood suna dan good time da shi, amman Maleek da Namra makiyansa ne kamar yadda shi ma suke kallonsa a makiyansu, Sai dai ganin Ummi da yayi ya dan saka shi jin sanyi, ya karasa gurin cikin gadara ya dafa kujera ya gaishe ta.

“Ummi ina kwana”

Ta dago ta kalleshi yanayi fuskarta da idonta sun fada masa ba lafiya ba.
Chapter 125 · 0% Book details