← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 170

Sashe 154

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fadar hakan ya wuce gaba ya barta a gurin tsaye da mamaki, cikin falon ya shiga ya saka Hanne ta fito ta kwashe kayan da suke cikin motar, Nuwaira kamar kazar da kwai ya fashewa haka ta shigo cikin falon.

“You can go in, da alama gidan babu kowa sai Hanne, but please you should be careful ba zan ce ban yarda da Ameer ba a yanzu ba, amman na san so babu abun da ba shi sawa, karki yarda wani ya taba jikinta sai muharraminki kuma as i told you muharamminki na nufin mijinki, kannenki ko yayanki wanda uwa ko uba suka haifa, ko kuma kuka sha nono daya, ko kuma yan uwan mahaifiyarki ko mahaifinki, ni da Ameer da Mahmood duka ba mu da wannan ikon a yanzu so ki cula da kanki”

Yana gama fadar hakan ya nufi kofar fita falon zuciyarsa na masa mugun zafi, ya san yayi yankan kaddara ya naukar abun da ba shi da tabbacin zai iya ko akasin haka a yanzu, yes be taba furta yana son Nuwaira ba kuma ba shi da tabbaci idan abin da yake ji a kirjinsa da zuciyarsa so ne ko kuma kokarin karewa kawai kamar yadda yayi ikirari da farko. Cikin motarsa ya zauna ya kasa tuka motar kuma ya kasa fadawa direba ko daya cewar Nuwaira zata fita su kaita idan ta bukaci haka, a duk lokacin da ya tuna Ameer zai kebe da ita sai ya ji wani irin abu na fisgarsa, a yanzu dai ya shirya da dan'uwansa kuma baya fatan wani abu ya sake shiga tsakaninsu domin ya ga canji a rayuwar Ameer sosai ba kamar baya ba, a yanzu zai iya masa shaidar mutumen kwarai amman duk da haka zuciyarsa bata natsu ya kebe da Nuwaira ba.

Duk wani dauki da take na son dawowa gidan da kuma samun abun da zamu iya kira da yanci ya ragu saboda ta tararda Ummi bata cikin gidan, idan kuma ta tuna da kalar ciwon Ummi sai hankalinta ya tashi, a lokacin dakinta sai ta nemi farkom gadon ta zauna ba tare da ta yi komai ba, tunanin auren da aka daura musu da Maleek ya tsaya mata a rai, rashin lafiyar Ummi ma wani abu ne dake dauke mata jindadi. Mikewa ta yi tsaye a hankali ta isa gurin windows din dakinta ta daga curtains din ta bude windows din tana kallon Motar Maleek dake harabar gidan har lokacin, shi ma saitin windows din dakinta yake kallo kamar ya san zata leko ya ganta.

“Ya Allah make it easy for me, me nake ji now? Me na aikata why yanzu nake jin kamar ba zan iya numfashi idan bata kusa da ni ba?”

Shi dai kam mamakin kansa yake domin be tabbatar son Nuwaira yake ba ko akasin haka, abun da yake ji a kirjinza so ne ko kuma sabo ne da shakuwa. Sai da yayi da gaske sannan ya iya jan motarsa ya fice daga gida. Sai da ya daina hango motarsa sannan murmushi ya cika fuskarta ta kai hannu ta tana kirjinta dake cikin hijab wani abu take mai bugewar da saka farinciki na rabarta wani kalar abu ne dake kokarin rayuwa a tsakanin kirjinta da zuciyarta, wani kalar abu ne da bata taba jin irinsa ba, wani irin bugawa zuciyarta take da karfi kamar zata fasa kirjinta ta fito numfashinta har nauyi yake. Wani abu take ji mai kamar nishadi tuna abun da Maleek yayi a gaban Sarkinsu da kuma irin yadda Sarkinsu ya nuna yana tsoronsa, a yanzu kan ta yarda Maleek taba dake da duk mazan da ta hadu da su, a yanzu yana burgeta fiye da kowa, jarumtarsa da tsayarwa da yayi a gaban matsafan garinsu ya nemi aurenta abun a jinjina masa ne. Har ta cire tufafin jikinta ta yi wanka murmushi ne a fuskarta tunanin abubuwan da Maleek yayi ya rika ruhuta, ya hana ta tunanin komai sai shi, ciki har da aikin da ya taya ta, sai a yanzu daure mata idon da yayi yake bata dariya. Wasu tsofin tufafi da ta bari a dakin a lokacin da zata tafi su ta dauka ta saka domin bata da wasu tufafin da suka yi saura a dakin yanzu tofafin da ke motar Maleek bata san inda aka aje su ba. Bata samu hijab ko daya ba dan haka ta shiga dakin Ummi ta dauki mayafin abayarta ta rufe kanta ta fito ta sauko kasa. Hanne ta gaisheta ta mata barka da dawowa Nuwaira ta amsa cikin far'a da sakewa domin tana cikin nishadin zuciya. Waje ta fito ta zauna a kujerun da Maleek ya saba zama make herself comfortable tana jin kamar shi ne yake zaune kusa da ita. Although direban zai zo da kansa ya same ta a gurin ne ya dauko mata ya kai ta, sai ta ga sabanin haka domin babu wanda ya zo ya ce mata ta taso su tafi, haka ta yi da zama a gurin har rana ta fara yi, ana hada hadar fara Sallah azahar motar Mahmood ta kunno kai cikin gidan, ko fitowa motar be yi ba ya sauke farin gilashin motar ya mika hannunsa ya bude mata front seat.

“Ta so Nuwaira”

Da hannu yayi kiranta sai ta taso da saurinta ta nufi motar ta shiga ta rufe.

“Ummi tana son ganinki amman zamu fara zuwa ki duba Ameer”

Bata ce komai ba, shi ma be sake ce mata ba har suka bar gidan. Ta kunsa labari a ranta kala kala da zatawa Ameer idan sun isa na jarumtar da Maleek yayi dan haka ta fita motar da kuzarinta bayan sun isa asibiti. Mahmood yayi mata jagoranci suka shiga cikin asibitin, shi ya bude mata kofa ta shiga shi kuma ya juya ya koma yana fadin.

“Idan kun gaisa ki fito ina jiranki gurin motar”

“Okay toh”

Ta amsa har sau biyu saura da turanci, sannan ta shiga cikin dakin, bata saba sallama ba dan haka bata gwada yi a nan ba, sai dai ta gaishe da kanwar mahaifinsa Bahijja da ta samu a dakin, sai kuma Humairah da kusan wannan ne gani na hudu da ta yi mata. Ameer ya sauko da kafafuwansa daga saman gadon yana kallonta murmushin dake fuskarsa kamar zai rikide ya zama mutum tsabar farinciki da shaukin ganin Nuwaira, gaba daya sai ya ji kamar babu ciwo a tare da shi.

“Mama bari mu ba su guri”

Humairah ta fada tana kallon Mahaifiyarta Bahijja, a take ta tashi tsaye suka fice tare da Humairah, Ameer na ganin haka ya cira kafarsa mai ciwo ya dan taka cikin karfin halin da ya saba yana son mika hannu ya riko hannun Nuwaira, domin to him rike hannun mace or hugging dinta is nothing to him ko da kawarsa ce balle kuma wanda yake so, even a yanzu ya canja but baya jin zai iya rike kansa daga taba hannun Nuwaira ko hugging dinta musamman ma a yanzu. Ganin yana kokarin rikota ya saka ta dan ja baya tana masa kallon tausayi ganin rauni a tare da shi.

“Ya Maleek yace na daina bari wanda ba muharrami ba yana taba ni”

Yayi murmushi.

“I just want to touch you, i miss you so much ji nake kamar shekara kika yi baki kusa, karki damu kin kusa zama tawa ni kadai na kusa zama muharraminci halak malak, bana tunanin zan iya dauka lokaci baki kusa da ni Nuwaira we will gate married soon”

Daga tausayi dake fuskarta ta koma mamaki.

“Daman ana iya a addinin nan namiji biyu zai iya auren mace daya?”

Wannan karon dariya yayi kamar ba marari lafiya ba.

“No auren da aka daura muku da Maleek ba auren gaske ba ne irin na addininmu, a yanzu ne dai za a daura miki aure na gaskiya a tare da ni”

“Ya Maleek fa?”

“Shi ai ba mijinki ba ne, and he won't be, you're mine forever and ever come here”

Ya mika mata hannunss yana murmushi wani irin farinciki marar misaltuwa yana cika ransa. A take mamakin dake fuskarta ya gushe zuwa wani abu mai yanayi da damuwa, ta kasa karasa inda yake sai ma juyawa da ta yi da fice daga dakin ta kasa amsa kiran da yake mata.
One Month Later...

Dakinsa ya fito yana gyara rigarsa ya isa bakin kofar da Nuwaira take ya murda kofar a hankali ya tura, ganin babu kowa ya saka ya shiga cikin dakin ya kwankwasa bathroom ya saurara ko zai ji motsin ruwa ko kuma ayi magana be ji ko daya ba.

“Nuwaira...”

Shiru be ji an amsa ba, he has no other option bayan ya juya ya fita. Kasa ya sauko ya zauna yana kallon upstairs din ita kawai yake son ya gani.

“Wa kake nema?”

Ya juyo ya kalli Namra dake zaune kasa tana cin tuwo.

“Nuwaira...”

“Tana dakina tun da kuka tafi da Ummi kullum a dakina take kwana”

“Tsoro take ji?”

“Maybe, but ta fi yin haka idan Ameer yana nan”

“Kila she's feeling lonely without Ummi ya kamata ki jata a jiki”

“Ina fa kokarina, kasan bata daman can ta mu bata jika ba, a dakin ma idan ina ciki takurewa take kamar zata yi kuka, kuma kamar dole sai ta kwana a dakina, idan na ce ta fito ta zauna sai ta ki, Ameer ma yayi har ya gaji, Mahmood ne kawai ke fitowa da ita shi ma yana fita take kowa daki, idan ka ganta a waje toh makaranta zata tafi ko kuma ta dawo, sai kuma idan ta ji yunwa”

“Tun a video call din da muka yi da ke na lura bata cikin walwala kuma ta rame”

“Wa yake cikin walwala rashin Ummi ya taba kowa a gidan nan, har Hanne balle kuma mu da muke yayanta, ba san yadda nake ji ba idan na doso cikin gidan na tuna cewar Ummi bata ciki, ba Ummi ba Abiey kai ma baka nan kuma ka san ban saba rayuwa da Ameer ba, Mahmood kawai nake kallon na ji sanyi”

“This too shall pass”
Chapter 154 · 0% Book details